Sashe 71
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na yi shiru, ban tanka ba, na tashi na je na tafasa masa shayin na kawo masa, na sako tuwo na zauna ina ci, ya ce"Ina Dauda ko ya yi bacci?"
Na ce"E ya yi bacci".
Ya ce"To gobe kina da baƙi, 'yar'uwarki Anisa da mijinta, ɗazu yake faɗa min za su zo gobe su yi dinner a nan".
Na ce"Allah Ya kawo su lafiya".
Ya ce"Sai dai kuma gobe ba ranar kwanaki ba ce, Hajiya ce da ni, kin ga sai dai ki je ɓangarenta ki zauna don me girki ita ce mai saukar baƙi".
Na ce"Ko baƙin ba nata ba ne? Indai wajena za su zo me zai kai su wajenta?"
Ya ce"Haka tsarinmu yake".
Na ce"Babu damuwa".
Na gama na tashi na tafi ɗakina, na yi shirin bacci na kwanta, can wajen ƙarfe goma kawai sai na ga kira, kafin na ɗaga ta katse alamar flashing ne, na duba abun mamaki sai na ga shi ne, kafin na ajiye wayar sai ga wani flashing ɗin, na ajiye wayata, ai kuwa bawan Allah ya ce mu je, ya dinga flashing babu ƙaƙƙautawa, mamaki ya kama ni, na kira shi, sai ya ɗauka, na ce"Na ga ana ta flashing".
Ya ce"Amma dai kin san ba za mu rasa kati a wayarmu ba ko?"
Na ce"To amma me yasa ba za ka yi kira ba?"
Ya ce"Ba wayar ce buƙatarmu ba, ki zo ɗakinmu za a ba ki hakkinki".
Ya katse kiran, na yi turus ina jin ba na son wannan zuwan, amma ba ni da hujjar ƙin zuwa, na tashi na tafi, ɗakin babu haske, don haka na yi lalaube na ƙarasa gadon, ya ce"Sayyada, daga yau idan kin ga muna yi miki flashing to kiranki muke yi, don mu yi amfani da ke, ba wai don ki ɗaga mu yi magana ba".
Na ce"To".
"Wai me yasa ba za ki dinga kwana a É—akinmu ba ne?" Ya yi maganar yana janyo ni jikinsa
Na ce"Ai zaɓi ka ba ni shi ne na zaɓi kwana a nawa ɗakin".
Ya ce"Jiya ba mu ji daÉ—in yadda kika sakar mana jiki ba kamar gawa, don haka yau ke za ki sarrafa mu".
Na yi shiru ina mamaki, a raina kuwa ina raya ashe ba ka shirya ba, ya ƙaraci gadarar shi ƙarshe ya sauke sauke sarautar a gefe ya samawa kan shi nutsuwa, da zan bar ɗakin ya riƙe hannuna ya ce"Yanzu sai gata kenan? Yau kwananki zai ƙare".
Na ce"Za ka yi kewata ne?"
Ya ce"A'a, kawai dai faɗa miki muke yi ko za ki buƙaci a ƙara ba ki hakkinki, kar mu bar ki da kewarmu ta kwana biyun".
Na ce"Ni ba zan yi kewarka ba".
Ya ce"Ok, nan gaba za ki yi".
Na fita daga É—akin, ina tunanin me nake ji a game da shi? Akwai alamun zan so shi kuwa? Cikin mu'amalar auren dai ba na karantar komai, amma ban sani ba ko zan samu lafiya a gaba.
Washegari tun da sassafe sai ga bugun ƙofar ɗakinmu, a tare muka fito da shi, Hajiya Halima ce cikin ado, ta duƙa ta gaishe shi, ya amsa yana cewa"Hajiya lafiya?"
Ta ce"Lafiya lau mai martaba, ranku ya daÉ—e Allah Ya ja kwana da zamaninku, kewarku ce ta hana ni sukuni, tun da gari ya waye girkina ya zagayo shi ne na kasa jurewa na taho tun yanzu na tafi da ku".
