← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 126

Sashe 112

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ranar sun raya wannan daren sosai cike da ɗokin juna,sun sha soyayya kamar su kadai je a duniya, lokacin da yaji shi rungume da zee samun kanshi yayi da jin kunyar asmah sai yake ga kamar bai kyauta mata ba duk da ita ta bashi dama, Aslam ya tausaya ma zee sosai ya kuma tabbatar ba ƙaramin kaunar shi take yi ba, take yaji a ranshi bai kyauta mata abin da ya mata, sai dai kuma a wani bangare na zuciyar shi sai mamaki yake yi, lallai ya tabbatar da zancen hausawa da suke cewa mata suna suka tara, sun sha romanace zafafa, wanda shi karan kanshi yasam yayi missing dinsu, domin ba karya zee gwana ce sosai a wajen romance sai dai kuma lamarin ya canza lokacin da ya shige ta, salam yaji kamar gari ba sugar, haka dai ya daure ya bar abin a ranshi ko a fuska bai nuna mata komai ba.

A bangaren Asmah kam ranar bata iya barci ba sai juyi kawai takeyi a makeken gadonta, tana yi tana zirarar da hawaye, zuciyarta na hasaso mata ga ya Aslam ɗinta cen da zee suna soyayya, tayi kuka kamar me har sai da tayi dana sanin tura shi gurin zee ji tayi dama ta kyale shi kawai duk ranar daya ga dama yaje gare ta, haka zuciya tai ta hasaso mata mugayen abubuwa, har da kudirin cewa baza ta sake bari Aslam ya je gurin zee ba idanunta sun rufe kishi kawai ke kwakwular zuciyar ta, cikin ikon Allah kamar daga sama taji wani bangare na zuciyar ta na cewa, me kike yi haka kuma Asma'u? So kike ki kwashe ladar ki a wajen Allah maza kiyi istigfari, samun kanta tayi da cewa astagfirullah a baiyane, kamar kuma an tsungule ta, ta diro daga kan bed din ta fada toilet ta dauro alwala, nafila ta gabatar sannan ta shiga addu'o'i daga karshe ta dauki kur'anin ta ta shiga karan tawa a nan gurin barci ya kwashe ta mai cike da daddadan mafarki wai tana dauke da juna biyu. Da a suban fari ta farka take mafarkin da tayi ya shiga dawo mata dalla dalla, daga hannu tayi sama tace "ya Allah ka tabbatar da wannan mafarkin nawa kasa wata rana ya zama zahiri ba mafarki ba." Sakayau ta farka zafin da zuciyar ta ke mata na kishin zee ya ragu sosai sai ɗan burbushi wanda baza a rasa ba. Bayan ta gabatar da salla wanka tayi ta shiga gyara gidan ta bayan ta gama kuma ta shiga kitchen ta haɗa breakfast bata haɗa da Aslam ba, sanin cewa yana gurin zee iya ita da boy kawai ta haɗa suka ci abinsu suka koshi ta dawo falo ta zauna zaman jiran shigowar Aslam dan wlh kewar shi take kamar ta bishi take ji, tana yi tana kallon agogo har karfe takwas babu shi babu alamar shi, take taji ranta yana so ya ɓaci, cikin taimakon Allah harshen ta ya shiga karanto innalillahi wainnailaihi rajiun, tana nan dai zaune a falo karfe Tara da minti goma dai dai taji an danna doorbell, da rawan jikin ta, tashi ya shiga buɗe ƙofa sai dai abin da ta gani ya kusa tarwatsa zuciyar ta...

Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book ɗin ga duk waccce ta rasa mahaifiya allaha kajiƙan iyayen mu}

Page 129

Aslam da zee ta gani tsaye a bakin ƙofar hannunwan su sarƙe dana juna, fuskar su dauke da wani irin annuri kai da ka musu kallo ɗaya kasan suna cikin madaukakin farin ciki, a tare suka sakar mata murmushi, hakan yasa tayi karfin danne ƙululun daya taso mata ya tokare mata zuciya, ta mayar musu da martanin murmushin da suke mata, idanu ya tsura wa fuskar ta yana karantar yanayin ta, ji yayi babu daɗi a zuciyar shi, take duk wani farin ciki da annashuwar da yake ciki ya fara gushe wa, hanya ta basu suka shigo zama zee tayi a falo shi kuma ya haura upstair, ita ma zama tayi a kujeran dake fuskantar na zee, zee ce ta fara gaishe ta, fuskar ta a sake ta amsa mata suka gaisa cike da mutunta juna, Asmah har da karfin halin tsokanar zee, ita kam zee sai murmushi take mata ba tare da ta tanka mata ba.

Kasa zama yayi koda ya isa ɗakin shi, daga yadda yaga yanayin idanun ta yasan tayi kuka, dama shi yayi mamakin karfin halin ta, yayi mamaki yadda ta nuna ya tafi wurin zee ba tare da wani alamun kishi ko wani damuwa a fuskar ta ba, har sai da yaji abin a ranshi dan a tunanin shi ta daina son shi ne, ko kuma soyayyar shi ya ragu a zuciyar ta, baiwar Allah ashe jira take ya tafi ta yi kuka Allah ka ɗai yasan halin data kasance a daren jiya, gaskiya ya jinjina ma kokarinta, a wannan marran ba ko wace mace bace zata iya aikata abin da ta aika ta sai yar baiwa kamar dai ita, ji yayi so da kaunar ta sun ninku a zuciyar shi sannan ga wani irin matsayin da girma data ƙara a idanun shi, uwa uba kuma wani irin tausayin ta daya lulluɓe shi, Allah Allah yake su kebe ya rarrashe ta ya kwantar mata da hankali.
Chapter 112 · 0% Book details