← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 89

Sashe 15

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta ce"La haula wa la ƙuwwata illa billah! Haba Sayyada, ke kuwa wane kalar kishi ne da ke? Kishiya kanki farau? Waɗanda aka yi musu ɗin mutuwa suka yi? To wallahi ki kiyaye ni Sayyada, ko dai ki kwantar da hankalinki ki yi haƙuri, ko kuma ki ƙarasa ɓarar da garinki a wajen mijinki, domin yanzu yadda ya yi sabuwar amaryar nan babu abin da ba za ki gani ba".

Na kashe wayar na ajiye, ina ji tana kira na ƙi ɗagawa, to me za ta ce min? Na gama lura babu wanda ya san yadda nake ji, ba za a fahimce ni ba, faɗin kukan da na sha a ranar ɓata baki ne, fuskata ta kumbura ta yi ja, ga shi Sadam bai dawo ba, babu wanda ya zo gidan a dangina ko ƙawaye, kodayake wa ba gayyata? Dama Anisa ce nake tunanin zuwanta, kuma ba ta zo ba, ta ma kashe wayarta, nan take na ayyana ƙila ma don ni ta kashe don kar ta zo, haka ba wuni cikin wani hali, amma hakan bai sa na ƙi jin yunwa ba wajen ƙarfe uku, ni dai na ga baƙincikin da zai sa na kasa cin abinci, shayi da biredi na sha tsaye a kitchen, na nemi waje na zauna a ƙasa dirshan, kawai gani nake duk duniya babu mai sona a yanzu sai Mama, ita kuma ba ta iya ja da maganar Baba, don haka ita ma ba ta da wani tasiri idan ba addu'a da take cewa tana yi mini ba, da na yi tsam na yi tunani sai na ga to idan haka ne mene ne amfanina? Ba ni da wani sauran amfani, idan na mutu ni kaɗai ce na yi asarar rayuwata, Sadam dai ba shi da asara tun da yana da wata matar a yanzu wacce ya ma fi so, iyayena suna da wasu 'ya'yan bayan ni, wanda nake da tabbacin yanzu sun fi son su fiye da ni, tun da su ba su saɓa musu ba suna yi musu biyayya, sannan ni ba ɗa ba ballantana jika, da na haihu shi ne nake da tabbacin yarana za su koka idan na mutu, tun da kuwa ba mai damuwa da mutuwata ai ya kamata a ce na mutu kawai, sauke idona da na yi a kan wuƙa ya yi daidai da tunawa da hukuncin wanda ya kashe kansa, kafin ma na mutu na tarar da wannan hukuncin ita kanta azabar da zan sha na tuna ta, tun da ban manta raɗaɗin da na ji ba lokacin da na yanka hannuna, ba zan kashe kaina ba, ba zan sake cutar da kaina a kan Sadam ba, don bai cancanci haka ba, sai dai na cutar da shi, 'Kashe shi zan yi?' Na yi wa kaina tambayar a zuciya, wata zuciyar ta ce'Mene ne ribarki idan kin kashe shi an kama ki kin ƙare rayuwarki a gidan yari?'

A fili na furta "Babu! Shikenan kawai ya riga ya cuce ni".

Gidanmu kawai zan tafi, ko kashe ni Baba zai yi sai dai ya yi, amma ba zan iya wannan zaman ba na takaici, na É—auki waya na kira Mama, tana É—auka na ce"Mama ki yafe min, don Allah ki cewa Baba ya yafe min".

Mama ta ce"Sayyada ai mun yafe miki, me kuma ya faru?"

Na ce"Gani nan a kitchen riƙe da wuƙa zan kashe kaina na huta, tun da babu mai sona babu wanda ya damu da rayuwata, Mama zan kashe kaina fatana kawai ku yafe ni".

A matuƙar ruɗe Mama ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi! Sayyada! Kar ki yi, kar ki sake ki aikata wannan babban kuskuren, don Allah kar ki cutar da kanki, ki kamo hanya ki taho gida, Babanki zai karɓe ki, ki tuna rainon ciki da zafin haihuwa, ki tuna shayarwa da rainonki da na yi har zuwa girma, ina son ki har gobe, har abada, idan kika illata kanki ba ki yi mini adalci ba, kuma sai Allah Ya yi mana hisabi da ke" Ta fara kukan da ya tashi hankalina.

Ni ma cikin kukan na ce"Shikenan Mama, na fasa, ki daina kuka, zan haƙura na zauna har ciwon zuciya ko na damuwa ya yi ajalina, zan zauna da Sadam baƙincikinsa ya kashe ni Mama..." Na rushe da kuka.

Ita ma kukan take yi ta ce"Sayyada ki taho gida na ce, ki haÉ—a kayanki ki taho gida".

Na ce"Ba na son abin da zai ja miki matsala da Baba, Mama ba na so..."

Ta daka min tsawa ta ce"Na ce ki taho gida!"

Da sauri na ce"To, gani nan".

Na hau haɗa kayana a babbar jaka, na tattara komai nawa me amfani na saka hijjabi na bar gidan, mai gadi bai hana ni ba, tun da ba a ba shi wannan umarnin ba, ina zuwa ƙofar gida na tarar da Baba yana alwalar sallar la'asar, gabana ya fara faɗuwa, haka na daure na tunkare shi, ina hawaye, na duƙa na gaishe shi murya a dashe, ya bi ni da mugun kallo kafin ya ce"Ina za ki je da wannan uwar jaka?"

Na ce"Gida na dawo Baba, na gaji da auren nan, don Allah ku yafe ni, na tuba, wallahi na gane kuskurena".

