← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 126

Sashe 122

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Asmah taga gata iya gata a wajen yan uwa da abokan arziki ko ta ina tururuwan zuwa mata barka akeyi harda ma wa'inda ba dangin iya ba na baba irin su AyshaNalado😁 kula kuwa ta kawane bangare samun shi take yi baga mummy da daddy baga Mami da Abba ba kai har su Alhaji baba ba'a bari a baya ba, Ummi kam tun kwana uku da haihuwa ta iso kuma a part mummy ta sauka wannan karon dan karma tayi nisa da yaran, kafin ranar suna ya zagayo ta murmure tayi wani irin fresh ta dawo yar cakwai cakwai da ita asalin Asma'un ta babu wanda zai ce itace ta haifi y'ay'a har uku a cikin ta, zee da Aslam kam kullum sai mummy ta koresu suke tafiya dan in suka zo tun safe sai sukai sha daya a gidan hatta little ba'a barshi a baya ba son yaran yake kamar kamar me da an dauke su zaice a bashi kannen shi idan anki ya saka rigima wata ran sai mummy ta make shi dake ita fire fire ce bata daukar fitsara, sai da daddy yaga abin yayi yawa ya taka ma Aslam birki shine suke wucewa tara, ana gobe suna zahra ta iso ita ma da babyn ta dake gudu ko ina, tana daukan yaran tace "um lallai yara kunzo inda ake neman ku, Asmah da y'ay'an kanta wai aiko zaku sha kula aradu." Ranar suna tun da farar safiya gida ya fara daukar harama. Kowa a k'age yake da yaji sunan da Aslam ya saka wa y'ay'an shi dan an kad'a an raya yaki fad'a duk wanda ya tambaye shi cewa yake sai ranar suna, dan rashin ta ido har Alhaji baba daya tambaye kin fad'a mai yayi. Hatta Asmah bata sani ba daga shi sai zee suka san sunan yaran, aiko abin ya matukar kayatar lokacin da liman ya baiyana sunan yaran, mummy ce da Mami da kuma Ummi, aiko abin yama su mummy dad'i kamar me Aslam yasha ruwan albarka ranar kamar ba gobe. Haka akaci suna aka sid'e abin sai wanda ya gani, suna na gani na fad'a akayi abinci da abin sha enough anyi taron da a tarihin gidan ba'a taba yin taron daya kai wannan cika ba, dan yan dama ta biyu fans ma kawai mun ishi gayya, mu kusan dari hud'u muka zo kuma duk saida mukaci mukayi hani'an mani'an harda masu guzirin na dumame😅. Asmah da yara sun samu kaya bana wasa ba dan saida aka cika store biyu manya manya da kaya bana yaran ba bana uwar yaran ba, kudi kuma cash ta samu yafi miliyan biyar daga abokan Aslam na kusa dana nesa, banda masu transfer wannan kuma Allah kadai yasan adadin su, masha Allah yara kam sunyi goshi harda keya😂 .

Second 2 d last page💃💃💃💃💃💃 luwaiiii

Oum Ummeetarh
07041130088

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}

Paga 133

🔚🔚🔚🔚💃
Chapter 122 · 0% Book details