← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 126

Sashe 69

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A haka ta gama ciyar dashi, ta mike zata bar gurin komar da ita yayi ya zaunar, sannan ta mike a hankali ya dauki plate da cup din ya isa inda sauran abincin suke a kula, ita dai binshi takeyi da kallon mamaki, mai zaiyi da abinci kuma bayan yace mata ya koshi, mamakin ta bai ƙaru ba saida taga ya ciko plate da cup da kunu da kosai ya zauna gabanta ya dibo yakai bakin ta, kin bude baki tayi ta tsaya kallon shi, katseta yayi da cewa "umhumm ke nake jiya oya haaa" girgiza kai tayi ta bude baki zatayi magana, katseta yayi ta hanyar daura dan yatsar shi akan labban shi yace "shiiii bana son musu kawai kiyi haaa" yadda ya bata rai sai taga ya koma mata asalin ya Aslam data Sani a baya ba wannan Aslam d'in ba dake binta sau da kafa kamar wata uwar shi, bata San sanda ta bude ɗan bakin ba kuwa ya shiga bata a hankali tana karba, gaba dayansu wani irin nishadi suka tsinci kansu a ciki a daidai wannan lokacin, ji suke kamar su tabbata a haka, har saida ya tabbatar ta koshi sannan ya barta, kwashe kwanukan tayi ta kai kitchen ta wanke, sannan ta dawo ta bashi magani yasha,ta wuce kuma toilet ta hada mishi ruwan wanka.

Kamar kullum yauma mika mata hannu yayi ta dagashi, tsayawa tayi tana kallon shi tunawa da dazu daya mike yaje ya dibo mata abinci ai bata dagashi ba kuma taga ya iya tashi da kanshi, muryar shi ta tsinta yana cewa cikin shagwaba "pls mana Mrs Asmah tunanin me kikeyi" jiki a mace ta mika hannu dan ɗaga shi, saidai ji tayi ya fisgota ta fado jikinshi, komawa da baya sukayi kan bed d'in,tana a sama shi kuma yana a kasa ya mutsa fuska yayi yana cewa"wash Allah kirgina kin fado min a kirji zaki karyamin kashin hakarkari, gaki da nauyi, kamar buhun siminti, wash kirjina zai balle" jin abinda yake cewa yasa tayi maza ta sauka akanshi, ta shiga bashi hakuri a rude kan bata San yanda akayi ta fado kanshi ba, dago kai yayi ya kalleta ganin duk yadda ta rude tana ta faman bashi hakuri, yasa ya saki murmushi a zuciyar shi a fili kuma fakan idanta yayi ya mata gwola, saidai cikin ikon Allah karaf a kan idanunta, turuss tayi ta tsaya daga ban hakurin da take mai tana kallonshi ganin haka yasa, ya shiga pretending yana zaro harsher waje yana mayarwa, yana jan yaji, cikin rasa madafa ya shiga cewa "wash harshena yaji, kai gsky yau kosan nan naki yayi yaji sosai wlh hala tarugu guda goma kika zuba"Asmah kam tsabar mamaki daskarewa tayi a tsaye a gurin, kosan da yaci kusan 30minute da suka wuce duk baiji yaji ba sai yanzu, ita dai ganin idanunta ta kamashi yana mata gwalo, sharewa tayi amma a ranta ta sakama lamarin ? mark, na biyu kenan dazu ta kamashi yana tikar dariya yanzu kuma gashi yana mata gwalo, amma ya fake da wani abinda hankali ba bazai dauka ba wai yaji.

Bata dai nuna damuwar komai ba ta tallabo shi zuwa toilet d'in kamar yadda ta saba kullum, rabin jikinshi na cikin nata ta kaishi toilet d'in ta fito, ta Ciro mai kayan da zai saka ta bar dakin zuwa falo,zama tayi ta shiga tunanin abubuwa biyu da suka faru yau a kusan lokaci daya da suka matukar bata mamaki, shin da gaske ne abinda idanu da kunnayenta suka gano da juyo mata, kodai karyace kawai sukeyi yi mata, kai gaskiya da gaskene dan tasandai bata da matsalar ji da gani balle tace ciwon su ne ya motsa mata yau, to kodai mr Aslam ya warke kawai pretending yake mata dan ta dunga kulawa dashi, kai anya ya za'ayi mutum da girman sa da hankalinsa yayi kar yar ciwo haka, ajiyar zuciya ta sauke mai karfi kafin a fili tace koma me ke ciki zan Saka ido sosai domin na gano gaskiyar lamarin, inko karya yake min ko hmmmm ta kareshe tare da girgiza kai.

