← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 126

Sashe 99

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asmah tace "menene?" Yace "su mummy ke Neman su saka mishi hypertension wai matar shi suka dauke zuwa gida wani wai zata yi wankan jego a gida." Ya karashe maganar yana shan U turn da motar suka dauki hanyar family hause, tace "to shine kake mishi dariya, yau dai ga mutum gobe gare ka." Yace "ina! Ba wannan maganar , aini babu Wanda ya isa ya min irin wannan talalan mai kamar tsaki, wlh bazan yarda ba kinji na rantse idan kuma suka matsa to sai dai su bamu daki ɗaya a gidan muyi zaman wankan tare." Tace "haka kace ko to a dai yi mu gani idan tusa zata hura wuta." Yace "za kuwa ki gani Allah dai ya kaimu lokacin." Tace "Amin kuwa" ganin yadda yake tukin a slow yasa tace "dan honey kayi sauri na matsu naje naga babyn mu."

Minti 20 ya dauke su, suka iso family hause, direct kuwa part din mummy suka yi,inda suke kyautata zaton samun su. Falon mummy cike da yan uwa Mami, ya Rabi'ah, batool, Khadijah, hajiya mama, kamal, da kuma Amir. A na zazzaune fuskar kowa cike da farin ciki banda Amir dake ta ciccin magani.

Asmah ce a gaba tana sallama batool ta taso da sauri tana mata oyoyo kamar yadda suka saba yi ma juna da tirtsetsen cikin ta da ko nauyin shi bata ji, cike da kulawa ta tare ta tare da cewa"ayya yar uwa da kin bari ni na karaso na miki ai." Aslam dake Bayan su ganin sun tare mai hanya yasa yayi gyaran murya, sauri batool ta sake ta, tare da kallon gefen da ta jiyo muryar ya Aslam, suna haɗa ido ya galla mata hararan da saida babyn cikin ta yayi zillo. da sauri har tana dan risina wa tace "sannu da zuwa ya Aslam, ina wuni." Bai amsa ta ba sai ma qare hade rai da yayi kamar bai taba dariya ba, kallon shi Asmah tayi ta juya ta kalli batool da tayi tsuru ta dukar da kai kasa cikin ladabi. Kawai sai ta kwashe da dariya, ita ma hararan ya watsa mata, tare da bi ta gefen su ya shige falon, Jan hannun batool tayi suka bi Bayan shi, ita dai batool a tsora ce take, bata son taga ya Aslam cikin irin wannan fuskar, domin duk ranar daya tashi musu da irin wannan fuskar uban su yake ci, kowacce sai ta samu rabon ta a cikin su ranar ko mari ko rankwa shi.

Aslam dake gaba shiya fara karasawa gaban hajiya mama dake rugume da babyn ya asma, cike da farin ciki da wani irin so da shauki yake kallon babyn bakin shi yaki rufuwa take fuskar shi ta washe ya shiga sakin wani irin kayataccen murmushi, itama tana shigowa falon abinda idanunta suka hango mata kenan babyn dake hannun Aslam, da sauri ta saki hannun batool ta ƙarasa bagan shi tana kallon fuskar kyakkyawan yaron itama fuskar ta dauke madaukakin farin ciki.

Gaba daya mutanen falon kallon su sukeyi cike da sha'awa da tausayawa, kowa yasan yadda suke matuakar kaunar haihuwa gashi har yau allah bai basu ba, mika hannun tayi zata karbi babyn a hannushi ƙin bata yayi tare da ƙara rike babyn da kyau, sake kai hannu tayi zata karba ya kara hanata, sai kawai ta fashe da kukan shagwaba tana bubbuga kafa.

Muryar hajiya mama suka tsinta tana cewa "yayi kyau tantabaru sarakan soyayya, to muna nan dai." Cak ta tsaya da kukan da take yi kamar wacce aka danna mata stop, dariya su batool dasu ya Rabi'ah suka saka musu, harga Allah hankalinta bai kai kan mutanen dake falon ba gaba daya idanunta ya makan ce babyn su kawai ta ke gani, a kunyace ta juya ta karasa gurin hajiya mama dake zaune ta rungume ta, ture ta hajiya mama ta shiga yi da wasa tana cewa "ni daga ni dallah can karki karkare ni." Batool tace "lallai ji matar nan ma dan ma kin gode ta rungume ki, kema sister ga Mami da zaki rungume kinje kin rungume wannan taohuwar." Hada idanun da sukayi da Aslam ya dalla mata harara yasa tayi shiru.

Gaishe da sauran mutanen falon tayi su Mami ta musu barka sannan ta nemi guri ta zauna kusa da Khadijah dake ta sakar mata murmushi, Khadijah tace"naji muryar ki yar uwa amma wlh kafata tayi tsami na kasa tasowa na tare ki." Cike da tausawa take binta da kallo tayi wani ƙiba, kafafun ta duk sun kumbura. Tace "ayya sister sannu kuma Allah ya sauke ku lafiya." Gaba daya aka amsa da amin.

Hajiya mama ta kalli Aslam tace "to ai sai ka bata ɗan ita ma ta dauka ko." Kallo ta yayi tayi narai narai da ido, tayi fuskar tausayi suna hada ido ta sakar mai kallon pls mana, badan ya gaji ba ya mika mata, innalillahi Aslam ji tayi kamar ta maida babyn cikin ta gaba daya ta tattara dukkan hankalin ta akanshi tana kallo tana sakin murmushi.

