← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 126

Sashe 43

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Akace rana bata karya, saidai uwar diya taji kunya, tunda sassafe, gida ya dauki harama baki ta gabas ta yamma ta kudu da arewa, kafin karfe tara gida ya cika makil, da jama'a na masaka tsinke,.

Karfe goma daidai babban masallacin juma'an minna ya cika makil da jama'a, idan kaga mutane zaka dauka sallar idi akeyi motoci kuwa tun daga complex har mobile parking ne , yan sanda ke faman kula da gyara fakin motoci, bosso road ranar kasheta akayi saboda cinkoson jama'a indai zakabi hanyar saidai ka zagaya ta bay pass,. Saida duk wani mai muhimmanci ya hallara sarakuna daga garuruwa mabanbanta, haka manyan malamai daga fadin duniya , ga governor da sauran kusoshin gwamnati,.

Haka aka shiga gabatar da daurin aure bi da bi, har saida aka daura na amare biyar rerasss,akan sadaki mafi karanci da albarka, masha Allah angwaye idan ka gansu bakin nan har kunne, karma amir yaji labari sai daukan selfi yakeyi da friend dinsa, Alhamdulillahi aure ya dauru saidai muyi fatan Allah ya bada zaman lafiya,.

Har zuwa wannan lokacin Aslam na kwance a gadon asibiti, amma har nan labari ya iske shi na daurin auren, shidai har zuciyar baya jin zai so wannan zabin na alhaji baba kamar yadda yake son Asman shi amma zai yi iya kokari shi ya danne son da yake ma Asmah tunda yanzu ta zama mallakin wanin shi zaiyi hakuri da koma wacece aka daura mai aure da ita, kawai don dai yama iyayen shi biyayya, zai ta rokon Allah ya saka mishi son ta a zuciyar shi ya kuma cire mishi son Asmah, tunda ba rabon shi bace, yayi imani ya dauki kaddara zaici gaba da jinyar zuciyar shi , har ta warke daga wannan mummunan ciwo da take dauke dashi na son maso wani , amma a zuciyar shi ya kudiri aniyar ana sallamar shi a asibiti zaibar Nigeria dan bazai iya tsayawa yana ji yana gani wani ya angwance da Asmah bashi ba, bazai iya jura ba, ƙasa mai tsarki zai tafi, yaje yata rokon Allah a gaban dakinshi mai tsarki har sai yaji sanyi a zuciyar shi zai dawo 9ja,.

Acan gida kam yinin biki ake yi cikin girma da arziki ko ina manyan mata ne ta ko'ina sai watayawa akeyi, karfe uku daidai jumai mai kidan kwarya ta dasa a tsakar gida, nan kuma aka shiga caskalewa , dama ta biyu fan's kam an samu abinda ake so tunda suka shiga fili kallo ya kama Kansu, nan suka shiga kwangwajewa, jama'a sai yan gulmace gulmace ake yi kasa kasa , su waye wadannan kuma da suka zake haka sunata rawa, basu suka bar tsakiyar fili ba saida jumai ta nade kayanta,.

Duk wannan shagalin da akeyi Asmah nacen kwance kudundune cikin bargo wani zazzafan zazzabi ne ya lullubeta, tun bayan da aka gama daurin aure alhaji Mallam ya kirata ya damka mata sadakin ta a hannu ya mata nasiha mai ratsa jiki, da kuka shabe shabe ta baro falon Alhaji baba tunda ta fada kan gadonta ta kwanta, zazzafan zazzabi ya lullubeta, gashi Neman duniya tama Khadijah a cikin gidan bata ba labarinta , ko mai kama da ita bata gani ba duk Wanda ta tambaya saidai ace mata bari a kira mata ita, saidai tashi shiru a haka har bayan magrib inda motocin daukar amare suka layu a kofar gidan alhaji baba,..............

DAGA YAU INSHA ALLAH DA RANA KO DA YAMMA ZAN DINGA POSTING🙏 dan allah ruwan comment dan mu samu mu karkare da wuri mu shiga sabon buk
(MIJIN NOVEL, zan aura) daga jin sunan kunsan zai nishaɗan tar daku fiye da dama ta biyu kudai kawai ku bani haɗin kai comment dinku kawai nake bukata, ba sai yan dama ta biyu fans kaɗai ba.

NAGODE SOSAI MASU MIN COMMENT HAR KULLUM DAKU KADAI NAKE TAFIYATA😍

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wanna book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Page 81 & 82

Tun daga farkon layin gidan alhaji baba har karshen sa motoci ne laye iya ganin mai hange, wanka amare sukayi mami da kanta ta shirya su shirin barin gida, sai sharar kwalla sukeyi, Asmah kam da yake bata da lafiya wata kanwar mahaifiyar ta da suke uwa daya uba daya , da suka zo biki, ita ta mata wanka ta shirya ta har zuwa lokacin jikin da zafi kau.

