Sashe 119
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan wata daya da rasuwan Dad, zaman lafiya tsakanin Asmah da zee sai abin da ya ƙaru, zuwa lokacin zee ta koma asalin zee ɗin ta, tayi laushi ta kara miƙa wuya ga lamarin ubangiji, ta dau hakuri da dangana akan rashin mahaifin ta, idan ta tuna shi sai dai kawai ta mishi addu'a, Aslam ma ya dena yi mata wasu abubuwan da yake mata zuwa yanzu dan ba karamin tausayi take bashi ba , musamman idan ya tuna da wasiyyan da mahaifin ta ya bashi da kuma amanar ta daya damƙa a hannnun shi a lakacin yana kan gargarar barin duniya. A bangaren Asmah yau ta wayi gari cikin wani irin yanayi mara daɗi tun cikin dare ta ke jin cikin ta na wani motsi kamar akwai abu mai rai a ciki,dama takanji haka lokaci lokaci cikin kwanakin nan tana sharewa amma na yau sai yayi yawa gashi Aslam ba'a dakin ta yake ba, tun cikin daren tayi ta kiran wayar shi amma yaki shiga, haka ta zauna ta dafe cikin ta tana ta kuka, idan taji motsin yayi yawa sai ta shiga karanta ayatulkursiyu ta tofa, ta firgita ainun da lamarin kafin safiya duk ta fice daga hayyacin ta, kwanaki da cikin ta keta kumbura taje asibiti taga likita, Dr Aysha ta mata duk wani tambayoyi akan alamomin ciki tace bata jin ko daya, kuma duk watan duniya al'ada takeyi, duk wani test daya kamata tayi, tayi harda su scanning babu komai, kwantar mata da hankali Dr tayi tace ba komai kawai tumbi bi ne, ta kiyaye cin abubuwa masu maiko da kitse kuma ta ringa motsa jiki zai baje insha Allah, koda taji haka sai ta tattara lamarin ta watsar kawai tunda dai ita ba ciwo yake mata ba, kuma ma ba wani shegen girma yayi ba itace kawai take ganin abinta sai ko Aslam shi da yake mijin ta , amma idan ba mutum kallon kurulla ya mata ba bazai ga komai ba, shine kuma cikin wannan week ɗin ta farajin motsi motsi a cikin nata, tana dai daurewa tana basarwa don ko Aslam bata fadawa ba, sai dai tayi ta addu'a tana rokon Allah koma menene ya yaye mata, har aka kira sallan assalatu idanun ta biyu bata rintsa ba, da'ker ta lallaɓa tayi sallah, tana idarwa ta farajin kamar ana yaki a cikin har in ta taba tanajin motsin a hannun ta, wayar ta ta dauka ta sake gwada kiran Aslam still bai shiga ganin haka yasa ta juya akalar kiran ta zuwa numbar mummy dama abin da ya hana kiran ta tun jiya dare ne dan karta ɗaga mata hankali, mummy nakan dardumu da asuba tana lazumi taji wayar ta na ringing kamar ta share haka kawai taji zuciyar ta na azalzalan ta akan ko baza ta dauka ba ta duba, ganin sunan Asmah na yawo a saman screen din wayar yasa taji gaban ta ya fadi, a fili ta furta "Asma'u da wannan farar safiyar Allah dai yasa lafiya." Ɗaga kiran tayi ta kara a kunne tare da yin sallama, cikin shehsheka taji muryar Asmah na amsa mata sallama, cikin dan tashin hankali jin Asmah kamar kuka taje tace "subhanallahi! Asma'u mekefaruwa, meya sameki waya taɓa ki?" Dan ita duk a tunanin ta cikin Aslam da zee ne wani ya saka ta kuka a Cikin kuka take ba Mummy labarin abin da ta kwana ji a cikin ta yau, mummy karan kanta abin yadan tsorata ta, wani tunanin ya faɗo mata a rai da sauri ta kauda shi tare da yin istigfari a zuciya, cikin sanyin jiki tace "Ina Aslam ɗin yake to?" Tace "yana ɗakin anty zee yau a can yake kuma tun cikin dare nake ta ta kiran shi wayar shi yaki shiga." Katse kiran mummy tayi tare da cewa "Ina zuwa." Lambar Aslam ta shiga kira itama cikin rashin sa'a yaki shiga, ganin zai bata mata lokaci yasa ta shiga shirya wa dan tafiya gidan Aslam taje taga halin da marainiyar Allah take ciki. A waya ta sanar ma daddy abin dake faruwa shi kanshi lamarin ya daure mishi kai, baiyi kasa a gwuiwa ba yace ta shirya ya kaita, minti 30 ya dauke su zuwa gidan Aslam, har zuwa lokacin Aslam na part ɗin zee dan koda ya dawo masallaci can ya koma da nufin yayi shiri ya sallame ta gaba ɗaya sai ya koma part ɗin Asmah, horn din motar su mummy da kuma ƙaran bude get da mai gadi yayi shiya janyo hankalin shi, yana tsaye gaban mirror yana shirwaya zee na gefen shi tana taimaka mai, kallon juna suka yi da mamaki fal fuskokin su, waye da wannan sanyin safiyar a gidan su, kasa hakuri yayi ya karasa bakin windo ya daga labule ya leka zaro idanu yayi lakacin da yayi arba da motar Daddy kafin ya gama mamaki yaga Mummy ta fito ta nufi part din Asmah, da sauri ya saki labuleb ya juyo ya kalli zee data ke nan tsaye tana jiran taji su waye, yace cikin dan tashin hankali "Daddy da Mummy ne fa." Cikin kaɗuwa tace " A