← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 126

Sashe 36

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daddare bayan ya idar da sallan isha'i yayi wanka ya fesa adon shi kamar yadda ya saba idan zaije tsonaka nan fada, daukar key din motar shi yayi ya fice daga gidan su zuwa gidan alhaji baba,

Daidai wannan lokacin batool na hango zaune a gaban alhaji baba, kallonta yayi yace"batula abinda yasa na kira ki dama naga har yanzu baki gabatar da naki manemin ba kuma gashi naga yau har saura sati hudu biki, ina fatan baki manta da magana na ba na cewa duk wacce bata fitar da miji ba zuwa lokacin dana baku ni zan zabar mata miji da kaina".

Gaban batool ne yayi wani irin faduwa nan take ta shiga haɗa zufa, ita dai a halin yanzu bata da Wanda zata gabatar a matsayin mijin da zata aura , don ko saurayi bata dashi, ita yanzu babban damuwar ta batasan Wanda alhaji baba zai zabar mata a mastayin miji ba , kilama daya daga cikin almajiran wannan abokin nashine alhaji Mallam.

Wani zuciyar ne ta ce mata ya bashir fa, take kuma wata zuciyar tace Allah ya kiyaye ki da auren wannan dan banzan mutumin, wata zuciyar kuma tace, to aiko gara ya bashir d'in akan almajiran alhaji Mallam dan ko ba komai shi dan gayu ne kuma kyakkyawan gaske, wata zuciyar kuma tace kina hauka ne batool idan ke kina iya auren shi to shiya gaya miki yana sonki ne,haka tata saƙe saƙe ta saka wancen ta kwance wancen.

Alhaji baba ganin shirunta yayi yawa yasa yayi gyran murya tare da cewa "ke nake saurare fa batula,".

Dagowa tayi ta kalle shi bayan ta hadiye wani busashen miyau tace"ni bani da wani zabin kaina a halin yanzu, dama dai za'a kara mini lokaci ne zuwa gaba kadan" alhaji baba "yace babu wani lokacin da za'a kara miki nasan kinsan halina sarai bana magana BIYU, yanzu tambayan da zan miki ki bani amsa tsakanin ki da Allah idan kika boye wani Abu kin cuci kanki, menene tsakanin ki ba Dr bashir?" .

Sautin bugun zuciyarta ne ya kara karfi jin an ambaci sunan shi, itako menene tsakanin ta da Dr bashir banda rashin mutunci, ita ko'a fuska bai taba nuna mata alamar yana sonta ba,amma tanaji a zuciyarta da ya furta ba shakka zata iya auren shi, don tana jinshi sosai a ranta,

Cikin kasalalliyar murya tace"babu komai a tsakanin mu , daya danganci soyyaya" murmushi alhaji baba yayi yace "to masha Allah , tashi kije daga nan zuwa ko wani lokaci zaki iya tsinkayar kirana"

Dr bash kam yana isowa part d'in mummy ya fara nufa da nufin ya ganta kafin yaje amsa kiran Alhaji baba, shiga yayi main parlour ba kowa sai katon TV dake kunne yanata aiki , neman guri yayi ya zauna, ko wani daga cikin su zai sakko.

Cikin harde hanya ta fito daga part d'in alhaji baba, innalillahi wainnailaihi rajiun me tayi kenan me hakan ke nufi hakan na nufin za'ayi sarakar ta kenan, ga almajiran alhaji Mallam , tabdijam Ashe akwai kallon rashin M a gidan nan don wlh baza ta yarda ayi sarakarta ba saikace wata kosai,

A haka ta shiga parlourn hankalin ta duk a tashe, jin motsin kofa yasa. Dr bash dake zaune a falon sauri dagowa ya kalli bakin kofar, aikuwa caraf idanun shi ya sauka akanta, wani dadi ne ya lullubeshi shi , take ya saki wani kayataccen murmushi , saidai kwata kwata ita bata ganshi ba, ganin haka yasa , tana zuwa daidai shi zata giftashi ya saka mata kafa.

Tuntube tayi da kafar shi hakan yasa tayi baya zata faɗi, harta rintse idonta don ta sadaƙar ta fadi ta gama, saidai jinta a jikin mutum yasaka ta saurin bude idanun ta, irin rikon nan ya mata kamar suna rawan indiya , karaf idanuwansu ya sarke Dana juna , kallon kuda suka shiga yiwa juna na some seconds.

Hannayenta ta mika ta tunkude shi , ba shiri ya saketa, balla mai harara tayi ta buga tsaki, ita yau bata jin yin surutu don tana da tunanin yi a gabanta, raba shi tayi ta wuce shi, cikin salon takunta na yanga juyawa yayi yana kallonta har ta kama kafar bene zata haye, ta tsinci muryar shi yana cewa" mutum mummuna sai shegen yanga haka, ke ba kyauba amma iyayinki yafi karfin ki, tsabar muni ko saurayi baki dashi duk yan uwanki ankai kudin aurensu banda ke, kibani dama kawai na taimake ki na rufa miki asiri na lallaɓa nace ma su daddy kince kina sona, nayi maneji dake don barinki haka a gida a aurad da yan uwanki, zaki zama abin tausayi ne,".

