← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 126

Sashe 115

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Anyi haka kamar da kwana biyar Dad ya dira a Nigeria shi kaidai dan ko mom bai gayawa zai zo ba, direct a Niger state ya sauka, ko huta baiyi ba ya dauki shatar taxi yayi ma gidan Aslam diran mikiya, part ɗin ta daya sani tun farko ya nufa mai gadi na tare shi ya wanka mishi mari, suna zaune a falon ta kamar yadda suka saba suna hira, cikin nishaɗi zee nata tsokanar Asmah dake ta mata complain akan maganar tumbi,zee na cewa to kodai ciki ne, Asmah tace cikin lafiya ban fa Dade da gama period ba sai dai idan wani ciwon ne nidai wlh asibitin zani, kafin zee ta samu daman bata amsa , suka ji an shiga bubbuga ƙofa ba kaukau tawa duk sun tsorata musamman Asmah da take da saurin tsora ta har sai da taji wani abu yayi zillo a cikin ta, zee da yake ta ɗan fita karfin hali, ita ce ta tun kari kofar ta buɗe, gaban ta ne yayi wani irin mummunar faɗuwa har sai da ta yi saurin dafe shi, take kuma marar ta yayi wani irin murdawa, wanda ta gani a bakin kofar yana huci kamar mayuncin zaki tabbas ba kowa bane face Dad ɗin ta take ta duke a wajen tare da kama marar ta duk da haka kuma tana karfin hali ja da baya dan ta tsere mishi, duk da Asmah bata San shi ba ta tsora ta ainun da ganin shi hakan yasa itama ta fara da ja baya tana yarfe hannu, shigowa falon yayi ya tunkari zee da ke daga kafa daker daker tana rintse idanu numfashin ta na seizing baiyi wata wata ba ya dauke ta da wani irin mahaukacin lafiyayyen mari, abin da bai taba shiga tsanin su ba a tarihin rayuwar ta wai Dad ya mare ta, ko lura da yanayin da take ciki bai yi ba idanun shi sun rufe fisgar hannun ta yayi ga shiga janta, tana daga duƙe dafe da marar ta, ta shiga dan kokarin coge wa amma ina bata da wannan karfin ganin haka yasa Asmah kwasowa da mugun gudu ta biyo su ta rike ta da karfi tana kuka tana canja, tun da dai ita ba sanin Dad tayi ba, baza taba bari ya tafi da zee a gaban ta sai dai ko ya haɗa su, su biyu ya tafi da su, ganin Asmah ta na jan zee yasa ranshi ya ƙara ɓaci da wani irin karfi ya fusge su gaba daya dukan su sai da suka watse a kasa, Asmah ta bugu da kujera bai bi takan hakan ba ya fisgi hannun zee da karfi gaske yayi waje da ida, daidai sun iso tsakiyar compound din gidan cikin hukunci ubangiji motar Aslam ta shigo gidan duk da lokacin dawowar shi bai yi ba, akan abin dake faruwa direct idanun shi suka dira, wani irin burki ya taka tun daga bakin get da wani mahaukacin gudu ya fito daga motar ya nufosu, baiyi wata wata ba yasa hannu ya fisge zee daga hannun Dad take ta zube a wurin yaraf ba numfashi tsugunawa yayi akan ta yana jijjigata da karfi yana ambaton sunan ta hankali tashe, muryar Dad ne ya katse shi,a fusace cikin kaukausar murya yace kai tsinanne dan matsiya ta ka kyale min ƴa ta dan uban ka." Jajayen idanun shi ya dago ya zuba a fuskar dad, zuciyar shi yaji yana tafasa tsabar fusata har wani rawa labenshi yake yi baki ya bude zai yi magana amma ya kasa, kuma hakan ya taimaka dan duk abin da zai faɗa a lokacin bazai zama alkhairi ba , wani irin tafasa zuciyar shi ta shiga yi, tun daya kafe Dad da ido bai ko kefta ba , kawai hasaso ta ina zai kai mai makura yake yi.......