Baba ya ce"Maza ki koma inda kika fito, wallahi ko sakinki ya yi na faÉ—a miki ba ki da matsuguni a gidana, ni da ke har abada! Sayyada cutarwar da kika yi min ki sani sai Allah Ya yi mini hisabi da ke, ki koma inda kika fito, kuma idan kika je gidan wani É—an'uwana ban yafe miki ba!".

Ya tafi masallaci ya bar shi tsaye ina kuka, ga masu wucewa zuwa masallaci sai kallona suke yi, ban ji maganarsa ba, haka na ja ƙafa na shiga gidan ina ƙara sautin kukana, Mama ta zo ta rungume ni tana kukan ita ma, ta ce"Sayyada duk na jiyo tattaunawarku, ba ki da wajen zuwa da ya wuce nan gidan, so yake ki shiga duniya ko kuma zama za ki yi ɗan iskan mijinki ya kashe ki?"

Ta tura ni a ɗakinmu na yara, ina kuka, ta zaunar da ni, tana cewa"Idan har ya hana ki zama to ni ma ba zan zauna ba, sai dai mu tafi tare, me yasa maza ba su san ciwon mace ba? Ai ni dama na sani, mijinki ba zai taɓa daraja ki ba, saboda kin cuci kanki ki ɓarar da darajarki a idonsa".

Zuciyata ta cika da fargabar hukuncin da Mama take son yankewa, na ce"Mama don Allah kar ki yi haka, kar ki bari Baba ya yi fushi da ke, tun da kuka haife ni na taso ban taɓa ganin kun samu saɓani ba sai ta silata, idan aurenki ya mutu ta dalilina wallahi na cika asararriya, ba zan yafewa kaina ba, rayuwata ma ba za ta yi albarka ba, zan tafi Mama ki yi min addu'ar fatan alkhairi, na yi miki alƙawarin ba zan taɓa sake aikata kuskuren da na aikata a baya ba, zan tsare mutuncina a duk inda nake".

Mama ta ce"Me da me yake yi miki ne? Abun ya yi tsananin da ba za ki iya haƙuri ba?"

Na ce"Komai ma yi min yake ma, abubuwan ba za su faÉ—u ba".

Ta ce"Ki zauna, ko yaya ne ki ba shi iska, zan faÉ—awa Babanki ba ki shigo ba, sai ki bari sai ya fita sannan za ki dinga fitowa tsakar gida".

Na gyaÉ—a mata kai alamar na amince.

Ta tashi ta bar ɗakin. Baba yana dawowa daga masallaci ya fara faɗa yana tambayar ina nake? Da sauri na ja jakata na laɓe a bayan ƙofa, ina ji Mama tana ce masa ban shigo ba, ya cigaba da sababi yana cewa ko gidan wani nashi bai amince na je ba, gawata kawai zai gani ya yafe min abin da na yi masa, na guntse baki ina sakin kuka, yanzu idan ya riga ni mutuwa fa? Hakan na nufin ya tafi bai yafe min ba? Wace irin zuciya ce da Baba?

Da daddare Mama ta kawo min abinci na ci, ta zauna tana ta kwantar min da hankali. A haka na yi sati ɗaya cir a gidanmu, ba na taɓa fitowa sai Baba ba ya gidan, na yi mamakin yadda Saddam bai kira ni ba, na sake tabbatarwa ba ni da wani sauran mutunci a idonsa, wato ya samu amarya har ya manta da ni, hankalina har ya fara kwanciya, saboda da gaske fa ba na son ganin Sadam ballantana aurensa.

Ashe shi duk bai san wainar da ake toyawa ba, yana sane ya ƙi kirana, ya ƙi zuwa gidana, saboda ya hukunta ni da hakan, bai taɓa zaton ba na gidan ba, sai da ya gama sati ɗayansa da amarya cikin kwanciyar hankali, a ranar da ya dawo gidana ya ga ba na nan, mai gadi yake faɗa masa ai tun ranar aure da na fita ban dawo ba, hankalinsa ya tashi.

A ranar ina kwance ina bacci da safe ina jiyo firar Mama da Baba a tsakar gida sai ga kiran Sadam ya shigo wayata, da yake a silen take ban sani ba, sai da ya yi kira uku, a na huÉ—un ne na ga waya tana haske, ina ganin sunan shi gabana ya faÉ—i, na kashe wayar bakiÉ—aya, babu jimawa kuma na ji sallar yaro, tare da faÉ—in"Wai Sadam yana sallama da Sayyada".

Ƙirjina ya doka da ƙarfi, har sai da na dafe shi, Baba ya ce"Ka je ka ce babu Sayyada a gidan nan".

Yaron ya dawo ya ce"Wai ya ce mijinta ne, yau sati É—aya ba ta gidansa".

Mama tuni gumi ya fara yanko mata, ta É—auki buta ta shige banÉ—aki, Baba kuma gabansa ya faÉ—i ya yi tsam da jin ashe ban koma gidana ba, amma ya maze ya ce"Ka ce masa ba ta zo nan ba".

Ina ɗaki a tsaye a bayan ƙofa ina ta gumi sai jin sallamar Sadam na yi ya shigo cikin gidan, na ƙara ruɗewa, ya gaishe da Baba ya amsa a taƙaice, Saddam ya ce"Baba dama Sayyada ce..."

Baba ya katse shi da faÉ—in"Ba na son jin komai! Ta zo nan amma ko gidan ba ta shiga ba ta koma, don haka sai ka san inda za ka tafi nemanta".
Chapter 15 · 0% Book details