gidan nan da sassafe? To duk yadda akayi ba lafiya." Bai tsaya jin me zata ce ba ya zira jallabiya ya fice da sauri ganin haka yasa ta rufa mishi baya. A can kuryan ɗaki Mummy ta same ta durkushe tana hawaye da sauri ta karasa ta dago ta, ganin mummy yasa ta fashe da kuka, rarrashinta Mummy ta shiga yi "yi shiru Asma'u ya isa haka, yanzu zamuje asibiti insha Allah koma mai ke ciki zasuyi scanning mu gani, asibitin Dr nasidi zamuje babban likitan mata me kuma yana da wankin ido imma jinnu ne ko sihiri zai gane." Kasancewar sanye take da hijabin da tayi sallah yasa mummy kamo hannun ta kawai suka nufi kofar fita, daidai nan Aslam ya iso da sauri zee na biye da shi, ɗaga ido mummy tayi ta musu kallo daya sai taji wani haushin su ya tirnike ta suna can suna soyayya sun bar mata yarinya ita kadai zata mutu a banza ita fa shi yasa auren mai mata bai taba birgeta ba, sama sama ta amsa gaisuwar su, ta wuce su rike da hannun Asmah dole suka matsa mata a hanya, ganin yadda ran ta ke a bace, daddy na hango su ya fito ya bude musu gidan baya, zaunar da ita tayi tare da rufe mata kofar ta zagaya ta shiga mazaunin ta nada suka dauki hanyar asibitin Dr nasidi dake kwangila, suna fita Aslam na fitowa, hankalin shi gaba daya ya tashi dafe kai yayi ya shiga karanto innalillahi wainnailaihi rajiun, ganin haka yasa zee nufar dakin ta da gudu ta dauko makullin mota bata tsaya mai bayani ba ta shiga ta tayar ganin haka yasa shima yayi sauri ya fada ta bi bayan su mummy cikin sa'a ta cim musu saboda traffic light daya tsayar da su, koda suka iso asibitin sun taradda da layi duk da likita bai karaso ba sai Karfe takwas, duk wani zirga zirgan da za'ayi na bude file da sauran su Aslam ne yayi, so yake ya tambayi meke damun Asmah amma yana Shakkar mummy ganin yadda fuskar ta ke daure, kasa jurewa yayi ya nufi ta inda yasan zai iya sanin sauki, wurin daddy, a nan yake jin mekefaruwa, aiko dai hankalin shi ba karamin ta shiga yi ba haryaso yafi Asma'un shiga rudu, takwas daidai Dr nasidi ya iso, mutane da yawa ke gabansu amma kasancewar akwai sanayya a tsananin su, ɗan wani tsohon abokin daddy ne yasa aka musu wuru wuru wanda ba'a rabuwa dashi a Nigeria suka shiga, yana gama jin bayanin ta daga bakin Mummy kallo daya ya mata yasan lamarin ta akwai saka hannun mutanen ta a ciki, amma bai gaya musu haka ba, scanning ya fara mata take ciki ya bayyana yaya uku rerass da ransu da lafiyan su yan wata shida har an gama halittan su, bai basu bayanin komai ba saida ya gama daidai ta komai, duk wani abin da ya kamata ya mata yayi, ya bata duk wani taimako da ya dace sai da ya tabbatar yanzu komai normal, sannan ya nemi ganin mijin ta a office din shi, jiki a sanyaye Aslam ya tafi don tunda daddy ya gaya mai mekefaruwa jikin shi yayi sanyi, musabaha sukayi da Dr nasidi shima matashi ne dan akalla zasuzo tsara da Aslam din, dan da alama ma sunsan juna, bayan Dr ya nuna mai wurin zama ya zauna, farin takarda ya mika mishi tare da cewa " Da farko dai zan fara da cewa Congratulation Mr Aslam." Ya fada yana sakin kayataccen murmushi, kamar wani gaula haka ya tsaya yana kallon shi, zaka rantse baijin yaren da Dr nasidi keyi ne,ganin bai amsa faifan ba yasa Dr sake cewa "karbi mana dan uwa." Kamar mara jini a jiki haka ya miƙa jhannu shi nya karɓa,koda ya karba bai iya budewa ba sai rike wa yayi gam kamar wanda aka ba tikikin shiga Aljannah, Dr ganin bai bude ba yasa yace ka "Bude mana." Ba musu kuwa ya warware faifan ya fara binshi da idanu, wani irin yam yam yam haka ya ringa ji yana ratsa tsakanin kanshi da zuciyar shi, tabbas ba barci yake yi ba idanun shi biyu amma kuma abinda yake gani a rubuce jikin faifan ne yasa yake gani kamar mafarki yake, bayani ne akan cikin Asmah watannin Cikin da matsalar Cikin da kuma saka hannun Dr akan tabbatar da cewa yayi duk abin da ya dace yanzu komai nomal abu daya ne babu adadin babies din wannan kuma ya bar musu su jira ranar haihuwa, yana gama karanrawa dago kai yayi yace "Dr a mafarki muke ko a ido biyu?" Dariya Dr ya kwashe dashi, indai irin wadan nan bankauran ne ya saba gamo da su iri iri amma nayau na Aslam ya bashi dariya sosai, cikin zolaya yace "ko nadan mare ka ne sai ka tabbatar" ga mamakin shi saiji yayi Aslam yace "eh Dr pls ka mareni kozan dawo cikin duniya ta." Sai kuma hawayen farin ciki shaaa wanda shi karan kanshi Aslam din baisan wanda suka zubo ba, can kuma ya mike ya kaima Dr nasidi runguma,yana zuba mishi godiya, shikam