← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 126

Sashe 17

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miqewa sukayi suka bishi, suna shiga harabar gurin taron Kamal yayi parking suka fito suka shiga cikin hall d'in, wuri saka nema suka zauna , had'ad'd'un samarin dake wajen kuwa sai binsu da kallo sukeyi sunga kyakkyawan yammata, wuri ya tsaru sosai amarya da ango sun zuba kyau, kamar wasu wata da zahra a cikin sararin samaniya, anfara gudanar da komai cikin tsari da wayewa,an kira amarya da qawayenta sun taka, haka ma ango saidai shi angon baiyi rawa ba sabanin amarya da ta tiki rawar ta, kamar ba itace amarya ba, liqi kam anyishi kamar ba gobe su zahra ma sunje summa yayansu liqi amma basuma zee don duk haushinta sukeji,

(tab zee bata samu shiga ba wajen qannen miji😅)

Kamal kam kasawa yayi ya tsare Asmah ganin irin kallon da mazan gurin ke binta da shi, guri ya samu kusa da ita ya zauna yana gadin kayarsa, suna dan fira jefi jefi,

Amir dake zaune a high table kusa da ango a matsayin babban abokin ango,tun shigowar su Asmah hara zuwa sanda sukaje sukayi liqi hankalinshi na Kansu, ganin yawanci mazan wurin hankalin su na Kansu yasa yaji gaba daya hankalinshi bai kwanta. Shawarar da zuciyarshi ta bashi yabi, sakkowa yayi daga kan high table din, ya nufo inda suke, suna ganin shi suka shiga gaishe shi amsa musu ya shiga yi cikin sakin fuska yana dan tsokanansu irinta abokan wasa, kallon Amira yayi yace"am Amira pls zoki tayani shigo da wasu kaya daga mota ," to Amira tace tare da miqewa tabi bayan shi suka fita daga hall din, suna Zuwa gurin motar shi mai makon taga ya bude mota ya dauko mata kayan daya ce,sai gani tayi ya jingina da jikin motar ya tsaya yana kallonta,itama kallon nashi tayi taga meya tsaya yi bai dokko mata kayan ba, suna had'a ido ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi mai dauke da manufofi kala kala, gabanta ne yayi wani irin faduwa,ya salam ta furta a zuciyarta, batun yau ba ya Amir ke burgeta musamman in yana wannan murmushin nashi mai masifar kyau,

Ya Amir kyakkyawan gaske ne gashi da masifar sauqin kai ba kamar ya Aslam mai shegen girman kai da rashin fara'a ba,

Amir ne ya katse mata tunani da cewa "Amiran mami an girma yanzuma shekaran ki nawa " d'ago kai tayi tana kallonshi jin tambayar da ya mata, aiko gani tayi ya qara mata ido sai murmushin shi mai kyau yake saki, kunyarshi taji ya kamata ganin irin kallon da yake mata, fuskarta ta rufe da tafukan hannayenta tana murmushi tace" sha takwas fah'. Amir yace"masha Allah ashe dai yarinyar ta zama ammata, to yaushe zaki turo mana sirikin mu yazo ya gaishemu mu big big brother's". Aiko da sauri ta bude fuskarta tace "laaa ya Amir nifa bani da saurayi" wani boyayyan ajiyar zuciya Amir ya sauke tare da ce mata "da gaske" tace ". Eh " yace "aiko ya kamata kiyi saurayi kin zama ammata yanzu eighteen years fa"

Haka Amir yaci gaba da jan Amira da fira yana bugan cikin ta yana mata wasu tambayoyi da wayau, hakan yafi mai kwanciyar hankali akan ya barta cen wasu qattin banza su dinga kalle mai tanadin shi na shekara da shekaru har a samu wani mai tsaurin ido yazo yamai shigar sauri, wanda yake ganin bazai taba lamuntar hakan ba,

A can cikin hall kam anata ci gaba da gudanar da programs hankali kwance, wayar Amira dake hannun batool yayi qara, kallon su zahra batool tayi tace "kunga Amira daga zuwa dauko kaya shiru shiru tana neman kwashe awa guda, ko lafiya" zahra tace "wlh nima tambayan da zanyi kenan kika rigani, a baki". Wayar ne ya sake ringing batool tace"gashi ma anata kiranta barin kai mata wayar daga nan na duba ko lfy "

Cikin sauri sauri ta miqe riqe da wayar Amira a hannunta, ta nufi qofar fita daga hall hall din, tana d'an gudu gudu sauri sauri dinta samu ta kai mata wayar kar call din ya katse, dai dai qofar fita suka zabga wani uban karan da saida kofin glass d'in daka hannushi cike da ruwan taceccen lemo ya fadi qasa ya tarwatse bayan ruwan lemon ya xubar mishi a jiki, baya tayi taga taga zata fad'i , Allah ya taimaka jinta tayi a jikin mutumin da suka zabga karo ya tarota jikin shi, handset din amira dake hannunta tuni ya fadi qasa, kallon fuskarta Dr bash yayi don yaga da wa yaci karo haka, idanun shi ya sauka ana batool da itama ta dago kai a fusace , fusge jikinta tayi daga nashi, cike da tsiwa da rashin kunya tace"dalla Mallam baka ganine, ko kai makaho ne ko, baka da ido ne ko idonka a tsakiyar ka yake da zakazo ka bangaje ni ka watsamin lemo mai sanyi a jikina, mutane kuna tafiya bakwa kallon gabanku sai kace wasu tumaki, " takwai karshe tare da banka mai wata uwar harara kamar idanunta zasu fad'o qasa,

