Sashe 54
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk kallon kurillan da take mai yana kallonta ta mirror, yana murmushi, saida ya gama duk abinda zaiyi ya juyo da sauri auko tayi saurin maida idonta ta rufe kamar bata farka ba, dariya ya kwashe dashi a fili ya shiga rera wakar "muna furci dodo maiyi baza yaci riba ba, haka" tana jin shi bata kanta ba, yana gama wake waken shi na habaici yace " ni bana son munafurci kince bakya sona bana burge ki wacece wacece yanzu kuma kinzu kina satar kallon min jiki kinga haɗaɗɗiyar sura me kyau, irin wanda baki taba gani ba ko'a tv, to wannan haɗaɗɗiyar surar na nana faɗima ne, amma tunda an ƙaƙaba min ke zan iya sammiki kafin mai guri yazo mai tabarma ya naɗe" jin kalaman son ranshi da yake faɗa yasa ba ta San sanda ta buɗe ido warass ba ta manta ma baccin karya takeyi, tashi tayi zaune ta rafka wata uwar shewa tana tafa hannaye, kafin ta kwashe da dariyar rainin hankali,cikin dariya tana nuna shi tace"ina haɗaɗɗiyar surar take a nan, dallah mallam ware cen, in ana maganar haɗaɗɗu ka daina saka kanka a cika, jibe ka fa" ta karashe tana kwasar dariyar ta, haushi yaji yace "ni kike cewa ma bani da haɗaɗɗiyar sura to kalli nan kiga" wani irin bubbuɗewa ya fara yi yana baza kwanji yana daga kirji sama da kasa, sannan yayi wata irin tsayuwa na aftoci, take taga ya rikiɗe mata ya koma mata kamar wani barden soja ba Dr ba,dunkule hannun hagun shi yayi ya tara Pawern shi guri daya yana bubbgawa gurin da daya hannun, nan take damatsen hannun shi suka koma kamar na wani dan wrestling, da sauri ta dauke kanta daga kallon shi dan gaba daya wani yamyam take ji a jiki ta, duk yana lura da yanayinta tsaf, taɓe baki tayi tana kawar da kai gefe tace"to na gani kana da naman kirji da hannaye ba shike nan ba" dariya ta bashi wai naman kirji, aiko ya shiga darawa, yace"kwanji ake cewa ba naman kirji ba" tace "oho dai koma menene ni bai wani burge ni, bari kaga na tashi na samawa ciki na abinci" mikewa tayi ta nufi hanyar fita daga dakin yace "ke kazama ina zakije a haka ki dawo kiyi wanka tukun " bata kula shi ba ta wuce kitchen abinta, shima ganin ta wuce yasa ya shiga shirya wa don hatta kayan sawan shi rabi na dakin.
Kitchen ta shiga ta hada lafiyayyar breakfast mai rai da motsi, tuni kamshi ya bade lungu da sako na part d'in, Dr yana gama shiryawa cikin kananan kaya bakin wando da riga red colour, masu mugun kyau da tsadar gaske, ya fito yana baza kamshi yayi kyau kuwa ba kadan ba, tunda ya sako kafarshi waje daddadan kamshin girkinta ya nurnike mai hanci, shaka yayi yana lumshe ido take miyan shi ya tsinke,gsky koma meye wannan take girkawa yayi alkawarin yau sai yaci shi saidai ayi duk bura'uban da za'ayi, falo ya nufa ya zauna yana lallatsa faskeken wayar shi.
Saida ta gama tsab ta kwashe a kula ta jere a dining,sannan ta fito a kitchen din tana miƙa, ganin shi tayi zaune, yana ganin ta yace "sannu da aiki, " harara ta watsa mai tare da cewa "ban sannu ba ina ruwanka da aiki na" ta karashe tana murguda baki, yace "to naji je ki zubo muci yunwa nake ji wlh," tace "yau naji wani sabon salo hammata a diraya, na saba dafa abinci da Kaine dama" yace "to yau dai dani kika dafa dan wlh sai naci" tace "aikodai baza kaci shiba in ciki gara yau saidai ya zube, bari kaga naje nayi wanka nazo naci abincin na oh" ta karashe maganar tana miƙewa zuwa dakin su, don ragon azanci anan tabar kulolin abincin ta wuce.
Tana bada baya ya saki wani murmushin keta a fili yace"yarinya man kaza, in bakiyi sharar masallaci ba kyayi ta kasuwa ai" mikewa yayi tsam ya shiga kitchen ya dauko plate ya nufi dining bude kulan abinci yayi dan kadan kuwa tayi daidai cin mutum daya, murmushi yayi yace "kin ma kanki da kinyi da yawa da saina diba na bar miki, amma wannan ba wani isana ma zaiyi ba balle na rage miki" juye abincin yayi tas a plate din har yana karkade kulan, ya dauki kofi daya ya hada kakkauran tea , ya dauki plate dinshi da kofin shayin shi ya nufi daya extra bedroom din ya bamo kofa...............
Tabɗijam Dr ka taro mach😳
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
DAMA TA BIYU 💖 KƘIRƘIRARREN LABARINE MALLAKINANE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYA MIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZI
NINA BA❌❌❌❌
(In👂👂👂yaji gangar jiki ya tsira👌a kiyaye pls)
{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 93 & 94
Mintuna talatin batool ta dauka kafin ta fito a shirye tsab cikin Riga da skirt na atamfa, ta kashe daurinta ture kaga tsiya, sai baza kamshi yakeyi, cike da takama zatazo tama Dr shegantaka, bata ganshi a falo ba hakan yasa ta nufi dinning taja kujera ta zauna zatayi ɗa'amun, saidai tana jawo kula taji ya biyota ba nauyi, da sauri kuwa ta ƙarƙare buɗe kullan wayam.
