← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 126

Sashe 31

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amira kam bata ɗakin tana cen wajen Amir dinta suna hira a main falo, saidai ta dawo aka gaya mata ,me zatayi kuwa itama ba dariya ba , haka suka saka ma batool zafi ranan ,ita ko kasancewar jikin ta ya mutu yasa ta kasa tankasu,

Saidai sukayi mai isarsu suka kyaleta, har ummi dake abuja saidai zahra ta kirata ta bata labari, kasancewar sun dauketa kamar kawarsu basa boye mata komai, itama ummi dariya tayi , tace gulmammiyar banza ku kyaleta kawai nan gaba zata gane kuranta,

Shima bash a nashi bangaren kasa sukuni yayi yau gaba daya bai sakata a Ido ba bai ji muryarta ba ,baiga dan cikulin bakinta dake bala'in burgeshi na murgudawa ba , duk sai yake jinshi kamar Mara lfy,

Kasa daurewa yayi dole ya lalubo wayar shi ya danna ma lambarta da ya dauka a wayar Amir kira,

Tana kwance jiki a mace call ɗin ya shigo wayar ta, ganin number mara suna yasa taqi dagawa har ya katse, sake kira yayi dan haka ta daga, danjin wake damunta a tsohon Daren nan,

Shiru tayi batace komai ba kuma bata katse kiran ba ta dai daga ta kara a kunne,

Daga can bangaren Dr bash yayi sallama, tunkan ya karkare sallaman ta gane muryan shi, take wani dadi ya lullubeta, bata San sanda ta saki murmushi akan laɓɓanta ba

Amsawa tayi, tare da tambayar "dan Allah wake magana" shima acan bangaren yace "pls dawa nake magana".

Miqewa tayi daga kwnacen da take ala dole bata gane shi ba tace "Mallam ya zaka kirani kuma kana tambaya wake magana, bakasan wacece ba ka kira," danne dariyar sa yayi ya dake yace "nima gani nayi anmin flashing da wannan number yanzu , shiyasa na kira naji kowa ke damuna cikin wannan Daren,"

Zaro ido tayi waje jin sharrin da zai mata wai tamai flashing, tace " wlh ya bashir kaji tsoran Allah niban kiraka ba banima da lambarka"

Dariya ya kwashe dashi yace"Ashe dai kin gani ne, ni zaki kawowa rashin M kice wani wake magana, to Dr bashir ne yaro mai farin jini san kowa kin Wanda ya rasa, kyakkyawa ajin farko, ba irin wata ba"

Aiko nan ta shiga kushe shi, shi kuma yana wasa kansa yana tsokanan ta , yana kunna ta bai barta ba kuwa saidai ya sakata kuku, su karan Kansu basu San dare ya tsala haka ba saida suka kashe kiran ,

Washe gari da misalin sha biyu na rana Aslam ya isa school ɗin su Asmah, daidai lokacin ta fito daga, canteen ruwa ta siya ta sha dan kishi takeji, zahra kuma taki rakata wai akwai rana,

Tun daga nisa ya hangota , cikin tafiyarta mai jan hankali, shagala yayi da kallonta kafin kuma a hankali ya furta"ya Allah ka mallakamin wanna baiwar taka badan halina ba Allah badan na isa ba," gani zata wuceshi yasa ya tada motar nufanta yayi gadan gadan kamar zai tureta da mota , har ta gama sadaqar wa ta mutu, ya taka burki a gabanta daf da ita, fitowa yayi ya sha kwalliya sosai cikin kananan kaya,sai zuba kamshi yakeyi, don kuwa saida ya tsaya ya mata kwalliya mai sunan kwalliya sannan ya baza turare ya kamo hanya,

.ganin ya Aslam yasa gaban ta yankewa yayi mugun faduwa, nan ta shiga a'uziyya a zuciya ,

Takowa yayi gabanta ya jingina bayanshi da jikin motar, zura hannaye a aljihu ya zuba mata idanu, itama dai ƙuri tamai idanunta cikin nashi babu alamar kunya ko shakkar shi a cikin kwayar idanunta sabanin da ,da idan ta ganshi ko daga kai bata iyayi a gabanshi balle har ta kalli cikin idanunsa,

Ganin kallon kudan yaƙi ƙarewa yasa tace "lafiya Mallam zaka tsaidani a tsakiyar hanya, inada abinyi fa" ta fad'a cikin hade giran sama data kasa,

Dadi ne ya lullubeshi shi jin muryarta daya dade yana begen ji,

Murmushi mai ciwo yayi yace"husnah ina sonki"

Idonta kur cikin nashi tace"karya kakeyi Aslam baka sona kuma baka taba sona ba,yaudaran kanka kakeyi da cewa kana sona, bakin da ya furta ki koya zo ya furta so daga baya karya ce kawai, to barin gaya maka ko ka soni ko ka qini Aslam ni bana sonka bana sonka bana sonka , ka fita a hanyata Kamal nakeso domin shine ya soni ya tallafi rayuwata tun bansan kaina, " hade hannayenta tayi alamar roko , tace"dan Allah na roqeka Aslam karka kara shiga sabgata, domin na zama mallakin wani , nan da yan kwana ki , zan zama mallakin farin cikin zuciyata kamaluddeen"

Tana kaiwa nan ta juya a fusace kamar kububuwa ta barshi nan tsaye kamar mutum mutumi,

Ya kusa kwashe twenty minutes a tsaye a wurin bayan wucewarta, kafin ya shiga motar shi ya figeta da wani irin mahaukacin gudu yabar cikin school,