Ya fara murmushi ya ce"Ina godiya gimbiya Allah shi albarka, bari na yi wanka na fito".
Sai ta shagwaɓe kamar ƙaramar yarinya ta ce"Ni dai mu je na yi muku, kwana biyun nan da ba na yi muku har kun fara yin baƙi".
Takaici ya ishe ni, yau ga abun amai ba tashin zuciya, ni fa ba kishi nake yi da kalamanta ba, kawai yadda shagwaɓar ba ta yi mata kyau ba ne abun ya ban haushi, shi kuma da alama burgeshi take, don sai murmushin ƙasaita yake yi.
Ya ce"Da gaske mun fara yin baƙi? Kin san fa kin iya wanka gimbiyata".
Ta kama hannunshi za su tafi, na ce"Idan ya gama kwana biyu a ɗakin naki kafin ya zo wajena ki cire masa fatar jikinsa yadda ba zai yi baƙi ba".
Ya ce"Ke Sayyada".
Ta ce"Rabu da ita mai martaba, kun san ku hamshaƙan maza ne, dole ne kishi ya susutata".
Ta kalle ni ta ce"Hattara dai yarinya, za ki iya yi min rashin kunya na shanye, amma kar ki sake ki gwadawa yi wa mai martaba, domin kuwa kin taɓo wanda ba ni da saiti idan aka taɓa shi".
Ya ja ta yana cewa"Ki huce ranki ya daɗe, yarinya ce, a yi mata uzuri, akwai ƙuruciya".
Ta ja shi suka tafi, na bi su da kallo, na taɓe baki na koma na cigaba da baccina.
Da zai fita aiki ya shigo, ya ce"Mun shirya za mu fita, akwai abin da kike buƙata ne?"
Na ce"A dawo lafiya, ba na buƙatar komai".
Ya yi murmushi ya ce"Sayyada kenan".
Abiy ya yi wajensa, ya É—auke shi yana cewa"ÆŠana barka da safiya".
Sai kuma ya ce"Wai me yasa ba kya kaiwa É—aya babar tashi shi?"
Na ce"Aubdama yana da wata uwar bayan ni?"
Ya ce"Tun da kin yarda É—anmu ne, to É—an matata ne".
Na ce"To ai sai ka bari sai ta nuna É—anta ne tukunna ko?"
Ya ce"Hmm, ki kwantar da hankalinki, wannan rashin kunyar gaba ko an ce ki yi mana ba za ki yi ba".
Ya miƙo min wayar shi ya ce"Ki saka min account number".
Na ce"Me yasa?"
Ya ce"Ba tukuicin daren jiya zamu ba ki ba, ballantana ki dinga yi mana yanga, za mu ba ki ne saboda ko za ki yi baƙi idan kina so ki yi musu alheri, akwai su turare da wasu abubuwan da Hajiya takan siya saboda wannan, idan za ta siya za mu ce ta siyo da ke".
Na ce"Ba na so, indai sai ita za ta siyo".
Ya É—age kafaÉ—a ya ce"Kin huta".
Kafin ya fita na ga alert É—in dubu hamsin, na ce"An gode Allah Ya saka da alkhairi".
Ya ce"Ko sau É—aya ba za ki ce mana mai martaba ba? Sunan yana yi mana daÉ—i".
Na ce"Tun da kana da me faÉ—a maka ka je ta cigaba da faÉ—a maka".
Ya ce"To na gode".
Ya ajiye yaron ya fita yana yi masa bey-bey.
Wajen ƙarfe goma sai ga 'yan'uwana sun zo, ƙannaina biyu, maman Anisa, yayar Mama da ƙanwarta, ƙawayen Mama su biyu, da kuma ƙannen Baba su biyu da suke kusa, na kuwa ji daɗin zuwansu, a roƙe su suka wuni, muna ta fira, manya suka yi min nasiha sosai, na turawa ƙanwata kuɗin da na ara jiya, bayan la'asar suka tafi, da daddare ko girki ban yi ba, na ci sauran na rana.
