Sashe 67
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta tsaya tana kallona, ni kuma na cigaba da abin da nake yi, ban damu da maganganun da aka fara yi ba, ana ba ni rashin gaskiya, Anisa ta fice daga É—akin a sanyaye, na kammala shiri na yafa mayafi, aka raka ni É—akin Mama, ta ce"Sayyada ai duk wata nasiha da za mu yi miki ni da mahaifinki mun yi, Allah Ya ba ku zaman lafiya da zuri'a É—ayyiba".
Mutanen ɗakin ma suka dinga tofa tasu nasihar, sannan yayar Mama ta riƙe ni har zuwa mota, a karo na uku zan shiga rayuwar aure, kuma ina fatan ya zama na ƙarshe da izinin Allah, hawaye ya kufce min, na share da sauri ina ƙarfafawa kaina gwiwa.
Gidan ɓangare ɓiyu ne, part na farko shi ne na uwargida, nan aka fara kai ni, tana falo tare da 'yan'uwanta, duk da ina lulluɓe ban kalli fuskarta ba, amma dai an yi mana karɓa ta mutunci, ana ta addu'ar zaman lafiya da shawarar haƙuri da juna, uwargida ta furta da bakinta ta karɓi amana, za ta zauna da ni da zuciya ɗaya, 'yan'uwana ma suka ba su tabbacin ni ma zan zauna da ita lafiya da biyayya, tun da ba sa'ata ba ce.
Aka ɗauke ni zuwa ɓangarena, sai a lokacin na buɗe fuskata na kalli gidana, babban falo ne, wanda ya ƙawati da komai na alfarma, sai ɗakuna guda uku biyu akwai gado, ɗayan kuma a rufe yake sun ce bai bada mukullinsa ba tun da aka zo ganin ɗaki a haka yake, sai yalwataccen kitchen da banɗaki, sannan kowane ɗaki akwai banɗaki a ciki, komai na gidan ya fi na gidan Sadam kyau, tsada, har ma da tsari, amma sam ba wannan ne a gabana ba, saboda ba na son me gidan, kuma ba na jin zan so shi har abada.
Kowa ya watse aka bar ni ni ɗaya, wani sabon salo da ban taɓa ji ba, sai ga matar shi ta yi sallama a ɗakina, na amsa ina kallonta, babbar mace a kaina, tun da ni har yanzu a shekara ashirin da shida nake, ita kuwa a kallon da na yi mata za ta yi talatin da biyar, na amsa fuskata babu yabo babu fallasa, na ce"Sannu ina wuni".
Ta zauna tana cewa"Lafiya ƙalau amarya, ya zaman kaɗaici da baƙunta?"
Na ce"Alhamdulillah".
Ta ce"Ma sha Allah, Allah Ya ba mu zaman lafiya, Ya kuma ba ki haihuwa mai albarka".
Na ce"Amin, ke ma Allah Ya ba ki".
Sai na ga ba ta amsa ba.
Muka yi shiru na 'yan mintuna, tana ta danna waya, can ta ce"Ango shiru bai ƙaraso ba, bari dai na kira shi na ji me ya tsayar da shi haka".
Ban ce komai ba, ni zaman ma ya gundure ni, ba don kar ta ce na yi mata wulaƙanci ba da tashi zan yi na shiga ɗaki na kwanta. Yana ɗaga wayar na ji mace ta lanƙwashe murya har tana wani rangwaɗa kai gefe ta ce"Hello mai martaba".
Na dinga kallonta ta gefen ido, ban ji dai me ya ce mata, sai ta ce"Amarya fa tana ta jiranku, ya kamata ku dawo, kun bar ta da kaÉ—aici".
Shiru na É—an lokaci, da alama bayani yake yi mata, ta ce"To Allah Ya dawo mana da ku lafiya".
Ta sauke wayar ta ce"Ki yi haƙuri, wai wani uzuri ne ya taso masa babu shiri, sai wajen sha ɗaya zai ƙaraso gidan".
Na ce"To Allah Ya kawo shi lafiya".
Haka muka cigaba da zaman jigum-jigum, ina ta tunanin ɗana wanda Mama ta hana a taho da shi yau ta ce sai an kwana biyu, wannan ce rana ta farko da zan kwana ba tare da shi ba tun da na haife shi, tun ina mazewa har na ji kamar zan fara gyangyaɗi, wajen ƙarfe goma saura kwana na tashi, ganin ita ba ta da niyyar tashi, na ce da ita"Anti ni zan je na kwanta sai Allah Ya tashe mu".
Ta yi murmushi ta ce"To sai da safe".
Na shiga ɗakin da shi ne nawa, na canza kaya zuwa na bacci na kwanta bayan na murɗawa kofar key, na fara tunanin ranar aurena da Sadam, da yadda ya nuna ba ya zumuɗin kusantata a ranar, duk na damu, amma a yau na ji ba na so wannan sabon mijin nawa ya kusance ni ma, na tuna darena na farko a gidan Ustaz, abubuwan da suka faru a gidan suka dinga dawo min, na fara istigfari, tun ina yi a fili har bakin nawa ya gaza saboda bacci da ya ci ƙarfina.
Can cikin bacci na ji ana ta bugun ƙofar ɗakin, na tashi a ɗan razane, na kalli agogo na ga sha ɗaya da rabi, na ƙarasa bakin ƙofar na ce"Wane ne?"
Na ji muryar mijina ya ce"Mu ne".
Na sauke ajiyar zuciya, na buɗe, da na ji ya ce su ne na yi zaton zan gan shi tare da matarsa ne, sai na gan shi shi kaɗai, gabana ya faɗi ban san dalili ba, raina kuma ya ɓaci, rayuwar aure da wanda ba ka so kuma shi ma ya furta ba ya sonk akwai ƙalubale, na daure na ce"Sannu da zuwa".
