← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 126

Sashe 71

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka ci gaba da Rayuwa har tsawon sati hudu babu wani sauyi a game da zaman su, Dr bash yayi iya kokarin da zaiyi ya shawo kanta yayi Abu yaci tura, dole ya koma gefe ya zura wa sauarautar Allah ido ,gefe daya kuma ya dukufa da addu'a, kuma alhmdllh yaga alfanun hakan dan yanzu rawan jikin nan da takeyi idan ta ganshi ta daina, takan fito falo ta zauna tayi kallo wani bin ma suyi tare ammafa tana a takure dan ko kallonshi bata iya yi, idan ya mata magana zata amsa shi amma ba tare da hada ido dashi ba, yakan shiga dakin ta idan bukatar hakan ta taso yanzu ta daina garkamewa, shima kuma bai kara nuna yana son koda rike hannunta bane,duk da a matukar takure yake, kullum daren duniya daker yake iya bacci amma ya daure yaci gaba da gayawa mai duka, hakan kuma yasa ta dan fara sakin jiki kadan kadan dashi.

Zaune take a dakinta a gaban dressing mirror fitowarta daga wanka kenan, zata yi shafe shafe,cike take da tsantsar damuwa tun last 2 Weeks take ta zuba idon ganin period dinta amma shiru, abin tun tana dauka wasa har gashi ta kwashe sati biyu cur ba amo ba labari, abinda bai taba faruwa da Ita ba, tunda ta fara al'ada bai taba kin zuwa mata ba, kuma bai taba canza mata lokaci ba, imma ya canza baifi ya kara kwana uku ko biyu ba amma wannan karon gashi har 2 weeks, da wannan tunanin ta shiga shafa man shafa warta, tun kan tayi nisa ta fara jin kamshin man da take mutuwar so yana shiga mata hanci yana tayar mata da zuciya daure wa tayi ta CI gaba da shafawa a jiki, ta gama da jiki tana kai hannunta fuska wani irin yun kurin amai ya taso mata ba shiri ta mike da gudu zuwa toilet ta shiga kelayawa.

Daidai wannan time d'in Dr bash cikin shirin shi na tafiya hospital, ya nufo dakinta dan ya mata sallama, wayar shi kare a kunnenshi, waya yake yi da maah, tana kara jaddamai mai ya kula da batula da abida ke cikinta kuma in ya tashi aiki ya biyo akwai jike jiken da masu ciki kesha maganin zaki da sanyi , tasa an hado ma batool d'in ya biyo ya karba, shidai kawai da to yake amsa mata yana mata godiya, a karshe ta nemi ya hada ta da batool d'in taji lafiyar ta.

Yana isa kofar dakin yayi sallama har sau uku bata amsa ba hakan yasa ya kutsa kai kawai cikin dakin yana shiga yaji kakarinta a toilet ga kofar toilet d'in a bude, baisan sanda ya katse kiran maah ba ya ajiye jakar sa ya nufi toilet d'in da sauri, aamunta yayi duke a toilet din ta dafa kwamin wanka da duka hannayenta, sai kwarara amai tajeyi baji ba gani, da gudu ya karasa ya tallabota jikinshi, a haka ya samu ta gama aman, amai tayi bama wasa ba don babu abinda yayi saura a cikinta na daga ruwa da abincin da taci.

Jikin ta gaba daya ya saki lokaci gudu, taimaka mata yayi ta kuskure bakin ta ta wanke fuskarta, rungumota yayi ya fito da ita a toilet d'in, yadda tayi lamo a jikinshi abin ya matukar bashi mamaki, idan ya kula da kyau harda kara cusa kai yaga tanayi a kirjinshi tana shaqan kamshin jikin shi tana sauke ajiyar zuciya a wahalce, kan gado ya direta yana binta da kallo, matsayin shi na Dr baya bukatar Karin bayani daga bakin wani tsab ya fahimci meke damunta, farin ciki ne fall a ransa kamar ya daddage ya tsala ihu haka yakeji amma sanin wacece batool yasa ya Adana farin cikin shi ko a fuska bai nuna wani abuba, ba karamin aikinta bane ta saka mai rigima bata son cikin, bazai yi gangancin sanar da ita ba har saiya tabbatar tana son cikin tukunna, take kuma idan shi ya sauka akan wayar shi dake ajiyar bakin bed, maah ce ta fado mai arai baisan sanda wani kayataccen murmushi mai sauti ya subuce mai ba, Wanda har saida batool dake kwance kan bed idonta a runtse, ta ware idanu akan fuskar shi.

Wani yarr taji a jikinta, tsigar jikinta ya fara tashi, wani irin azabebben feeling taji ya ziyarce a lokaci daya, bata San ta ƙura mai idanu ba, Dr bash mamakin irin kallon da take binshi dashi yake yi, tunda abin nan ya faru a tsakanin su bata taba bari sun hada idanu sun kalli cikin idan juna ba , amma yau a lokaci daya ji yadda take binshi da wani irin mayen kallo kamar zata cinye shi.

