← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 126

Sashe 106

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Muryar Asmah ne ya katse mata tunani, cikin kuka tace "mummy shike nan zan rasa ya Aslam, shike nan lokacin rabuwar mu ya gabato,mummy ya Aslam zai juya min baya ko?"goge hawayen ta tayi kafin kafin ta tausasa muryar ta tace"wa ya gaya miki haka Asmah? Kar na sake ji kin fadi haka Aslam bazai taba juya miki baya ba domin kuwa yana tsananin kaunar ki."tace "Mummy tsoro nake ji gabana faduwa yake yi." Mummy tace "Kiyi ta maimaita inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, zaki samu sauki a zuciyar ki." Gyada kai kawai ta ringayi tare da sauke wasu irin ajiyar zuciya, dago ta mummy tayi daga jikin ta, ta tallaɓe ta nufi ɗakin ta da ita. Zaunar da ita tayi a bakin bed ta taba jikin ta zafi zau kuwa daman tasan za'a rina, magani ta kalli ta bata dakyar ta haɗiya tana gama sha sai amai shaa, cike da tausayawa mummy ta tallabe ta, har ta gama a mayar da duk abin da taci, toilet ta kaita ta kuskure baki ta wanke mata fuska, ta zame mata dan kwali ta zuba mata ruwan sanyi a kanta, sannan ta tallabo ta ta dawo da ita dakin ta kwantar da ita akan bed ta gyara wurin, ko kafin ta gama tsabtace gurin bacci ya kwashe ta, sauke ajiyar zuciya mummy tayi tare da rage mata karfi Ac ta fice daga dakin ta ja mata kofa a hankali.

A tare Aslam dasu Amir suka fito daga falon Alhaji baba, Kamal yana sauri zai koma gurin aiki don dama excuse ya dauka, hakan yasa bai shiga cikin gidan ba ya fada motar shi jiki a sanyaye yabar gidan, wannan abin da ya faru ya taba mai zuciya sosai, kwarai ya tausaya wa Asmah.

Amir kuwa bayan Aslam yabi domin ganin duk yadda ya duburbuce ya susuce a halin yanzu yana bukatar mai kwabatar mishi da hankali, binshi yayi da sauri ya kama hannun shi hakan yasa Aslam sauke mishi jajayen idanun shi, gyada mishi kai Amir yayi kafin a hankali ya shiga jan shi suka fara tafiya, parking lot suka iso ya buɗe motar shi gidan baya ya ce ma Aslam "Bismillah bro magana nake so muyi." Shiga motar yayi Amir ya maida kofar ya rufe tare da zagayowa ta daya side din shima ya shiga ya zauna tare da rufe kofar, a tsanake ya kira sunan Aslam cikin kamewa hakan ya tabbatar wa da Aslam cewa maganar da zai fada mishi mai muhimman ci ne, shima tattara dukkan hankali da nutsuwa shi yayi ya baiwa Amir din, domin a halin yanzu yana bukatar wanda zai rarrashe ya kwantar mashi da hankali shi ya bashi shawara ta gari, kuma yana da tabbacin zai samu duka wandannan abubuwan daga dan uwan shi abokin shi yayan shi Amir.

A can falon Alhaji baba kuwa zee mami da Abba ne kawai suka rage.
Abba kam dan nasiha ya ƴara ma zee din ita kadai, akan cewa ta kwantar da hankalin ta kar abin da Aslam ya faɗa ya firgita ta, shima ɓacin raine ya saka ya faɗi haka taje ta kwantar da kai tayi ladabi tayi biyayya, ta nuna mishi da gaske ita ɗin ta canja daga yadda ya santa a baya, in sha Allah komai zai daidaita, ta toshe kunnen ta ta rintse idanun ta danne zuciyar ta akan dukkan abin da zata fuskan ta daga wurin Aslam, idan tayi hakuri naɗan wani lokaci komai mai wucewa ne. Nutsuwa tayi ta bada dukkan hankalin ta tana sauraren nasihar Abba, bayan ya gama tashi yayi ya fice daga falon nan mami ma ta daura da nata. Daga karshe kuma suka baro part din alhaji baba suka dawo na mami.