Fira aka shiga yi amma ita kwata kwata hankalinta baya Kansu bata San me ake cewa ba, batool kuwa duk ta takure don duk haɗa idanun da zasuyi da ya Aslam sai ya banka mata harara gajiya tayi ta mike salin alin ta nufi dakin su Nada dake upstairs kusa dana mummy inda nan ne dakin da Amira zata zauna, tana shiga suna fitowa daga toilet da alama wanka akama Amira, batool ta kalle ta tayi wani jajur abinka da farar fata, mummy tace yawwa batool dauko babyn ki kawo shima a masa wanka, komawa tayi da nufin amsar babyn a hannun Asmah takai ma mummy ƙememe Asmah taki bata, ta kara kamkamewa sai dariya su Mami ke mata, kar she dai cewa tayi ita da kanta zata kaima mummy yaron, haka suka rankaya ita da yar Aiken suka koma sama, samun Amira sukayi ta saka kaya riga da zani harda sock da dan karamin hijjab mummy ta zuba mata ruwan zafi sai sha takeyi tana yarfe zufa, ga ɗakin dunɗum ko fanka ba'a kunna ba balle Ac, kallon juna sukayi suka sake kallon Amira

dake kurban ruwan zafi, takr batool taji cikin ya bada ƙulululu.....
,

Oum Ummeetarh
07041130088.
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqanñjjn iyayen mu}

Page 122

Tana jin labarin jego jego kuma tana farƙgaban wankan nan da aka ce mata ana yi da tafasashen ruwa, yanzu kuma ganin Amira na kurban ruwan zafi sai abin ya ƙara girgiza ta wato bancin wanka da tafasashen ruwa har tafashen ruwan mutum ke sha, bata gama wannan tunanin ba taga mummy ta miƙo ma Amira kunun kanwa cike da Kofi sai tiriri yake, "oya maza maza ki kurɓe shi da zafi zafin shi ki gaggasa cikin ki jego ba abin wasa bane." Kwabe fuska Amira tayi zata yi kuka, mummy tace "oh lallai a haka da mijin ki ke neman mu bashi ke ya tafi dake gida, gashi a agaban muma kenan, to bari na gaya miki cikin ci nan naki a halin yanzu danye ne sharaf, kamar gwambo. shan abubuwa masu zafi su zasu saka ya warke, idan kuma kika ƙi sha ki ruɓe, kita wari sai dai kiga Amir ya auro galliyar amarya ya aje ki a kwandon shara." Ba Amira ba hatta batool da Asmah sai da suka zaro ido mummy tace "kwarai kuwa ba kun wani ƙolalo min idanu ba, wannan wankan da shan ruwan zafin nan da shiga ruwan zafi da tsarki,da cin abinci sosai mai jego taci abinci sosai taci tuwo tasha kunun kanwa tasha shayi ta koshi ta gasa ciki shine jego, in kika ƙi yin waɗannan abubuwan wlh kanki zaki cuta, bari na baku labari, lokacin muna yan mata a unguwar mu, wani gida akwai wata mata data haihu, taki yarda a mata wanka taki yarda tayi tsarki da kyau, taki shan ruwan zafi,wacce aka kawo mata dan ta ringa mata wanka tayi tayi da ita taki, kawai sai ta kyale ta, hmmm kunsan me ya same ta kuwa." Har suna haɗa baki wurin cewa "A'a mummy." Tace "to haukacewa tayi" batool cikin ta shin hankali tace "haukacewa fa kika ce mummy." Amira kam tuni ta kafa kofin kunun kanwa abaki ta fara kwankwaɗa, mummy tace "kwarai kuwa hauka tuburan, tana zaune kawai sai a ga tana zabure zabure kamar ta ɓaɓɓiya aka rasa mai ke damun ta, karshe miji ya koreta Gidan su ya dallo amarya." Asmah da duk tafi su ruɗewa tace "ta yaya aka gane rashin yin jego da kyau ne ya saka ta hauka." Mummy tace " labarin Nada tsowo kudai bari na barku a nan, dare nayi kuma zanwa yaro wanka." Ta amshi babyn a hannun Asmah ta fice dashi.

Zama Asmah tayi a bakin bed jiki a sanyaye tace "Allah mun gode maka, abubuwa iri iri daga wannan a shiga wancen,Allah dai ya raba ku dashi lafiya kuma." Ta faɗa tana kallon batool, "ke kuma Amira wlh ki tsaya kiyi wanka nan da kyau kin dai ji abin da mummy tace idan ba'ayi da kyau ba haukacewa akeyi ni wlh duk jiki na yayi sanyi, gashi haihuwar ma ba karamin azaba bane dashi aka ce." Zaro ido Amira tayi tare da cewa "kaiii azaban ma, in kinji azaba kara mashi S." Batool da duk ta ƙara tsurewa tace "dan Allah sisters mu bar wannan zance kar kusa na kasa barci yau."dariya suka saka mata Amira tace "yar banza ga tsoro ga mugun aiki." Itama dariyar ta kama yi tace "wlh Allah jikiña yayi sanyi, ga kuma wancen mutumin sai harara na yake yi, tunda ya shigo falon nan yake ta auna min harara, duk hankali ya tashi wlh."Amira tace "wa kenan" tace "wa kika sani banda yaya babba" Asmah ta kwashe da dariya tare da cewa "Zakiyi bayani ne, duk rashin M din da kika gama zazzaga mishi a waya ɗazu a kunnen shi." Dafe kirjinta da yayi wani irin buga wa tayi tare da cewa "dan girman Allah." Asmah tace "wlh kuwa" daura hannu tayi aka tare da cewa "na shiga uku na ni batula." Duk dariya suka shiga yi mata Asmah naba Amira labarin yadda abin ya wakana.
Chapter 99 · 0% Book details