← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 126

Sashe 53

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da kallo ta rakashi har ya shige kitchen d'in, sauke ajiyar zuciya tayi, gaskiya yanda taga yana rawan jikin nan sai ya bata tausayi, a ranta ta shiga tunanin anya abun da tayi ya dace kenan, ko ba komai Aslam mijinta ne kuma miji yafi gaban wasa, don yana sonta bai kamata ta ringa mai haka ba, gaskiya ya bata tausayi, ya Aslam d'in da ta sani giant baya wasa baya son raini dan gayu dan kwalisa, wanda da ko kallon ta yayi ada sai taji kamar ta saki fitsari a wando tsabar kamewan shi da rashin daukar wargi shine ya dawo haka a hannunta, hmmmm lallai duniya juyi juyi, take shedaniyar zuciya ta shiga ce mata, wai kina nufin har kin karaya kin fara jin tausayin shi, kin manta abubuwan da ya miki a baya kenan, to wlh karki kuskura kiji tausayin shi yanzu saiya kara gasuwa, Allah ne ya kama miki shi ya kuma baki dama akan shi kema ki rama musgunawan da ya miki a baya, shima yaji a jikin shi.

Da haka shedan yayi tasiri akanta ɗan tausayin shi data faraji nan ya wuce.

Minti arba'in ya kwashe yana faman aikin girka sakwara da miyan taushe, harda farfesu, gas biyu yayi don ya yi sauri ya gama kar ranta ya baci ta fasa ci,lokacin da ya fara daka taji kamar taje ta ce ya barshi kawai , amma ta dake, tana nan zaune ya gama ya jera a dinning, zuwa yayi ya shaida mata ya gama,yana dining, kallon shi tayi, ganin duk ya hada zufa, gashi duk ya wani rarrame, yasa taji ya ba'il baya tausayi, tsintar bakin ta tayi da cewa "sannu da aiki ngd" wani dadi ne ya lullubeshi jin abinda tace,kenan ta yaba tunda gashi har da gdy, ya fahimci tana da raguwar zuciya, ta farajin tausayin shi,murmushi ya sakar mata, a zuciyar shi yace na samu logonki yarinya, saura kiris nayi nasara a kanki , zan jure koma meye, har zuwa sanda zaki shiga hannun, zakiyibayanine, saina birkita miki kwakwalwa ta yanda zakiji inba Aslam ba sai rijiya rijiyar ma mai kwalabe.

Ganin ya tsaya kanta yana kallonta yana sakar mata kyakkyawan murmushin shi, yasa tace "pls ka zubomin zuwa nan bazan iya zuwa dinning dinnan ba" yace "angama babyna" juyawa yayi da niyyar zuwa ya zubo mata, tace "wait Aslam" juyowa yayi yace "na'am sweetie" tace " pls daga yanzu baba sonjin baby, ko sweetie ko husnah or whatever, kawai ka kirani ni Asma'u na yafimin" yace "to shikenan an gama mrs Asmah".

Zuwa yayi ya zubo mata sakwaran katon malmala, ya zuba miya a gefe
ya zubo farfesun a wani plate din dabam, ya dauko ruwa da juice ya hado a tray ya kawo mata.

Ajiye mata yayi ya koma garin zaman shi data nuna mai ɗazu, daukan sakwaran tayi ta kai loma daya baki, so yummy ta fada a zuciyar ta, gaskiya yayi dadi, ware wa tayi taci gaba cin sakwwaranta hankali kwance tana Santi, ji tayi idanun shi sun mata yawa akai har tana neman kware wa, ɗagowa tayi ta kalle shi, shima ganin zata dago kai take ya koma fuskar tausayi, aiko dai ya bata tausayin.

Tace "kai baza kaci sakwaran bane" yace "babu saura ai duka na zubo miki" dage kafaɗa tayi taci gaba da cin abincin ta, can dai ta kasa jurewa, tace "ka wanko hannu kazo muci tare to" cikin zumudi yace "da gaske" tace "eh kobaza kaci bane?" yace "A'a zanci" wanko hannun yayi yazo ya zauna kusa da ita yasa hannu sunaci tare, sai kallonta yake yana murmushi, can kuma dan samun guri ya guziro sakwaran wai zai bata a baki, hararan shi tayi, ba shiri ya maida hannunshi bakin shi, haka suka gama, zai kwashe kwanukan tace ya barshi, ita ta kwashe ta kai kitchen ta shiga wankewa, tana ciki yi ya shigo yace ta barshi, itama tace ya barshi haka suka haɗa hannu suka wanke tanayi yana dauraya, har suka gama, ta share kitchen d'in yayi mopping, haka dai suke aikin kadaran kadahan ba wani fira a tsakanin su, ta daure fuska shi kuma sai murmushi yake mata.

Bayan sun gama tsab ta kama hanyar dakinta zata je ta dan huta binta ya shigayi a baya batare da ta sani ba, saida ta buɗe ƙofa zata shige juyowan da zatayi taga mutum a bayanta, gabanta ne ya faɗi don ya bata tsoro, kallon shi tayi tace "lafiya" cikin alaman rashin gaskiya ya shiga Sosa ƙeya kafin karya da zai mata ya faɗo mai, yace" ji nayi kamar kince nazo muje na miki tausa" harara ta wurga mai kafin ta shige dakinta, ta banko kofa tana Jan karamin tsaki.