Bayan sallar isha'i na ji shigowar mota, na san shi ya dawo tun da har ya leƙo mun gaisa, hakan ya tabbatar min da su Anisa ne suka zo, sai ga shi kuwa ya zo ya same ni ya ce"Baƙi sun ƙaraso, sai ki je ku gaisa a yi dinner gabaɗaya a can ko?"
Na ce"Ina gaishe su, amma ba sai na je ba".
Ya ce"Ban gane ba sai kin je ba, Sayyada kar fa ki bari mijinki ya yi shaidar rashin kunya, Anisa yar'uwarki ce fa".
Na ce"Idan har ita ba ta duba 'yan'uwantaka ta zo mun gaisa ba wallahi ni babu abin da zai kai ni na bi ta É—akin wata".
Ya ce"Shi kuma mijinta fa?"
Na ce"Mene ne haÉ—ina da shi? Idan ni ya zo yi wa murnar aure ai É—akina zai zo ba na wata ba".
Ya ce"Hmm, shikenan Sayyada mu ba za mu yi miki dole ba ki je don kanki, Allah Ya shirye ki, amma fa ki kwantar da hankalinki da sannu za ki saitu".
Ya bar É—akin, bayan wani lokaci sai ga Anisa ta shigo, muka gaisa babu yabo babu fallasa, ta ce"Sayyada Allah Ya sanya alkhairi ya ba da zaman lafiya".
Na ce"Amin Ya Allah".
Ya ce"Ga baban Amir can ya ce ki leƙa ku gaisa".
Na ce"Na gode ba sai na leƙa ba".
Ta fita tana yi min sai da safe, na bi bayanta da harara, ji nake a raina kamar yanzu da ta zo ta ga alamar ba a cikin tashin hankali nake ba ma haushi za ta ji, tun da na saka a raina hassada take yi min.
Bayan sun tafi ya shigo ya ƙaraci faɗansa ban ce masa ta tafasa ba, ƙarshe ya tashi ya ce"Sai da safe, matarmu mai ba mu cikakkiyar kulawa tana can tana jiranmu, wacce take neman hakkinta ba sai an kira ta an ba ta ba".
Na ce"Allah Ya sa ka kwana kana sauke mata wannan hakki".
RAUDA
Zuwa yanzu Rauda ta kai ajin ƙarshe a gajiya, ba dama dare ya yi ta matsa kusa da miji sai ya fara ƙorafin ya gaji, ita kuma ta dage ta ce ai haƙƙinta ne, ƙarshe kuwa abu ya zama faɗa, tana taɓa shi zai tashi zaune ya fara yi mata masifa yana faɗin"Wannan wace irin jaraba ce? Kamar ke kaɗai ce mace lafiyayyiya a duniya? Kamar ni kaɗai ni mai aure? Ba zan yi bacci ba ba zan huta ba kullum mace ta sako ni a gaba da jaraba? To gaskiya Rauda na gaji, duk yadda zan yi da ke ma ba yaba min kike ba, ganina kike yi kawai a lusari, idan kin san ke harija ce ba ki faɗa min ba ban yafe ba wallahi, kin shiga hakkina, ana aure ana ƙiba ni sai ramewa nake kamar wanda kike jan jinin jikina?"
Takaici ya ishi Rauda, ga zafin ba gamsar da ita yake ba, ga zafin maganganun da yake faɗa mata, da ma na rashin nunawa ɗanta kulawa, a fusace ta ce"To ƙarya na yi ba lusarin ba ne? Wallahi da zaman aure da kai har gara na san ba ni da auren ma, ban ga miji ba ballantana raina ya biya, basur ya cinye ka da sanyi ka ƙi ka nemi magani?"
Ya ce"Au! Haka abun yake? Da gaske da aurena gara babu?"