← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 126

Sashe 22

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummy tace" my son kaima har ka dawo ne haka da wuri yau" yace" a'a mummy nad'an samu free time ne , shine nace bari na dauko qannai na da kaina," mummy tace"kako kyauta wlh" murmushi yayi yace "mummy bari na koma" tace "to kamal Allah ya tsare". rarraba idanu ya shiga yi a falon alamar yana neman Abu , duk mummy na hankalce da shi, ganin dai bata falon yasa ya miqama batool jakar ta , yace"batool ga jakan Asmah ki bata " juyawa yayi ya fice a falon yana qara ma mummy sallama,

Suma su batool d'aki suka wuce bayan sun gaida mummy, mummy ma miqewa tayi ta nufi kitchen, don ta duba abinci ganin yaranta sun dawo, koda ta gama kuma bata dawo falon ba ta wuce d'akin ta.

Aslam ci gaba yayi da zama a falon shi kadai sai saqe-saqe yake, kusan twenty minutes mummy ta dawo ta duba abincin ta yayi ,don haka ta jere a dining,

Falon ta dawo tace ma Aslam abincin yayi ready , cewa yayi yace ,"ya qoshi" daga kafad'a mummy tayi , alamar, ko a jikina d'innana, ta wuce dinning abinta,

Su batool saida sukayi wanka sukayi sallah , sannan suka fito falon donyin lunch, still Aslam na falon,

Yana jin mostin step ana saukowa daga upstairs ya dago kai ya qurawa hanyan ido, kuri idanunshi a kanta baya ko keftawa,

Su basu ma san yanayi ba , dinning suka nufa , anan suka tarad da mummy , serving d'insu mummy tayi suka fara yin lunch d'insu hankali kwance,

Ganin sun manta da wanzuwarshi a falon ne yasa ya miqe ya nufi dining d'in, mummy ta kalle shi tace "ya akayi ne , ko zaka koma kenan " yace " no zanje part dinmu ne wajen amir, kibra Asmah abincin ta kawo min inta gama' to kawai mummy tace, fita yayi daga sashen mummy ya nufi nasu sashen,

Zama yayi a falo yana jiran zuwan Asmah, so yake ya gargad'e ta , ta rabu da kamal taje ta samu mijinta a wani zuri'ar , ba tasu ba, shi daso samune ma ta samu miji acan wani gari inda zai daina ganin ta ko zai samu salama da irin azabtarwar da zuciyarshi ke mai akanta, can kuma wata zuciyar ta gargade shi da cewa kana tunanin zaka iya jure rashin ganinta idan tabar gidan nan, zuwa gidan wani , bama garin minna ba, a fili ya furta" inaaa! zuciyata baza ta lamunta ba," cigaba yayi da cewa "wlh Aslam ka zama ragon maza tunda baza ka iya tursasa zuciyarka akanta ba, don jarumi shine wanda yake iya tursasa zuciyarshi ya hanata abinda take so" tsaki yaja , ya dunqule hannunshi ya naushi iska tare da furta "Ooh shirt"

Amir da shigowan shi falon kenan ya qaraso da sauri hango Aslam da yayi zaune yana naushin iska, yace " lafiya Mallam kazo kana mana naushe naushen iska a d'aki, kaida waye, ko amaryar take ce ta kunno ka " kallon amir yayi yace "nida wad'an nan yan rainin wayon ne kamal da Asmah" Amir a zuciyarshi dariyar qeta yakeyi amma a fili yayi kamar yana taya Aslam jin haushi, cikin yanayin nuna jin haushin su yace "me kuma suka qara yi maka yau" Aslam kunno status din kamal yayi ya miqawa Amir yace "kalla fa"

Amsar wayar amir yayi yana kallon hotunan saida ya gama kallo tsab ya kashe da wata irin dariyar mugunta harda riqe ciki, a jiye wayar yayi ya tashi tsaye, ya fara rawa yana wakar

♪♪♪abin ya mosta♪
♪♪♪yana dukan rai♪
♪♪♪ya bakin ganga♪
♪♪♪soyayya ce ♥

Qara kunnuwa Aslam yayi ji yake kamar ya shaqe Amir d'in, kozaiji sanyi ,

A part d'in mummy kam suna gama cin abincin mummy ta had'a ma Aslam abinci a tire ta miqawa amira tace taje ta kaimai , a ranta tana cewa yaro in kasan wata baka San wata ba ai, Batool tace "mummy Asmah fa yace aba " mummy ta mata daquwa tare da cewa "gidan ku batool, ni kurma me ce kenan, banjiba ko" batool tace "sorry mummy" mummy tace "cikin Amira da Asmah wa ya saba aika " batool tace "Amira" tace "to kin gani may be yazo cewa Amira ne ya manta yace Asmah'"

Amira na sallama a falon Amir ya tsaya da rawar da yakeyi ya nufota da sauri yana cewa" babyna keda kanki, " murmushi tayi , ya amshi tiren hannunta , gaishe shi tayi ya amsa mata cikin kulawa , tace"abincin ya Aslam' ne mummy tace na kawo mishi". "OK to barin miqa mishi, yanzu kije ki huta anjima zanzo muyi hira kinji" cikin dan jin kunya ta amsa mishi da to sannan ta juya ta wuce,

Ajiye abincin a gaban shi Amir yayi yace "bismillah" ji yayi gaba d'aya abincin ya fita ranshi , mummy ta rusa mai shirin shi miqewa yayi ya fice fuuu ya nufi tsohon d'akin , yabar amir nan yana tsokanan shi ko kulashi baiyi ba,

