← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 126

Sashe 88

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace "ya Aslam suna, gidan suna, yau sunan ya Rabi'ah, innalillahi gashi barci ya kwashe ni har sha biyu rana tayi" sai lokacin hankalin Aslam ya kwanta take ya saki wani ajiyar zuciya, jin Ashe ma akan zuwa gidan suna take wani firgita, sake yunkurwa tayi zata mike, ya sake rikota tare da cewa "wai kina nufin gidan sunan zakije, baki da lafiya fa" tace "ya Aslam idan banjeba zasu iya yin tunanin wani Abu" yace "idan kikajema sai sun fi gane wani Abu" dagowa atayi ta kalle shi tare da cewa "kamar yaya" yace"idan bakije ba kika ce musu bakiji dadi ba,baza su gane komai ba saidai suyi tunanin ciwon kai ne ya hanaki zuwa , amma kika kuskura kikaje kowa sai ya gane abinda kika aikata jiya" zaro ido tayi tare da cewa "to yanzu ya zamuyi" yace "kawai mu kira waya ki gayawa ummi" tace "anya kana ganin ummi baza ta gane ba kuwa,"yace "baza ta gane ba kawai bari mu kirata" ya karashe maganar yana mika hannu ya dauki wayoyinsu da ya sakasu a silent tun Daren jiya.

Daidai time din kuma missed call din ummi na bakwai na shigowa wayar shi, duk da shiyace a kira ummi saida gabanshi ya fadi ganin kiranta rututu, dagawa yayi tare da saka wa a speaker ya mikawa Asmah.

Muryan ummi suka tsinkaya tana cewa "Asma'u ina kuka shige ne kuka bar waya anata kira tun dazu,lafiya kuwa meke faruwa wlh hankali na ya tashi sosai, nakira Aslam shiru kema na kiraki shiru,yanzu nake cewa bari na biyo sahu" take bakin Asmah ya fara karkarwa bata iya karya ba a rayuwarta take abinda sukayi shirya da Aslam zata fada ya bace mata bat, ummi jin shiru ta kare" Asmah lafiya kimin magana mana, meke faruwa innalillahi wainnailaihi rajiun" jin yadda hankalin ummi yayi mugun tashi yasa tace tana zaro idanu "ummi ciwo ne" ummi hankalin tashe tace "what! ciwo subhanallahi waya ji ciwo" Asmah mai makon taba ta amsa sai kawai ta mika wa Aslam waya, da yayi tsuru tsuru shima, yana amsa ummi nacewa "kimin bayani Asmah wayaji ciwo cikin ku" shima ji yayi gaba daya ya ruɗe maimakon ya nustu ya bada amsa sai cewa yayi"hello ummi ina kwana" jin muryar Aslam yasa ummi dake firgice don ita kwata kwata hankalinta bai kawo kan kashe boss akayi ba, hankalinta tafiya yayi kan cewa ko sun fito zasu zo ne sukayi accident sukaji ciwo shiyasa duk ta rude, tace a rude"son, son dan Allah ka gaya min mekefaruwa hankalinta ya tashi" cikin rudewa ya samu kanshi da bata amsar da Asmah ta bata yace"ummi ciwo ne" daura hannu ummi tayi aka tare da cewa "innalillahi wainnailaihi rajiun gani nan zuwa gidan yanzu" kit ta kashe wayarta............

Oum Ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabilillah🙏

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}

Naceba🙋‍♀️
Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi😍
Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi🙏 kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama😍sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani😍

Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195
Call:08064532391
Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida🤝
💯 tested nd trusted
Natural/organic🥰

Page 115

Tsayawa Aslam yayi yana bin wayar dake hannun shi da kallo kamar ranar ya fara ganin waya a duniya, yayinda Asmah ta daura hannu aka, a ruɗe tace"mun shiga uku ya Aslam ga ummi nan zuwa, yanzu ya zamuyi"sai sannan ya dauke kanshi daga kallon wayar ya mayar kanta jiki a sanyaye, ya amsa da "nima bansan yadda zamuyi ba husnah" haka suka zauna tsuru tsuru kowannensu jikinshi a sanyaye, can Aslam yace " na samo mana mafita" a kage tace"yawwa ya Aslam, dan Allah ka taimaka karka bari ummi ta gane komai" yace "kawai abinda zamuyi idan tazo ni zan fita falo kekuma saiki kwanta a ɗaki kiyi barcin karya, kawai sai nace mata kinyi barci" shiru tayi bayan ta gama sauraren shi, tunani takeyi anya wannan shawara ta ya Aslam zata bullar dasu kuwa, ganin tayi shiru yasa Aslam cewa"kinyi shiru husnah koke kinada wani mafitar data fi wannan ne ki kawo" tace "ya Asmah ummi ne fa sai kace baka san umminmu" dafe goshi yayi tare da cewa "kash! to yanzu ya zamuyi" karyar da kai gefe tayi, tare da taɓe baki kamar zatayi kuka, idanunta sun cika da hawaye, jayota yayi ya rungume ya shiga rarrashinta yana bubbuga bayanta kamar wata yar goye, ita kuma sai wani narkewa take karayi tana kukan shagwaba.

Ummi na katse kiran bata koma cikin gida ba, direct wajen get ta fito da nufin taje ta samu keke napep, hankali tashe take tafiya tanayi tana gyara zaman mayafin, ko kudin napep din bata dashi daga ita sai wayar hannunta, kallo daya zaka mata kasan hankalinta a tashe yake, kwata kwata bata cikin hayyacinta, tana isowa bakin titi motar Abba hanifa na isowa shima.