Aslam koda ya gama wankan shi ya daura tawul gyaran murya ya mata alamar ta shigo ta taimaka mai ya fito, dan dama haka sukeyi yanzu har fitowa toilet d'in sai ta taimaka mai yakeyi, jin shiru alamar bata dakin abin ya matukar bashi mamaki, haka ya mike a hankali ya leko ganin da gaske bata dakin yasa ya fito da kanshi, zaman jiranta yayi tazo ta shafa mashi mai da sauransu amma har ya bushe shiru ba amon ta ba labarin ta, take yasha jinin jikinshi, lallabawa yay, yayi shafe shafen da kanshi ya saka kayan, kamar yabi bayanta ya dubo ko lafiya amma sai wata zuciyar ta kwabe shi da cewa muddin kayi haka sai ta zargi wani Abu, dole ya hakura ya koma ya kwanta amma zuciyar shi gaba daya babu dadi, a haka bacci ya kwashe shi Mara dadi mai cike da mafarkai barkatai, harda Wanda Asmah tagane Ashe kalau yake, ta kuwayi mummunan fushi wai harda su gaggauramai mari tayi a makarkin.

Koda ta gama zaman ta a falo lekashi tayi taga yayi bacci dan haka itama ta wuce dakinta ta kwanta, tana son tayi bacci saidai kash baccin yaki zuwa sai juyi tajeyi akan makeken bed dinta,jin ta tajeyi kamar a bude take dukda taja kakkauaran bargonta ta rufa, ji takeyi gadon ya mata wani irin mugun fad'i, karshe dai saida ta lalubi pillow ta rungume sannan ta iya baccin.

Sai bayan azahar ta tashi bata ɓata lokaci ba ta gabatar da sallanta, sannan ta nufi dakin Aslam, ta tarad shima ya tashi da alama ma ya dade da tashi don har yaje masallaci yayi sallan azahar ya dawo, sannu tamai da jiki, nan ya shiga yamutsa fuska yana amsa mata a wahalce kamar gaske, tambayar shi tayi abinda zaici ya fada, ta wuce kitchen taje ta girki ta kawo ta bashi a baki kamar kullum.

Haka dai suka wuni ranar har zuwa dare inda bayan ta gama bashi abinci ta dauko sauran maganin shi Wanda idan yasha wannan shikenan ya kare ta bare mishi tayi ta bashi, bayan ya gama sha ta kalleshi tace" Mr Aslam idan kasha wannan maganin na yanzu ka gama shanye duka magungunan da Dr ya baka gashi kuma ni banga alamar kaji sauki ba , ya zama dole ka yarda muje asibiti kokuma na sake kiran Dr yazo gida ya kara dubaka, ni abinda yafi bani tsoro ma, wannan rawan sanyin dake tashi maka da daddare kaga rannan baka ma Dr complain dashi ba kar azo kuma ba fever d'in bane wani ciwo ne na dabam"tsayawa yayi ya rasa wani amsa zai bata can dai ya daure yace "to Allah ya kaimu goben sai ki kira Dr James din ya canza min wasu magungunan, tunda dai wadanan basuyi ba", kamar kullum yauma haka rawan sanyin nan ya sake kama Aslam, bata jira yace ta rungume shi ba, tana ganin haka ta shige jikinshi suka Lula barcin su mai dadi cike da kwanaciyar hankali.

~ZEE~

Yau kimanin 3month kenan rabonta da Nigeria, zaune take a garding d'in gidansu ta mike kafafunta tana zaune a kasa ta shimfida dadduma, gaban ta littattafan addinine kanana irin su kawa'idi arba'una hadis durusul arabiya da sauransu, hannunta kuma kur'anine izifi biyar ta bude suratul jinn tana nazari a bayyane.

Daga bayanta taji an mata sallama, da fara'a a fuskarta ta juya ta kalli wacce ke mata sallaman ba wata bace illa malamarta dake zuwa har gida tana koyar da ita karatun addini, a wani babban Islamic school dake garin da suke a Malaysia ta dauki malama macce wacce zata dinga zuwa har gida tana koyar da ita, makaranta taso ta dinga zuwa tana daukan karatau saidai babban malamin ya nuna basa daukar matan aure balle ita gata harda ciki, hakan yasa ta nemi alfarman a bata malama mace wacce zata dinga biyota gida tana koyar da ita in yaso duk wata zata dinga biyanta albashi mai tsoka, babban malamin ya amincene kawai saboda ganin yadda ta nace da gaske tana son karatun, hakan yasa ya duba cikin yan unguwan da suke ya hadata da sumaita, balarabiya da zama ya kawo iyayenta Malaysia.

Zama sumaita tayi suka gaisa cike da mutunta juna , nan zee ta shiga biyo mata karatuttukan da sukayi jiya ba laifi kuwa kanta yana dan ja, kara mata sumaita tayi sukayi sallama ta tafi ita muka zee ta zauna tadanyi nazari na dam wasu mimtoci kafin ta lallaba ta tashi da'ker tukeken cikinta najanta gata ba auki ba,ta hada kayan karatunta a jaka ta linke dadduman ta ta nufo cikin gidan.

Sanda ta shigo falon mom da dad na zaune bata ce musu kala ba bayan sallamar data musu ta wuce dakinta da yanzu ya dawo falon kasa saboda hawa stairs na bata matukar wahala.
Chapter 69 · 0% Book details