Cikin zaro idanu ta furta "kutumelesi" mikewa tsaye tayi ta rike kwankwaso tana girgiza kai, kafin ta taƙarkare tace"basharrrrr" da ƙarfi saida ko'ina na gidan ya amsa , zuwa lokacin kam Dr ya gama tanɗe abincin tas ya suɗe plate, jin ihun muryarta tana kwaɗa mai kira yasa shi tasowa da plate din a hannu ya buɗo ƙofa yana lasar hannu da jan yaji, ga plate da cup empty a hannun shi, tsayawa yayi a gabanta yace "lafiya naji kina ta kwala min kira kamar naci miki bashi"yanayi yana suɗar yatsu tsut tsut.
Takaici kan takaici ina wuta batool ta jefe Dr bash, ba ta san sanda ta karasa gabansa taci kwalar shi ba cikin tsiwa tace"bashar ina abincina"
Ajiye plate d'in hannunshi yayi ya shiga tafa hannaye yace "la'iha'illallahu! yarinya wuyarki ya isa yanka ni kike çima kwala kike kira na da bashar gatse gatse, lallai na fahimçi kina so mu cire raini a tsakanin mu, kinaso aba hammata iska, karki damu nasan meke damuki, zaki samu dont worry" jijjigashi tayi da yake ya sake mata jiki, tace "ni ba wannan na tambayeka ba, nace ina abinci na" buɗe mata baki yayi yana nuna mata cikin bakin shi ma'ana ya lamushe.
Tsabar takaici da bakin ciki sake shi tayi ta zube a gurin ta b
ɓare baki tana risgan kuka, shiko dariya ya hauyi mata yace "kuma yarinya daga yau kika karayin girki ke keɗai a gidan nan muddin inanan to ba rabonki bane, Allah kinji na rantse" sautin kukanta ta kara tanayi tana shushura kafa kamar wata sabuwar ƴar yaye, kai da kaga kukan kasan na zallan shakiyanci ne.
Saida tayi ma'ishi duk yana zaune yana kallonta da taga ba sarki sai Allah, ta tashi tana gungumi tana hararan shi, baiji mai take cewa ba yace"inba tsoro ba ayi da karfi naji mana" bata tanka shi ba ta wuce daki abinta ta kwanta.
Bayan kamar 10 minutes ya shigo idan ta biyu ya wuce ta ya shiga toilet ya rage cikin shi, yana fitowa ta kalle shi kasakasa tace"anci abincin Allah ya isa ba dole ata kashi ba" tayi maganar ne kasa sosai yadda bazai jiba amma cikin ikon Allah karaf a kunnensa, haura wa yayi kan gadon hawa kanta yayi ya zauna ya danne mata kafa, haɗe hannayenta yayi duka biyu ya rikesu gam da hannu daya yadda baza ta iya kwacewa ba, dayan hannunshi kuwa ya mika ya hade leɓenta na sama dana ƙasa ya matse da karfi, azaban zafi taji sai mutsu mustu takeyi ta kasa kwacewa, yace "wannan wannan ɗan bakin naki ya iya rashin kunya manya manya duk randa na samu dama ta biyu a kanshi sai na kusa cinyeshi" batool dai ba baki azaba ya isheta sai hawaye tajeyi, ganin haka yasa ya saketa ya tashi a kanta, aiko ta rushe da kukan gaske ba irin na ɗazu na shakiyanci ba, don ba karya taji zafi sosai,sai Allah ya isa take jero mai amma a zuciya dan kar yaji ya ƙara mata.
Fita yayi ya bar mata dakin ya koma falo yana kallo, ita kuma daga wannan kukan bacci yayi awon gaba da ita, wani American film akeyi mai kyau a mbc 2, saida aka gama ya mike yana kallon agogo, ganin sha biyu harya dan gota yasa ya nufi dakin, bacci yaga tanayi ga layin hawaye nan daya bubbushe mata a fuska, kawai sai yaji ta bashi tausayi, hawa gadan yayi a hankali ya shiga shafa mata fuska yana hura mata iskar bakin shi a fuska, bude idanu tayi akan shi, murmushi ya sakar mata kamin yakai hannu ya rike kunnayenshi yace"sorry batulan bashir, nine na saka ki kuka ko?"jin haka yasa ta kara narkewa idanunta suka ciko da kwalla, cikin shagwaba ta gyada mai kai alamar eh shine, yace "to hi hakuri bazan ƙara ba kinji, ki tashi ki samu wani abu kici ki shirya muje gidan hajiyata ki gaisheta" aiko a ɗokance tace to , dan ta gaji da zaman gida tana bukatar ta fita taga gari, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka koda ta fito bai dakin dan haka ta saki jiki ta shirya tsab abinta ciki dogon rigar lace, ta kashe dauri nan ta fito shar da ita saidai dan kumburin da idanunta yayi saboda kukan da tasha, a falo ta same shi zaune yana jiranta, tana fitowa yace"inyeee kinyi kyau gaskiya zo muyi selfie" murmushi tayi jin yau shida kanshi yace tayi kyau, ba ta gama murmushin ba ta tsinci muryarshi yana cewa ,"saidai ko kaɗan baki kama kafar faɗima na a kyau ba" take murmushin fuskarta ya bace bat, itafa ko wacece faɗiman nan tashi ta mata mugun tsana wlh, ji take da zasu hadu zata iya shaketa har sai ta daina numfashinta.
Haka suka fito suka shiga mota yajasu sai gidan hajiyan shi,(batool a gidan surukai a dawo lafiya,nidai fatana Allah yasa karsu yada hali a can😕)
~AMIR~