Tun daga nesa ya hango wata mata mai kama da ummi, saidai kwata kwata bai taba zaton ummi bane, don duk Wanda yasan ummi farin sani idan ya hango yadda take tafiya daga nisa bazai yarda ita bace, domin ummi yar gayu ce sosai tafiyar ta kuwa a tsanake takeyi, cike da nutsuwa irin na manyan mata da suka amsa sunan su, wasu ma cewa sukeyi tana hadawa da yanga idan tana tafiya.

Saida ya iso daf da ita sannan ya tabbatar itace, itako bata ma kula da shi ba burinta bai wuce ta samu napep din da zaikaita London road ba, da sauri Abban hanifa yayi parking tare da fitowa a motar shi, har ta gota shi, haka ya bita da sauri yana yana kiranta, ummi jin ana kiranta kuma taji muryar Wanda ta sani ne yasa ta waigo, daidai nan kuma ya cimmata.

Ganin Abban hanifa yasa ummi dauke ajiyar zuciya, ko gaisuwar da yake mata bata amsa ba take"yawwa nura nagode Allah ma gaka, muje ka ka kaini London road gidan Aslam" yadda take maganar a rude yasa shima cikin dan rudewa yace "subhanallahi,ummi wani abin ne ya faru" kama hanyar moto tayi tana tafiya ta amsa shi da "inafa lafiya nura, nidai Allah yasa ciwon ma ba mai tsananin bane" ta karashe maganar tana bude motar Abba hanifa ta shiga gidan gaba ta zauna, shima zama yayi a mazaunin driver ya tada motar suka dauki hanya.

Jin horn din mota a bakin get din gidan ne ya dawo da hankalin Asmah da Aslam jikin su, ita dake kwance jikinshi ne ta fara jiyowa zabura tayi ta fizge jikin tana zare ido tare da yarfe hannaye, tana cewa "shikenan ya Aslam ummi ta iso" tsayawa yayi yana kallonta bai gane nufin ta ba, saida yaji mai gadi na bude get sannan ya ankare da abin da take nufi tashi yayi tsaye a rude ya nufi window ya ɗan bude labule kaɗan ya leka, daidai nan motar Abba hanifa na kunno kai cikin compound din gidan, da sauri ya sake labulen ya juyo ya kalleta, yana zare ido, Asmah da kenan tsuru tsuru dama ganin haka yasa ta kara aza hunnu akai.

Kallonta yayi yace kinsan abinda za'ayi yanzu" da sauri ta girgiza kai, yace "kwanta" kamar zatayi kuka tace "yaya Aslam k" bai bari ta karkare ba adan tsawace yace "ki kwanta nace" ba shiri ta kwanta, ya lullubeta da duvet har kirji, yace ta rufe ido tayi barcin karya, tuni jikin Asmah ya fara karkarwa don kwata kwata bata iya Abu na rashin gaskiya ba, balle ma yanzu da take rude.

A kwancen ya barta ya fice daga dakin zuwa falo, ummi ita kadai ta shigo Abban hanifa kuma ya tsaya daga waje, sallama ta rafka a bakin kofar main falon dake kulle ta ciki, Aslam da dama ke tsaye a falo yana jiran karasowarta, ya amsa da sauri tare da nufar kofar ya bude mata, sàwo kai tayi cikin falon tana kare mishi kallo, hakan bai mata ba ta mika hannu ta tattaba fuskar shi, shikam yana nan tsaye gabanta, sai yaƙen dole yake yi.

Ummi dai ganin tabbas Aslam garau yake babu ko gwarzane a jikinsa yasa, ta ayya na a zuciyar ta, to lallai Asmah ne taji ciwo bashi ba, kallon shi tayi suna haa ido ya washe mata baki tare da cewa "sannu da zuwa umminmu." Ya karashe maganar yana kama hannunta zuwa ciki, jiki a sanyaye ummi ta bishi, gurin kujera ya kaita zai zaunar da ita tace, "son ina Asmah, meya same ta a ina taji ciwo." Murmushi yayi yana sosa keya alamar rashin gaskiya ya bayyàna a fuskar shi muraran, cikin inda inda yace "tadan kwanta ne ummi, to ta ɗan samu bacci ne yanzu, dama ba fa wani ciwo bane, kawai kanta ne ke dan ciwo kaɗan kaɗan mà yama yi sauƙi" yadda yake maganar duk kame kame sai wani kasa kasa yake yi da kai yana Sosa ƙeya ummi ta fahimci karya yake yi.

Hankalinta ne ya kara tashi, take zuciyar ta ta raya mata,to ko Abin ya tsananta be yasa yake boye mata kar hankalinta ya tashi, kallon shi tace a tsawace tace "kaiii Aslam bafa wasa nake dakai ba, nace maka ina Asmah take meya sameta" ganin yadda ummi ta hassalomai yasa baisan sanda ya nuna mata hanyar dakin Asmah ba.

Da sauri kuwa ta nufi hanyar daya nuna mata shima ya take mata baya, tana isa ta faɗa kofar dakin da ta gani a gurin, Asmah jin muryar ummi na sallama a dakinta yasa rawan da jikinta akeyi ya karu.
Chapter 88 · 0% Book details