Amir yace zama ka dawo hanya ne uban yan taurin kai , zanga karshen wanna girman kan naka, kana son yariya amma girman kai ya hana ka yarda , kuma insha allahu Asmah sai kamal donni bana goyan bayan qarya ehee,

Kwanciya yayi a kan tsohon bed d'inshi yayi ruf da ciki, tambayar kanshi ya shiga yi shin wai da gaske sonta nake, to indai wadannan abubuwan da nake ji game da ita sune so, meyasa banjin hakan akan zee da take matata da mukayi auren soyayya, kai ina hakan bazai taba zama so ba, saidai in wani mugun abin tamin, tunda dama jikar Mallam ce, wayar shi ya dauka ya shiga Google don yin bincike akan alamomin soyayya,

,( hmmmm su Mallam Aslam an shiga ajin sanin alamomin soyayya, Allah ya bada sa'a😅)

Zee kam yau taga rayuwa, tun karfe biyu take saka ran ganin Aslam, shiru shiru har la'asar , yunwa ta gama sakad'arta, duk tayi laushi, kitchen ta nufa ko zata iya sarrafa wani abun ta samu ta zuba ma tumbinta, indomie ta dauka guda biyu , duba bayan ledan tayi anan taga yadda ake dafawa, nan tayi ta bin method din da taga ni a bayan ledar indomin har ta samu ta kammala da'ker, duk da haka ba wani dadi haka dai ta cuccusa, maganin yunwa , baza baza tayi da kitchen d'in kamar ba dazu Aslam ya gama share wa ba , nan ta bar shi haka ko cokali bata wanke ba , amma dai yanzu ta kashe hot plate d'in,

Aslam sai kusan magriba ya gama binciken da zaiyi a Google, duk wani amsa da yake nema ya same shi, yanzu kam ya tabbata son Asmah yakeyi soyayya mai tsanani ma kuwa ,soyayyar da tun baisan kanshi ba tun bai gama zama cikakken mutum ba take fama da ita, soyayyar da ta qullu a gani na farko, soyayyar da ta dauki tsawon shekara goma sha biyar a cikin zuciyarshi tana wahalar da ruhin shi, yanzu wa zai tunkara, ta ina zai fara, yasan duk ta inda yace zai fara akwai babban matsala, shawara d'aya, ya yanke shine zai fara ta kanta , zai fad'a yaqin neman soyayyar ta yasan idan yayi nasara a kanta komai zai iya zuwa mishi da sauqi, (hmmmm Aslam kana ruwa)

Sai qarfe takwas Aslam yabar yabar gidan bayan ya cika tumbinsa da abincin da momi ta aiko mai d'azu, saida ya sake biya wa sashen mummy ko zai samu, qara ganin Asmah, amma kowa ma bai samu gani ba , haka ya shiga motar shi ya tayar ya nufo gida cike da fargaban mai zai tarar kuma,,

Yana shiga harabar gidan ya tarar ba daya motarshi dake fake a compound din gidan , sharewa yayi ya shiga falon bai kawo komai a ranshi ba, yana shiga baiga zee a falo ba , duba dakinta yayi baibganta ba nan ya shiga kwala mata kira shiru, neman duniya yama zee a gidan bata nan, neman gurin yayi ya zauna a falon ya rafka tagumi,

Zee kam tana ganin 7:30 yayi Aslam bai dawoba , taci kwalliyar ta ta dauki key motar shi ta bar gidan a cewarta baza ta iya zama ita d'aya a gida kamar mayya ba, yawanta ta dinga yi kamar yadda ta sabayi a gida, dama duk qafarta qaiqayi take mata kwana biyu nan da tayi bata fita ba, bata nan bata can haka ta dinga yawo , saida taga tara tayi ta biya safara food tayi take away ta kamo hanyar gida

Tun a wurin parking ta ga motar da Aslam ya fita da ita alamar yana ciki kenan tabe baki tayi, ta dauki ledarta ta nufi cikin falon , bako sallama ta shiga ,

Aslam dagowa yayi ya kalleta cikin bacin rai yace"daga ina kike" tace "nad'an fita shan iska ne' yace"wa kika tambaya " tace "bangane wa na tambaya ba, kana nufin idan zan fita a gidan nan saina tambayeka,' yace "of course saboda zamana kikeyi a gidan nan' wani murmushin rainin wayau tayi tace " haba dai sai kace wata qaramar yarinya da duk inda zani saina tambaya"yace " haka kikace ko to wlh kika sake fita a gidan bada izinina ba sai na nuna miki true colour na" tabe baki tayi ta wuce ciki abinta bata ba maganar shi wani muhimmanci ba,

A d'akin ta taci abincin ta ta yadda take away din a gurin taci gaba da sana'ar tata na charting,

Aslam kam zama yayi abun duniya duk ya ishe shi, lamarin zee ya fara gundirar sa, ganin baida wani abinyi yasa ya ciro wayar shi ya bud'o hotunan Asmah da yayi saving , ya kunna yana kallo' inya qare ya sake danna play kamar wani mara abinyi,

Zee ganin shiru shiru Aslam bai shigo ba yasa ta tashi ta biyo bayan shi don ta bashi hakuri a tunanin ta fushi yayi don ta fita ba izini , tana sakkowa falon ta hangoshi ya duqufa yana kallo a waya, baima san ta sakko ba, bi tayi ta bayanshi ta duqa don ganin me yake kallo haka,
Chapter 22 · 0% Book details