Kusan awa daya suka kwashe yana bashi baki tare da kwantar mai da hankali yana kuma kara koya mai dabarun yadda zai zauna dasu su biyu ba tare da ya shiga hakkin daya ba, sai da Amir ya tabbatar ya kwantar mai da hankali, daga karshe ya dinga zolayar shi har sai da yaga yayi murmushi, kafin ya barshi, nan sukayi sallama, Amir ya tafi gidan shi yayin da Aslam ya nufi part ɗin mummy, domin duk abin da yake yi karfin hali ne kawai saboda bai San halin da take ciki ba.

Koda ya shiga bai ganta ba mummy kawai ya samu a falo, zama yayi suka gaisa ba wani sakin fuska, daga gaisuwar kuwa duk zama sukayi shiru, yana ta zuba idon ganin ta ina zata fito shiru gashi har yana neman kwashe awa ɗaya a zaune, can dai ya da ya gaji, yace "Mummy husnah tana ciki ne ina son tazo mu wuce." A dake tace "eh tana ciki amma yanzu tana barci ka je kawai bayan isha'i sai ka dawo ka dauke ta." Tana gama faɗin haka ta mike tayi ciki domin ta gama abin da ya zaunar da ita a falon.

Badan yaso ba dole ya sa kai yabar gidan domin dai mummy bata daukar wargi, balle yadda ranta ke bace yau gaba daya......

Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}

Page 126

Kamar yadda daddy ya faɗa karfe biyar na yamma daidai ya sauke zee a farfajiyar gidan Aslam, makulli part ɗinta daya amsa a hannu Aslam ɗazu ya damka mata, har kasa ta tsuguna cike da ladabi tana godiya, yace "Ba komai zainab ɗa na kowa ne, Allah ubangiji ya Baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba." Ta na tsaye har motar shi ya bar harabar gidan, mai gadi ya maida get ya rufe. mai da kallon ta tayi kan ɗaya plat ɗin da yake nan sak irin nata, ji tayi wasu siraran hawaye sun ziraro mata ko shakka babu nan ne part ɗin Asmah, compound ɗin gidan tabi da kallo tsab tsab dashi yana nan yadda ta sanshi a baya, sai dai a yanzu yafi da kyau sosai nisa ba kusa ba, domin ga dukkan alamau yana samun gyara da kulawa fiye da lokacin da ta ke gidan a baya.

Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban na ta part ɗin ta saka makullin da daddy ya ba ta buɗe, sai da ta yi addu'o'i sosai sannan ta kama hannun little suka shiga da sallaman ta a bayyya ne. Falon dumɗum da dubu ba haske kuma ko ina a kukkule, makunnin wuta ta laluba ta kunna take kuwa haske ya gauraye mai falon, bin ko ina ta shiga yi da kallo, take ranar ta, ta karshe a falon ya shiga dawo mata fresh a kwakwalwar ta, ranar da take ta malelekuwa a tsakiyar falon nan jini na kwaran ya daga jikin ta, ranar da Aslam ɗin ta ya saka hannu ya buge ta kamar yana bugun kato tsaran shi, kallon little tayi da yake ta wasan shi, a falon babu damuwar komai a tare da shi, samun kanta tayi da durkushewa a hankali a gurin da take tsaye tare da fashe wa da kuka tunawa d tayi duk abubuwan da suka faru akan zuwan shi doron duniya ne, gashi karshe duk gwagwarmayar da aka sha sai da ya shaki iskan duniya, tayi imani da maganar magaba ta da suke cewa, a duniyar nan babu wanda ya isa ya kashe wani ruhi face sai idan lokacin wannan ruhi yayi, sai dai kawai mutum ya zama sanadi amma badai shi ya kashe shi ba, Allah ne mai kashe wa kuma mai rayawa a duk sanda yaso, shi yake fitar da rayayye cikin matatce haka nan shi yake fitar da matatte cikin rayyaye kamar yadda ya faɗa a cikin alkur,ani mai tsarki.

Ta kusa kwashe 30 minutes a haka sai kuka take tana ƙara tunani da miƴa wuya akan lamarin ubangiji, sai da little ya gaji da wasan shi ya dawo ya faɗa jikin ta yana ce mata zai sha ruwa sannan ta dawo hayyacin ta.
Chapter 106 · 0% Book details