← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 126

Sashe 62

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba komai bane ya fado mata a zuciya sai cewa batool ciki gareta shi yasa taki shan juice din wata kila bata sha'awar shine, dama tun dazu take ta mata kallon tuhuma ganin yadda fuskarta da idanunta suka dan kukkumbura,(kukan data sha kafin su wuto) a zuciyar ta tace bari na kara gwada ta na gani dan na tabbatar, tace "daughter ya baki sha ba ko bakison kalan wannan dinne a chanzo miki wani kalan, akwai ma sobo mai dadi ko shi za'a kawo miki," dama batool akwai son sobo da sauri tace "to maah nagode".

Gani sukayi maah ta daga hannu sama tana cewa "Alhmdllh zargi na ya tabbata, bashir amma baka kyauta min ba dama ciki ne da batula shine baka gaya min ba, haba nidai ince naga fuskarta ya kumbura yayi danye danye kamar na mai yaron ciki Ashe kuwa shi d'inne, alhmdllh bana munyi abun kai bari na kira alhaji na gaya mai, wai masha Allah sannu kin ji batool" abinda ke fitowa daga bakin maah kenan cike da tsantsar farin ciki,.

Innalillahi batool gaba daya kunya ya gama lullubeta, ji tajeyi kamar ta nitse a kasa, tuni ta haɗe kanta da gwuiwa.

Dr bash kam tsayawa yayi kamar saƙago yana Kallon maah baki buɗe, ta dauki waya tana ta kiran mutane yan uwa da abokan arzikinta tana sanar dasu batool nada ciki, kasa hakuri yayi ganin ta gama waya da kanwarta dake bimata tana cewa yanzu kuma bari na kira yaya mustafa na gaya mai shima,shi tausayi ma ta bashi ganin yadda duk ta ruɗe, da alama dama jiraye take da samuwar cikin, dama yasan hakan zai iya faruwa yasan burin maah a kullum shine yayi aure ta samu jika daga ɓangaren shi, kusan kullum maganar ta kenan ɗaya, dalili kuwa shine maah irin matan nan ne da Allah ya zuba musu Son ƙananan yara, kamar kamar me, Amrat me bima Dr yayan ta uku, amma saiya kasance, baban yaran irin mazan nan ne masu shegen nuna iko akan yayansu, tana bala'il son yaran insunzo haka zata rasa ina ka saka ina ka ajiye dasu, sau dayawa takan bukaci abar mata yaran su kwana a wurinta ko kwana daya ne idan suna hutun school, kiri kiri zai hana yace tayi hakuri, takan ce "ku tafi da yayanku, Allah ya kyauta kuje ku dafa ku cinye , dama jikoki daga tsatson Mace ba abin dogara bane, ku zuba ido muna nan daku bashir dina zaiyi aure ya haifar min yan dagwai dagwai wadanda na isa dasu da mahaifinsu gaba daya, sai yadda nayi dasu" wannan lamari na daya daga cikin abinda yakara ma maah kwadayin samun tsatso daga bashir d'in.

Tana gama waya da yaya mustafah ta sake cewa yanzu bari na kira kawata hajiya luba na fada mata itama ta tayani murna.

Kasa hakuri Dr bash yayi ya katseta da cewa "maah wai waya gaya miki batool nada ciki" datatawa tayi daga niyyar kiran hajiya luba da tayi, dagowa tayi ta zuba mishi ido na wasu yan sakanni, kafin ta mai dakuwa tare da cewa "gidan ku bashir," zaro ido yayi yace "maah" ta katseshi da cewa "nace gidanku bashir, kana nufin kace karya nakeyi kenan ko me? Ka kalli yarinya yadda ta koma ɗanya sharaf kace wai bata da ciki, irin sakacin ku kenan yayan zamani, banda shashanci kana likita amma ka kasa gane matar ka nada juna biyu," nan fa maah ta shiga fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, fada fah sosai.

Ganin haka yasa Dr bash yace"kiyi hakuri maah nima sai yanzu da kikayi magana na kula da sawu alamomin cikin a tare da ita".

Washe baki maah tayi dama, tsoranta kar bashir yace mata ba cikin shiyasa ta fitittike tana ta fada ba gaira ba sabar, tace"ah to to madallah yanzu naji batu," juyo da kallonta tayi kan batool tare da cewa "sannu kinji batula Allah ya raba lafiya" kara kasa da kai batool tayi, ganin ta takura sosai yasa Afrah ta mikar da ita tace"antyna mu shiga daga ciki ki fada min abinda babynmu ya ke so na girka mishi" don suma su Afrah ba'a barsu a baya ba murna sukeyi jin cewa matar big bro nada ciki, dan suma kamar maah dinne wajen son kananan yara,

Suna wucewa maah ta kalli Dr bash tace "dan Allah bashir ka kulamin da yarinyar nan da abida ke cikinta, duk abida take son ji ko sha kanemo mata, kar ka barta ta dinga aiki masu wahala, saboda cikin karamine, aiki mai nauyi zai iya girgiza shi, sai kuma Abu na karshe bashir dan Allah kar kaje kata haike mata da yawa azo cikin nan ya zuɓe a rana in kayi so ɗaya ya isa shima a hankali, kana jina ko?"

Bashir kunya ne gaba daya ya gama lullubeshi, ya riga yasan halin mahaifiyar nashi haka take magana ita, bata da boye boye komai fadi takeyi abinta gaba gaɗi, saidai kai data fadawa kaji kunya.

Ranar a gidan batool ta wuni taga gata iya gata tuni ta saki jiki sosai a gidan dan samun guri harda wani shagwaba shagwaba take musu magana, sai dare suka baro gidan bayan maah ta kara tsare su na kusan 30minute tana sake jaddada ma bashir abubuwan da zai kiyaye.