Bayan sun idar da sallan magriba, ummi har falon alhaji baba ta musu rakiya, acan suka samu daddy da Abba da sauran yan uwa da abokan arziki, zubewa su kayi a tsakiyar falon kowacce kanta a kasa tana hawaye, alhaji baba ya fara buɗe taro da addu'a, kafin ya daura da nasiha mai ratsa jiki take jikin su ya kara sanyi, bakajin sautin komai a falon bayan amon muryar alhaji baba sai shehsshekan kukan amare, yana gamawa, Alhaji Mallam ya ɗauka daga nan sauran abokanan su kowa saida yasa musu albarka, Daddy da Abba ma sun musu nasiha sosai.

Daga nan wurin hajiya mama aka kaisu, itama ba'a barta a baya ba, haka aka ta bi dasu, suna sallaman dangi, mummy kam ɗakinta ta shige ta ɓame, koda ummi ta tura ƙofar dakinta taji shi a rufe a waya ta kirata wai tana inane amare zasuyi sallama da ita, jin haka dama abinda take dugarma ke nan, sai cewa tayi bata cikin gidan su tafi kawai Allah ya bada sa'a.

Mutane ƴan zakiyar amare tuni kowacce ta samu mota ta kame, ƴan dama ta biyu fans haka suka lodu cikin motoci wasu kan cinyan wasu, wasu ma har a boot, nima allah ne ya soni har zan shiga boot dan ban samu guri ba ,kiy kurs ta yafito ni na zauna a cinyarta, su kakus dai ana boot ido ya raina fata, tare za'ayi tafiyar' ma'ana zasu raka junan su, za'a fara kai batool daga nan akai Asmah, sai Amira, sai kuma a zarce bidda inda za'a kai zahra,. Kowacce motar da aka kawo na musamman domin ta aka nufa don sakata saidai hakan bai yuwu ba , dan zahra da batool kam kankame juna sukeyi , suna wani irin kuka mai ban tausayi ganin haka yasa dole aka saka su a guri ɗaya,.

Gidan batool aka fara zuwa dake nan M,I sauka akayi aka shiga da ita gidan sama ne dankarere Wanda misalta muku shi bata lokaci ne, sabo dal haka ma kayan cikin gidan sababbi ne, ga kuma sabuwar amarya, da sabon ango,Abin zad dadi,.

Bayan dangin Dr bash waɗanda da suke nan dan kar bar amarya sun karbe ta, abincin tarbar amarya mai rai da lafiya aka gabatar musu kasancewar suna sauri yasa suka saka a mota idan an koma gida aci,.

Tashi aka shigayi ana fitowa domin tafiya, nan fa kallo ya koma sama dan amare dai kamkame juna sukayi su hudu suna sharban kuka, da'ker aka samu aka banbare su daga jikin juna,.

Kasancewar basu da wasu kawaye sosai yasa wasu kawayenta sabbi ne ma dan a school ta haɗu da su su biyu suka tsaya da ita zuwa sanda ango zai shigo suma su san nayi a bar ango da amaryarsa,.

Ganin abinda sukayi a gidan zahra yasa lokacin da suka isa gidan Asmah, ba'a bari Amira da zahra sun fito daga mota ba, a nan aka barsu aka shiga aka mata rakiya,.

Itama dankarern gida ne mai girman gaske don yayi Na batool biyu, saidai shi part uku ne a gidan dan haka aka lalubi nata aka sakata, itama sabbin kawayenta ne suka tsaya da ita,.

Haka aka garzaya gidan Amir dake albishir, daga nan kuma waɗanda zasu koma gida suka koma waɗanda zasuyi rakiya zuwa bidda kuma suka dauki hanya, saidai muyi fatan Allah ya kaisu lafiya,.

nikam dai bani cikin yan zuwa bidda dan allah allah nakeyi naje gidan batool naga ya zasu kwashe da dr bash, harna kama hanya na ni kaɗai zan tafi, na dawo cikin sanɗa na yafito ummu muhammad naser, na mata kuskus a kunne, itama saɗaɗowa tayi ta biyo ni, ganin haka yasa ameera dake ankare da duk wani motsin mu yasa ta biyo mu a baya da gudu ba yacce muka iya dole muka tafi da ita.

Bari mu fara da mutuniyar taku😜

~BATOOL~
Chapter 43 · 0% Book details