Wani irin juyowa tayi tana kankance idanu cike da masifa, lip dinta har rawa yakeyi , tsabagen an tabo ta ,tace"Allah ubangiji ka tsare ni,"tuf ta tofar da yawu gefe, kafi ta tako gabanshi cikin wani irin cat walk, dan nisa dashi kadan ta tsaya ta kalle shi a yatsine ta daga yastanta tana nuna kanta daga sama har kasa tace " kalleni frm up to down , wlh nafi karfin ayi maneji dani, kuma da kake batun kyau nasan ko gasar kyau aka saka tsakanin mu kafin mutum dari su jefe maka kuri'a mutum billion sun jefamin, aure ne dai bazan aure ka ba, baka daga cikin tsarin irin mazajen da suke burgeni ka gane ai" ta karashe tare da daga mai gira da murza hannunta ya bada sauti Tass.

Tunda ta fara magana yake binta da wani irin kallon kauna, dan bakinta yake bi da kallon sha'awa ji yake yi kamar ya kamo ta ya shiga kissing dinta madly, har mafarki yakanyi jefi jefi gashinan yana tsotsan bakin ta.

Saida ta juya zata bar wajen ya dawo daga duniyar begen lips dinta, wani irin taku ta shigayi da gayya Wanda yafi na d'azu daukar hankalin shi, daga murya yayi yace"karfa kiyi tunanin sonki nakeyi taimakon ki zanyi kar azo ana kwatance dake a anguwa , wannan wadda tai kwantai dinnan to tunda kuma bakya so kin hutashsheni" ko juyowa batayi ba balle ta tanka shi ,saida ta kule wa ganin shi , sannan ya sauke ajiyar zuciya, wani kyakkyawan murmushi ne ya kufce mai tunawa da gadar zaran da yake shirin daura mata tabi takai, na turo iyayen shi yace injita,kwafa yayi yace yarinya zakiyi bayanine Allah dai yakai damo ga harawa.

Juyawa yayi ya fice daga part d'in zuwa na alhaji baba, yana nan a inda ya gama magana da batool bai kai ga tashi ba, bayan sun gaisa harda dan taba wasa na kaka da jika, alhaji baba ya kalle shi yace "abinda yasa na kiraka bashir tambayar ka nake so nayi tsakanin ka da Allah ka gayamin gaskiya, menene tsakanin ka da batula".

Wani irin farin ciki ne ya lullubeshi , hamdala ya shiga jerowa a zuciyar shi kafin yace" alhaji soyyaya muke yi, inason ta tana sona, amma taƙi bani dama na turo magabatana , nayi nayi taki amince min , wai ita bata da ra'ayin a hada bikinta dana kowa tafi son ayi bikinta ita kadai, wai na bari sai angama bikin yan uwanta saina fito, to dama nima gobe nake son na samu su Abba da zance".

Alhaji baba yace"kai madallah Abu yayi kyau tashi kaje Allah yama albarka gobe kacema alhaji usman ina son ganin shi".

Godiya bashir ya shiga zubawa kamar bakin shi zai tsinke, saida alhaji baba yace ya isa haka...............

💖more comment more typing💖

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabilillah🙏

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Page 71 & 27

Washe gari kuwa iyayen Dr suka zo ba bata lokaci akayi abinda za'ayi, a take suka bada kudin komai da ya kamata su bayar na àl'ada, iya mazan gidan ne kawai suka san da maganar don hatta mummy da mami basu Sani, balle kuma su Asmah.

Ummi mahaifiyar Amir da ke zaune a abuja yau ta sauka kasancewar da ita za'aje dubai domin siyayyan kayan amare, ita da mummy zasuje, don mummy cewa tayi ita da kanta zata je ta zabar a yan matàn ta kayan daki domin tafi kowa sanin abinda kowaccen su take so,da kuma kalan da take so.

Yan matan Mummy ba karamin murna sukayi da zuwan Umminsu ba, kamkameta sukayi suna murna da tsalle kamar wasu yan three - three years, Amira kan baya taja tana murmushi da sunsusne kai, ita ala dole tana jin kunyan ummi, matsayin ta na mahaifiyar Amir.

Dagowa ummi tayi ta kalli Amira cikin zaro ido da mamaki tace , "me zan gani haka yau ni Aminatu, Amira yau ni kuma kike jin kunya, oya oya zokima umminku oyoyoo" ta fada tana jawo amira ta rungume ta , "wani Amir d'in wofi zai shiga tsakanina da daughter na, karna sake ganin haka ki sa a ranki ke na haifa ba Amir kinji" gyada kai Amira tayi tana murmushi.

Haka suka wuni tare tana ta jansu da hira , tsaraban kayan kyaran data fara zuwa musu dashi ta babbasu wadan da zasu fara amfani dashi tun yanzu,irin su sabulu wanka da turaren wanka dana jiki , Dana wanke kai da dai sauran su, don tace maganar gyaran amare na hannunta ita zata musu komai na gyara , aiko karkuso kuga murna, wurin amaren.

Kwanan ta biyu da zuwa jirgin su ya daga zuwa Dubai ita da mummy,

Alaka zakanin M,M da Asmah sai kara karfi takeyi, kullum cikin charting suke, koda wasa Aslam bai taba tauko mata zancen abinda ya shafi aure ko saurayi ba , don yana tsoran jin abinda zai iya saka zuciyar shi bugawa.

Yau dai suna ciki charting Asmah tace, "friend wai ko na tambayeki ki mana " yace " ina jinki Allah yasa na sani" tace"kina aure ne?" yace "A'a kawa me kika gani" tace "ba komai nadai tambaya ne, niko kinga biki na saura sati uku yau insha Allah".

Wannan magana ba karamin sharking ya saka zuciyar Aslam ba, shi yama manta da batun cewa zatayi aure tunda ya samu yana charting da ita 24 hour yasa yake jinshi cikin nishadin da yasa ya manta abin da ke gaban,
Chapter 36 · 0% Book details