Bayan wucewar su ne maah ta bude ledan tsarabar da batool ta kawo mata, "wai wai wai cancadi, wainnan tsala tsalan zannuwa da lesuka haka masu mugun kyau haka"turaren ta dauko tana dubawa, zaro ido tayi ganin irin launikan turarukan, masu mugun kamshi da tsada wa'inda ba'a koina ake samun irinsu ba a Nigeria, ledar kayan ta dauka ta duba a ina akayi wannan kayataccen siyayar haka, tana gani murmushi ta saki tare da cewa a bayyane"dama nasan saidai can inba a R & U global enterprise ba a ina za'a samu irin wadannan kaya masu kyau haka duk fadin garin nan "

A hanyar su ta komawa gida kuwa shiru yayi a motar, tunda suka taso ba Wanda yace da dan uwan shi kala, kowa da sake saken da yakeyi a zuciyar shi, Dr bashir gaba daya tausayin maah ne ya kamashi ganin yadda ta dauki son duniya ta daura ma cikin data kakaba musu, yanzu mai zai faru idan ta gane babu cikin nan, wai ranar yasan a kwai gwarama, fatan shi dai kafin lokacin su daidaita da batool, don yanzu baya tunanin za'a iya samun ciki nan kusa.

Batool kam gaba daya jikinta yayi sanyi da wannan lamari, amma fa duk da haka ba wai ta saduda bane ita dai kawai tasan ta tausayawa maah, a fili ta tace Allah sarki maah na tausaya miki, kin dauki kwanda wahala kin daura wa kanki Wanda bansan ranar da zaki sauke shiba, dan nidai da ɗanki, ba haihuwa a tsakanin mu tunda bawai son juna mukeyi ba,................

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARI NE MALLAKINA NE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌

(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira 👌 a kiyaye pls)

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiy,Allah kajiqan iyayen}

Tallah!💖 Tallah!!💖 Tallah!!!💖

Albishirinku manyan mata! ma'abota kwalliya da
_Rantsattsun lesussuka💃,
_Atamfofi manya da k'anana💃
_Galla gallan shaddodi manya da k'anana muna da su kowani iri💃
_Akwai kuma yadiddikan maza kamarsu koranza,plan yard dadai sauransu💃
_Munada mayafai, takalman maza da mata,sarqoqi, awarwaraye,da duk sauran nau'ikan kayan ado na maza da mata muna dasu 💃
Akanfaninmu na""R & U""Global Enterprise Dake Nan Garin Minna Niger State, saikunzu..........

Ga numbern mu kamar haka👇
08062160424
08066891424.....

Sayan day'a ko sari acikin farashi mai sauqi👌
Kubamu odern ku,danshine aikimmu akoda yaushe da yardar Allah........👌
Sai an gwada akansan na kwaraiiii💃💃💃.....

Page 99

Kallon ta Dr bash yayi jin abinda take cewa, wai basa son juna, juyawa yayi yaci gaba da tukin shi, a haka har suka karaso gida, yana yin parking suka fito suka nufi cikin gidan, batool ɗakin barcin su ta wuce ta rage kayan jikinta kasancewar tayi wankan ta fess a gidan maah kafin su taso, kananan kaya ta sanya Riga karami mai kyau nashan iska, pink colour, da wando legis mai kamar jeans blue colour, tayi parking gashin kanta mai tarin yawa, tayi kyau sosai dass da ita kamar yar tsana babie, takalminta na yawo a ɗaki tàsako ta ɗauko wayarta ta dawo falo ta zauna tana kallon tv.

Dr bash kam wanka ya shiga koda ya fito bata dakin, tsane jikinshi yayi , yayi shafe shafen shi wardrobe ya bude da nufin ya samu kayan shan iska ya saka shima, sai kuma idanshi ya sauka akan wani rantsasttsen suits da wani abokin karatun shi ya bashi kyuatar shi da zaiyi aure, mai mugun tsada ne dan kudin suits din zai ishi wani mara karfin zama babban attajiri a dare daya, kalan shi ash ne mai duhu, na cikin shi kuma fari, samun zuciyar shi yayi da sha'awar saka kayan dan yama batool kwalliya ya burgeta,ciro kayan yayi ya Sanya bayan ya saka inear Wear's a cikin, masha Allah kar kuso kuga Dr bash hmmm abun ba'a magana, koni kaina badan badan a kwai Abban ummeetarh ba ko hmmm bari dai nayi shiru kar batool ta jini, su rabi iyayen gulma saura kuma ki je ji gaya mata, dan nasan zaki aika.

Tsayawa yayi a gaban mirror yana kare ma kanshi kallo, shi karan kanshi yasan ya haɗu iya haɗuwa, wani irin kayataccen murmushi ya sakar ma kanshi, cumb ya dauka ya kara gyara gashin kanshi ya canza mai style take ya fito kamar wani jarumi salman khan.

Tana kwance a 3sitter tana kallon wani carton mai kyau da ake haskawa a mbc 3 batool ma badai son carton ba kamar Oum ummeetarh,bata gajiya da kallon aljanan roba, kamshin tsadaddan turaren shi ne ya mata sallama, a hankali ta lumshe idanunta tare da shakar kamshin har cikin zuciyar takejin kamshin na taɓawa.

Cike da wani irin takun cikakkun maza, ya taho bai zame ko ina ba sai gabanta yayi wani irin tsayuwa mai kayatarwa tare da saka hannayenshi a aljihu, fuskar shi dauke da kayataccen murmushi.
Chapter 62 · 0% Book details