Zaune suke a chicken republic, sunyi order abinci , kowaccensu cikin kwalliya ,da kagansu kaga manyan bebs, ma'aikacin wurin ne ya gabatar musu da abincin da sukayi order, ana ajiye abincin kamshin shi ya bigi hancin zee take taji zuciyata na tashi, amma haka daure ta kai loma daya bakinta,wani irin amai ne ya taso mata, mai karfin kan kace koba ta shiga kelayashi a cikin mayafinta, yawancin mutane dake wurin masu kyama , tashi suka dingayi suna fita da gudu,

Ma'aikatan gurin ne sukayo kanta suna mata sannu, beebalo ma ba'a barta a baya ba , saidai ta amaye abincin da taci ranar kaf, beebalo ta tallabeta , ta kaita toilet ta wanke fuskarta da bakinta,

Mayafinta kam cleaner din gurin ta dauke ta saka a bola ta gyara wurin,

A mota bayan sun fito daga wurin hade kanta da sitiyari , tayi, tana sauke numfashi, beebalo da tun d'azu ta diga mata ayar❓ta kalleta tace "kawata badai ciki kikayi ba," da sauri zee ta dago ta kalleta tace "ci me" beebalo tace "ciki "zee ta girgiza kai tace "ina ba zai yuwu ba ciki adan shekaruna , ke bani da wani ciki " beebalo tace "taya kika tabbatar baki da ciki , yaushe rabonki da al'ada" take gaban zee ya fadi don ita ta manta da wani Abu waishi al'ada,don kan aurenta da Aslam rabonta da shi,

Ganin yanayin rudun da ta shiga hakan ya tabbatar ma da beebalo hasashenta ya tabbata kenan, murmushin mugunta tayi a zuciyata tace"na samu hanya mai sauqi da zan rabaki da aslam har abada , wawuya kawai, kin mutu tunda kia dauki amana kika damƙama beebalo taƙizama"....................

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabilillaha🙏
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Page 65 & 66

Beebalo ta kalli zee tace "ke nake saurare ƙawata nace yaushe rabonki da ,period" zee tace"tun kafin bukina yau wata biyu kenan" beebalo tace"tabdijama aikam dai bamuga ta zama ba, dole ne muje a gwada mu gani ko cikin ne, " zee tace" a'ina zamu gwada bayan yanzu dare ne ko wani asibiti mukaje kinsan dai zasuce muje mu dawo gobe ne, kawai mu bari goben sai muje, " murmushi beebalo tayi tace, " ba asibiti zamuje ba kedai kawai kibar komai a hannuna, tabbatar cikin kawai muke da buƙatar ji yanzu, muje pharmacy mu siya P-test mu gwada mu gani,"

Tada mota zee tayi suka gangara na'uzo family pharmacy suka siyo P-test din har guda biyar ,

Gidan su beebalo dake unguwar limawa suka nufa , gida ne da ba kwabo komai yaro yaga dama yayi , toilet suka nufa zee tayi fitsari a wani dan karamin kwalba irin na turaren duri, saka abin gwajin sukayi, minti daya kuwa ya nuna musu layi jajaye guda biyu,

Ciki ya tabbata a jikin zee, ɗaura hannu tayi aka tace "na shiga uku ni zainabu na lalace, wlh bana son cikin nan ban shirya haihuwa yanzu ba , wlh bana son jikina ya lalace, yanzu dana haihu shike nan , nono na zai zube abubuwa da yawa zasu canja a jikina , Aslam zai daina sona, zanyi saurin tsufa, ", beebalo tace baki shiga uku ba ƙawata ni zan tsaya miki mu zubar da cikin nan cikin sirri yanda ba Wanda zai Sani, muyi abin mu mu binne , ajiyar zuciya ta sauke, ta rungume beebalo, tace"nagode ƙawata Allah ya bar kauna," hararan bayanta beebalo tayi sannan ta amsa da "amin amin ƙawata" a zuciyarta kuwa tana aiyana zakici uban ki ne yarinya,

ƙwance yake akan makekan bed dinshi, sai juyi yakeyi, tsakar dare ne don kimanin ƙarfe daya ne na dare,bacci gaba ɗaya yau ya kauracewa idonsa, kalamanta na yau ba karamin matsuguni suka samu a zuciyar shi ba , tunda yake wani magana bai taba tada mai hankali ba kamar yadda kalaman ta na yau suka tada mai hankali, ko wani motsi zaiyi sai kalaman ta sun fado mai a zuciya kamar a lokacin take sanar dashi kamar haka

(karya kakeyi Aslam baka taba sona ba,yaudaran kanka kakeyi da cewa kana sona, bakin da ya furta ki koya zo ya furta so daga baya karya ce kawai, to bari na gaya maka ko ka soni ko ka qini Aslam ni bana sonka bana sonka bana sonka , ka fita a hanyata Kamal nakeso domin shine ya soni ya tallafi rayuwata tun bansan kaina, dan Allah na roqeka Aslam karka kara shiga sabgata, domin na zama mallakin wani , nan da yan kwana ki zan zama mallakin farin cikin zuciyata kamaluddeen")

A fili ya furta "mallakin wani nan da yan kwaniki , ina! wlh baki isa ki zama mallakin wani ba matuƙar ina numfashi, kamal wlh ka rabu da matata kokuma na maka mugun lahani wlh, baka isa ka shiga gonata ba, zanyi maganin kane kamal, ni za,a yaudaya ni za,a munafunta"
Haka yayi ta sambatu kamar wani taɓaɓɓe,
Karshe dai wata zuciyar ta bashi shawara daya tashi yayi alwala yakai kukan shi gurin mahalicin shi,

Haka ko yayi ya miƙe ya dauro alwala yazo yayi nafilfili, yana idarwa ya shiga miqa kukan shi gurin mai duka, baiyi aune ba sai ji yayi ana kiran sallan assalatu,
Chapter 31 · 0% Book details