Na juya zan koma É—akin, a zatona shigowa zai yi, sai na ji ya ce"Ko zo ki same mu a falo".
A raina na ce Ashe dai su biyun ne, to bibiyar me take yi masa? Ni kam zan faɗa mata ta ja shi kawai su tafi na bar mata, na zura hijjabina na bi shi, amma muna ƙarasawa falon sai na ga ba ta nan, na zauna a kujerar nesa da shi, ina kallon gefe, a jikina na ji kallona yake yi, muka yi 'yan sakanni a haka kafin ya ce"Sayyada".
Na ce"Na'am".
Ya ce"Ba ma son raini, za mu jure komai amma ban da raini, kuma kuma Hajiya Halima ba sa'arki ba ce, idan kika ce za ki raina ta to hatta ruwan gidan nan sai ya yi miki ɗaci, tun tuni mun faɗa miki muna sonta, don haka ba za mu juri ƙananun iskanci ba".
Na yi shiru ina ta mamaki, na ce"Amma wannan gargaÉ—in duk na mene ne? Na ce maka zan yi fitina da wani a cikinku ne?"
Ya ce"Ok, mun lura har yanzu akwai rashin kunya a kalamanki, to ki kwantar da hankalinki, nan ba da jimawa ba za ki saitu, amma yanzu ki tafi ki je ki ba ta haƙuri, ki ce ba za ki sake yi mata abin da kika yi ba, idan kuwa kika sake to mun san hukuncin da za mu yi miki".
Na haÉ—e gira na ce"Me na yi mata ne?"
Ya ce"Ta ce ta zo ɗakin nan don ta taya ki fira, sai faɗa mata maganganu marasa daɗi, ƙarshe ma kika tafi kika barta a falon".
Na yi sororo ina kallon shi, ma ma kasa musawa.
Ya ce"Haƙiƙa mun sani rashin kunya halinki ne, to ki sani ba za mu lamunta ba, ki tashi mu je ki ba ta haƙuri".
Na ce"To".
Na tashi na bi bayansa kamar raƙumi da akala, muna shiga falon, ba ta nan, ya nufi ɗakinta, ni kuma na zauna a kujera ina jiran ganin ikon Allah, tsayin mintuna sai ga su sun fito tare, suka zauna suna kallona kamar yadda nake kallonsu, ya ce"Sayyada mun kawo ki ne don ki kalle ta ko kuma kin zo ba ta haƙuri ne?"
Na ce"Hajiya don Allah ko zan iya sanin maganar da na faÉ—a miki mara daÉ—i? Wai saboda gana na kiyaye ko".
Sai kuwa ya daka min tsawa da faɗin"Ke! Ya isa haka, ba ma son raini fa, ki ba ta haƙuri aka ce".
Na danne zuciyata na ce"Ki yi haƙuri".
Ya kalle ta ya ce"Kin haƙura?"
Ta ce"Mai martaba kenan, ba don ma kun dage ba ni ban so kuka faɗa mata ba, babu komai na haƙura ta ci albarkacinku, ƙanwata ce ba zan yi fushi da ita ba".
Ya yi murmushi ya ce"Tana godiya, tana sake neman yafiya, a yafe mata, rashin sani ne da rashin kunya irin na yaran zamani".
Na tashi ban ce komai ba na fice daga É—akin, na yi sa'a bai tsayar da ni ba, na koma É—akina ina ta mamaki, kenan ita kuma nata salon kishin kenan? Yanzu wannan kissa ce hakan ko mugun hali?
Ɗaki na koma na don cigaba da baccina, sai dai babu jimawa na ji dawowar shi, dayake ban rufe ƙofar ba, sai ya leƙo ya ce na fito falon, na tashi cikin ƙosawa ina jin ya fara shiga haƙƙina tun da bacci nake ji.
Na manta ma ban tsaya saka hijjabin ba, sai da na ga yadda yake bina da kallo sannan na tsargu, amma na maze na zauna ina cewa"Ga ni".
Ya ce"Sayyada barka da zuwa sabuwar rayuwar aure, ina yi mana fatan alkhairi da fatan zaman lafiya, duk da dai ba ma son juna, amma ya zama dole mu mutunta juna, kuma mu bawa juna hakkin da shari'a ta tanadar, hakane?"
Na ce"Haka ne".
Ya ce"Za ki ga kamar mun kai ki ki bawa Hajiya haƙuri ne saboda ƙasƙanci, a'a sam ba haka ba ne, muna son nuna miki ba zai yiwu daga zuwanki ki fara kawowa wacce kika tarar a gidan nan raini ba, tana da sauƙin kai, kuma duk kishinta ba ta hana mu aurenki ba, sannan muna jin tausayinta, saboda ba ta haihuwa, kuma ba za ta haihu ba, don hakaya zama wajibi ke ka ki girmama ta, ku zauna lafiya, wannan shi ne kwanciyar hankalinmu".
Na ce"To in sha Allah".
Ya ce"Ina É—an namu, ya yi bacci?"
Na ce"Ban taho da shi ba, Mama ta ce sai an kwana biyu".
Ya ce"A'a muna buƙatar shi a kusa da mu da wuri, za a kawo shi gobe in sha Allah, ina son haihuwa, ina son yara, da fatan idan Allah Ya kawo ba za ki gaji ba wajen zazzago su".
Na ce"Allah Ya kawo masu albarka".
Ya ce"Mun lura jikinki ya fara sanyi ba kamar haÉ—uwarmu ta farko ba, shin mun fara yi miki kwarjini ne ko kuwa kin fara sonmu ne?"
Na ce"Na yi niyyar yi wa iyayena biyayya ne".
Ya ce"To shikenan za mu gani".