Murmushi ya sake wani irin nishadi na musamman yake ji yau, jinshi yake makar an bashi kyuatar ticket ɗin shiga Aljanna, a fili ya furta"tausayin na takeji, tausayi kuma alama ce ta soyyaya, zan biki yadda kikeso,zan miki duk abinda kikeso zan maida kaina ba kowan komai ba a gabanki har sai na wanke kaina da dukkan tarin laifuka na a gareki, zan dasa miki soyyaya ta a zuciyarki, ba tare da kin shirya ma hakan ba, zan sakaki ki soni irin soyayyar da baki taba yima wani mahaluki a duniya ba,nayi miki alkawari" ya karashe maganar yana dunkule hannayenshi alamar maganar daga zuciyar shi take fitowa kai tsaye.

~BATOOL~

Yau kimanin wata daya kenan da auren su, kuma har zuwa wannan lokacin babu jituwa a tsakanin su kullum cikin rigima suke da juna,soyyaya ce zazzafa ke dawainiya da zuciyar ko wannan su, amma sun kasa ganewa balle su tsaya suyi rayuwar aure mai ma'ana, Dr bashi da matsala don shi tun ba yauba ya riga ya gane sonta yakeyi bana wasa ba, matsalar daga gare tane, taki ta gaskata zuciyarta dake azalzalan ta kullum akan lamarin Dr d'in.

Kowa zaman kanshi yakeyi a gidan, kowa shi zai neman ma kanshi abinda zaici, batool girkinta takeyi lafiyayye ta zauna taci a gaban shi, yana haɗiyan yàwu, amma ko siɗi saidai yaje yayi takeaway a waje yazo gida yaci kokuma yaje gidan hajiyan shi yaci, kullum cikin fada suke kamar wasu tom and jerry, duk wannan yanayi da suke ciki basu taba raba makwanci ba, ɗaki ɗaya suke amfani toilet daya komai daya duk da akwai wasu dakuna a gidan amma Dr bai yarda da hakan ba, duk fadan da zasuyi kuwa, ba yadda batool batayi ya bar mata dakin ba ya koma wani amma fir yaqi tayi naci tayi mita harta gaji, saidai insunzo kwanciya ta jera pillows a tsakanin su,ta juya mai baya, gata da birgima ta gama jere jeren pillows d'in karshe wataran a kirgin shi take kwana, shiko da ta birgimo jikinshi ya kara rungume ta susha baccin su,inta farka ta ganta a nan kuwa ta hau bala'i tace shine ya matsota dama dan haka yaki canja ɗaki.

Yau ta kama lahadi babu aiki kuma yaune ya saka rana zai dauke ta suje ta gaida hajiyan shi, don tunda akayi bikin bata fita ba, hajiyan da kanta ne tace karta fara fita yanzu ta bari ta dan kwana biyu sai ya kawota, kannen shi kuwa yammata zuwan su uku, kuma ba laifi tadan saki jiki dasu, dan kwata kwata basu da matsala ƙauna suke nuna mata sosai, anty sama anty ƙasa, duk da sun girmeta a shekaru ƙaramar su ce kawai zasu iya zuwa sa'anni, ashmat da amrah ma sun dawo so d'aya.

Misalin karfi takwas na safiyar ranar lahadi, kwance take a gadon ɗakinsu tayi daddaya abinta , don tunda ta idar da sallah, tayi azkar da addu'o'in ta ta koma ta kwanta bacci mai nauyi ya kwasheta, cikin baccin taji ana yayyafa mata ruwa a fuska , ba shiri ta ware idanunta cike da masifa,dan tasan aikin wanene wannan, wannan Ai wulakanci ne.

Maganar da zatayi ne ta makale hango shi da tayi tsaye gaban mirror daure da tawul a kugu ya juya baya, da alama daga wanka ya fito, lallausar farar fatan jikinshi mai sulbi dauke yake da dotdot naruwan wankan dayayi, mataji ne a hannun shi yana sharce jikaken gashin kanshi da gangan kuma yake yarfa mata ruwan a fuska, don tsokana, yanayi yana kallonta ta mirror ganin ta bude ido yasa yayi sauri dauke kallonshi a kanta.

Duk tsiwar batool idan ta ganshi a cikin irin wannan yanayi ,lukus tajeyi duk kunya ya cikata bata iya kallon shi a haka, gashi shi kuma ɗan duniyan kanshi ne, duk in yayi wanka haka yake fitowa abinshi kullum yazo yayi share shafen shi a gabanta ya shirya a gabanta, itako taita sunne sunnen kai, bata iya dagowa har sai ya fita, yaukam ganin ya juya baya ne baya kallonta yasa ta kurama bayanshi ido bako keftawa tana kisima tsaruwa da haduwar surassa.
Chapter 53 · 0% Book details