Zuciya ne ya d'ebi Dr bash ya d'aga hannu zai wanka mata mari sai kuma ya dunqule hannunshi ya naushi iska ya fasa marinta, kallonta yayi cikin bacin rai tare da nunata da yatsa yace ke wacece da zaki bangaje sannan kizo kina gayamin maganar banza maimakon ki bani hakuri, kinsan ko ni wanene, muza hannunshi daya nunta dashi yayi yatsarshi ya bada wani sauti tas tas, yace kinci albarkacin Aslam da mummy da yau saina nuna miki ke qaramar Mara kunya ce tsaki yaja sanan ya ra'bata ya wuce abin shi,

Binshi tayi da harara kafin tana tsaki tare da cewa "aikin banza aikin wofi AI da ka mareni da wlh yau sai kasan ka taba. husaina fatima batool abdallah, "

(Tofah ku kuma kalan naku salon kenan hmmmm ku dai ku biyoni muje zuwa in garin ba nisa)

Daukar wayar amira dake qasa tayi ta duba ba abinda ya samu wayar, fitowa waje tayi dan kaima amira wayar,

Hango amiran tayi ta nufo ta tsayawa tayi har amiran ta isota ,miqa mata wayarta tayi, batace mata qala ba don ranta ya Riga ya gama baci da abinda mutumin da sukayi karo ya mata,

Amsar wayar amira tayi ganin miss call din mummy yasa tabi kiran da sauri, mummy ta daga tace"Amira ina kuka shiga ne inata kiran wayoyinku a kwashe , da'ker ma na samu naki oyaa maza ku kamo hanya ku dawo gida daddynku yace ku dawo haka dare yayi sha daya ta gota,".

Qarasawa sukayi ciki nan ta sanar zasu saqon mummy, aiko babbata lokaci suka miqe da niyyar komawa gida duk da ba'a tashi ba,

Ya kamal d'in da ya kawosu shiya maidasu , a hanyarsu ta komawa gidane batool ke basu labarin karon da tayi da Dr bash tanayi tana kwashe mai albarka tunda ita bawai sanin shi tayi ba, a haka suka iso gida,

A mooris event kuwa sai 1am aka tashi a daga dinner bagan nayi ciye ciye anyi shaye shayen drinks, anyi rabe raben sobeniyas kala kala mutane suka watse , ango ma ya dauki amaryarsa suka wuce gidansu dake London road, bakin dan rakiyan nan da akema amare wai su yan boko😕 sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya

Oum ummeetarh
07041130088

Share
and
Comment
Fi sabillah🙏🏻
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen nu}

Page 43 & 44

Direct gidan su dake London road suka nufa, Aslam nayin parking ya fito ya bude na amaryarsa kofa, fitowa tayi tana lumshe ido alamar bacci takeji sosai, ganin haka ya sa Aslam daukarta cak a haka suka qarasa har cikin katafaren falon su mai kama da aljarnar duniya, don iyayen zee ba qarya sun kashe mata kud'i sosai a gidanta,

A main falo ya ajiyeta kan daya daga cikin manya manyan kujerun dake zagaye da falon, komawa mota yayi ya dauko kunshin ledar daya tanada na kayan ciye ciye , da ake buqatar ko wani ango ya riqe idan zai fara shiga dakin amaryassa, rufe motar yayi ya koma falon , a kwance ya samu zee a inda ya barta ko hannunta bata iya dagawa,saboda tsabar gajiyan da tayi, don ba qaramin rawa ta tiqa ba a gurin dinner nan,

A jiye ledar hannunsa yayi akan center table, zama yayi a kujeran da zee ke kwance, daukan kanta yayi ya daura akan cinyarshi, zame mata goggoron dake kanta yayi, take dogayen kitsonta na attached ya bayyana. dan kurama kitsonnata idanu yayi, a zuciyarshi kuma tunani yake , kardai ace duk gashin zee dayake gani dogo attached ne dama, tirkashi indai haka ne kam akwai matsala, don gashi na d'aya daga cikin abinda yake matuqar so a gurin mace, wani dan tunani ne ya fad'o mai arai , take ya lumshe idanun shi, ba komai yake hangowa sai hotan Asmah dazu a d'akin mummy, natural black hair dinta dogo mai sulbi dake kwance a gadon bayanta yana digar ruwa yake hangowa,

Kamar kuma an tsikare shi yayi fatali da wannan tunanin, ya bude idanun shi akan fuskar zee dake kan cinyarshi, zara zaran eye lashes din data qara yake bida kallo kafin ya sauke idanun shi akan dan qaramin bakinta daya sha jambaki rad'am, makeup d'in da tayi na dinner nanan bajau a fuskarta kamar yanzu aka gama mata shi,

Gsky zee ma kyakkyawa ce tana da kyawun fuska don ba Wanda zai kalleta ya kirata mummuna, saidai dirin jikin ne sai a hankali don irin matan nan ne da ake ma laqabi da muciya da zani, don a miqe take sambal kamar sandan agwai, sai uban tsayi masha Allah, kyawun fuska da hasken fata da tsayi kam akwaisu kamar ita taima kanta,

Iskan bakin shi ya shiga dan hura mata a fuska yanayi yana dan shafa kumatunta a hankali cikin wani irin salon soyyaya,
Chapter 17 · 0% Book details