Dage mata gira daya yayi tare da cewa "yadai" sai lokacin taji wani kunya ya kamata tayi kasa dakai, murmushi ya saki tare da cewa "zan tafi office inada theater da karfe goma sha daya, amma zan kira maah ta turo miki Afrah tazo ta zauna dake kafin na dawo bazan wani dade ba yau saboda ke ina gama abubuwa masu mahimmanci zan dawo" ba tare da ta kalleshi ba ta gyada mai kai, sa kai yayi ya fice daga dakin bayan ya dauki wayar shi da jakar shi.

Da kallo ta raka bayan shi har ya kule ma ganinta, ji take kamar ta jawo shi ta shige jikinshi ta shaki daddaɗan kamshin turarensa ko zata samu sauki akan abinda takeji yana taso mata game da shi,rutse ido tayi tana matse kafa, a bayyane ta furta"innalillahi wainnailaihi rajiun, meke shirin faruwa da nine ni batool na shiga uku na ya rabbi ka kawo min dauki"...............

Masu comment dina,ina mika muku dinbim godiya wlh naga zafafan comment ɗinku jiya kuma na karanta na yaba, wlh saboda ku kawai yau nauyi typing, kuyi min hakuri kar kuga ban yi reply ba, bani da isahen time da kuma caji ne, amma wlh duk na gani naji dadi sosai wlh inayinku irin totally dinnan💋 a ci gaba da gashi dama ta biyu insha Allahu yazo gangara saura kiriss💖

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabillilah🙏

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARI NE MALLAKINA NE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌

(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira 👌 a kiyaye pls)

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiy,Allah kajiqan iyayen mu}

💖Tallah!💖 Tallah!!💖

💖Tallah!!!💖

💖

Albishirinku manyan mata! ma'abota kwalliya da
_Rantsattsun lesussuka💃,
_Atamfofi manya da k'anana💃
_Galla gallan shaddodi manya da k'anana muna da su kowani iri💃
_Akwai kuma yadiddikan maza kamarsu koranza,plan yard dadai sauransu💃
_Munada mayafai, takalman maza da mata,sarqoqi, awarwaraye,da duk sauran nau'ikan kayan ado na maza da mata muna dasu 💃
Akanfaninmu na""R & U""Global Enterprise Dake Nan Garin Minna Niger State, saikunzu..........

Ga numbern mu kamar haka👇
08062160424
08066891424.....

Sayan day'a ko sari acikin farashi mai sauqi👌
Kubamu odern ku,danshine aikimmu akoda yaushe da yardar Allah........👌
Sai an gwada akansan na kwaraiiii💃💃💃.....

Page 104

Ko awa ɗaya Dr bash bai rufa da fita ba Afrah da afnan suka iso, har zuwa wannan lokacin tana kwance inda ya barta, dan kwata kwata batajin karfin jikinta,cike da tausayawa suke jero mata sannu kai kawai take iya gyada musu, Afnan ne ta gyara toilet d'in ta wanke shi gaba daya saboda amai da ya bata, ita kuma Afrah tambayar batool tayi me zataci, dan Dr bash yace idan sunje su Samar mata abinda zataci, saida ta tsaya tayi dogon tunani kafin tace "banbara," Afrah tace "bambara kuma anty, kina da tawaska ne?" batool ta girgiza mata kai alamar babu, Afnan ne da ta gama wankin toilet ta fito take tambayar menene babu, Afrah tace "wai bambara take so kuma babu tawaska a gidan" Afnan tace "Ai dole a nemo tawaska duk inda yake, a kwai a gida,bari na kira maah taba direba ya kawo sai a mata" ba bata lokaci kuwa sai gashi nan kuwa maah ta bayar an kawo.

Cikin abinda baifi 40minute ba suka gama soya mata shi yako ji albasa da mai, da suka kawo mata har rawa jikinta keyi tsabar yunwa da takeji gashi idan ba banbaran ba batajin zata iya cin komai, hannu baka hannu kwarya take ci ko kula da zafin shi batayi, kan kace kobo sai plate d'in.

Tana gama ci kuma take wani sabon al'amari ya ziyarceta,babu abinda take bukata a halin yanzu irin mijinta, feeling takeji sosai, ga kuma kamshin turarensa da take maitar so, daurewa tayi ta share, sunata fira dasu Afrah, can dai ta kasa daurewa dan ji tayi kamshin nata dakin ya fara tayar mata da zuciya, Afrah ta kalla tace "dan Allah anty Afrah kije ɗakin yayanku dake kasa ki dauko min duka turarukan sa da kika gani akan mirror" Afnan cikin wasa tace "tofah! da alama dai wannan babyn namu dan rigima ne, yanzu kuma turaren big bro yake so" dariya suka saka ita da Afrah, itadai batool bata wani fahimci zancen da sukeyi ba.

Afrah fita tayi taje dakin ta kwaso mata duk wani turare dake kan mirror manya masu tsadar gaske kusan kala bakwai, da sauri ta amsa ta shiga budewa ɗaya bayan ɗaya tana shaƙa, daga Wanda zai kusa sata amai, sai mai mata warin asibiti, harda mai kamshin hypo duk taji, ba shiri tasa aka tattara su aka mayar, duk sun tayar mata da hankali, karshe dai saida ta a maye banbaran da taci hankalin ta ya kwanta.
Chapter 71 · 0% Book details