Idan naga ruwan comment akwai update anjima

Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}

Page 130

Ganin yadda Aslam ya kafe shi da jajayen idanun shi yana huci kamar wani mayunwacin zaki, sai da ya firgita , amma dake riƙƙeƙen ɗan duniya ne daure wa yayi ko a fuska bai nuna ya razana ba sai ma ci gaba yayi da cewa"Ba da kai nake magana ba fitsararre ka zuba min wasu kwala kwalan idanun ka makar na kwadi, nace dan uban uban ka ka kyale min ɗiya ta." Bai dauke idanu akan shi ba kuma bai kyale tan ba, "OK baza ka kyale ta ba ko? To ina zuwa a kwai wadanda zasu shiga tsakani na da kai, zaka gane ƙaramin ɗan iska ne kai." Yana gama faɗin haka ya juya da sauri fuuu kamar zai tashi sama ya fice daga gidan, abu biyu ne ya saka shi fice wa ba tare da zee ba, na farko dan ya gujewa wannan kallon da Aslam ke mishi dan har ga Allah ya tsora ta da yanayin shi, yasan bai da ƙarfi yin dambe da Aslam koda hakan ta kama sai dai a nakasa shi a banza, na biyu kuwa dan ya kwaso police suzo su tafi da Aslam, dan wannan karon yayi alkawarin sai ya wulakan ta shi, don idan ya kulle shi a wannan karon, in ba wani ikon Allah ba sai dai ya kare rayuwar shi a gidan maza. Har ya fice daga get ɗin Aslam bai ɗauke kanshi daga kallon shiba , ba komai ne ya hana shi haɗa ma Dad jini da majina ba, sai dan darajar mutum biyu masu daraja a gareshi na farko little na biyu kuwa ita ce zee, duk lalacewar Dad mahaifin ta ne, Kuma su iyaye komai munin halin su ba'a kin su tana son uban ta sosai kamar yadda shima yake son ta, idan ya mishi wani abu makamancin duka ko zagi tabbas idan ta farka baza ta ji daɗi ba, ga kuma little da sauran ƴaƴan da zasu haifa nan gaba tare da ita, idan har ya duki Dad zai zama abin gori ne a gare su kuma ma ai shi yana da ilmi idan ya biye mishi sun zama ɗaya kenan.

Da'ker ta samu ta lallaba ta lalubi jikin kujera ta dafa ta mike, tana jin ta tsaye kan ƙafafun ta take duk abin da ke faruwa ya shiga dawo mata da gudu ta nufi waje tana kwala kiran anty zee hango sun da tayi yasa ta nufo su, ganin zee kwance a hannun Aslam bata numfashi yasa ta sauri duƙewa cikin tashin hankalin da tsinkewar zuciya ta shiga jijjjgata tana kiran sunan ta, shiru babu ko alamar zata motsa, dago hannun ta da zata yi da nufin ta tashi taje ta kawo ruwa a yayyafa mata sai ganin hannun tayi caɓal da jini, hankalin ta ne ya kara tashi cikin kuka tace "innalillahi wainnailaihi rajiun,shike nan ya Aslam ya kashe mana ita." Sai lokacin ya lura da hannun Asmah shima hankalin shi ba karamin tashi yayi ba yunkurawa yayi ya miƙe da ita sai ga jina faca faca ya na bin jikin ta, a guje ya nufi mota da ita ya buɗe bayan ya kwantar da ita, itama Asmah rufa mai baya tayi ta buɗe gefen me zaman banza ta shi a haukace ya figi motar ya fice daga gidan, sunzo dai dai fita kwanar gidan wanda zai hau da su babban titi suka ga cincirundon mutanen a tsatstsaye tun daga nisa ya din ga danna horn, ganin yadda yake mugun gudu yana danna horn yasa tun kofin su karaso wajen mutanen suka dare suka basu hanya, bai tsaya bi ko tambayar meke faruwa ba ya harba kan babban titi ya dauki hanyar wani babban private hospital, yana shiga aka karbe ta akayi emergency room da ita, likitoci kusan uku suka rufa akan ta domin ceto rayuwar ta abin ka da asibitin masu kumbar susa
Chapter 115 · 0% Book details