← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 126

Sashe 81

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daga ledar tayi tana nuna musa tare da cewa"Lalalalaaa kice abin yazo inji mai tsoron wanka, masha Allah naga biyu, kice gaba nan gaba inada suyan rago kashi kashi, saura su O'o da O'o, Allah ya raba lafiyar mrs kamaludden " tuni Khadijah ta saka kanta a cikin cinyoyinta ta dunkule wuri daya, duka dariya suka saka mata, suna tsokananta ta kasa dagowa saboda ummi, ummi kam dake musu dariya ganin abin zaiyi yawa sun sakata gaba karma batool da tafi zakewa yasa tace"kyale su oh Khadijah, ai bake kadai nabe naga kema batool ai cikin ne dake ko?" da sauri batool ta dago tana kallon umminsu, zaro mata ido ummi tayi tace"eh haka nace kema cikin ne dake ko nayi karya," kasa bata amsa batool tayi, ta maida kallonta kan zahra tace "dakema zahra" aiko dai zahra tayi tsuru tsuru Ashe duk boyon banza takeyi tun ɗazu, ummi taci gaba da cewa "a toh naga gara ayi tone tonen tunda haka kuma zaɓa, ga Abu a jikinku kuma, amma kun take kun saka min ƴa a gaba" shiru kakeji batool baki ya mutu, ya Rabi'ah kam guɗa ta daddage ta rangaɗa iya karfinta, kafin tace "masha Allah alhmdllh, waiko mummy Nada wannan labarin kokuma ni zan fara mata albishir," ummi tace "ta ina zata sani nima duk yanzu na gansu da abubuwan su" ya Rabi'ah tace"to ummi banji kinyi lissafi da madam misisi ba matar oga" kallon Asmah ummi tayi tace "kai ita naga kamar babu ko?" ta fada tana kallon Asmah alamar ita take tambaya, ya Rabi'ah kuwa kallon Asmah tayi ta rike haba tare da cewa "ke ko ma'ulle me kika tsaya jira haka, ake neman a barki a baya," ummi tace "barni da ita, zata gaya min bayani ne anjima" ta faɗa tana dan haharan Asmah, Wanda ita kaɗai ta fahimci hararan me ummi ke mata, duk tasha jinin jikinta dama tun da taji kowa nada ciki banda ita jikinta yayi sanyi.

Zahra kam silalewa tayi ta shiga kitchen, ta samu abinci a nan ta zauna ta shake flate ta hau ci, koda ta fito duk sun shiga ciki don yin sallan la'asar da, aketa kira, itama cikin ta nufa, a dakin da ummi ta sauka ta samesu suna sallah.

Bayan sun idar zahra tambayar ya Rabi'ah tayi ko akwai aikin da Za'ayi ne, ya Rabi'ah tace "ba wani aiki duk ayyukan ba'anan za'àyi ba a can family hause dinsu za'ayi raɗin suna, duk abinda ya shafi raɗin sunan a cen za'ayi, ni kuma nawa abinci yourbawa zasuyi,saidai ko ku jera drinks da ruwan da aka kawo dazu a fridge kubi duka fridge din da kuka sani a gidan nan ku cikashi da ruwa da drinks harda na dakunan bakin cen dake rufe Na waje, bari Na Baku keys " ta faɗa tana mikewa ta dauko keys din a cikin side drower ta mikawa Amira, amsa tayi tace "to kumuje mu gama ko kafin fira ya barke mu kasa tashi" zahra tace "aikuwa dai muje" miƙewa sukayi zasu wuce Ummi Na zaune kan pray mat tana addu'a, gyaran murya ta musu duk suka juyo suna kallonta,nuna Asmah tayi sannan ta mata alamar ta tsaya ita, cikin sanyi jiki ta dawo ta zauna a bakin bed, gaba ɗaya walwalarta ya ragu, haka kurum takeji kamar ta aikata wani zunibi ne, ganin duk yan uwanta da aka musu aure tare suna da juna biyu amma ita har yanzu tana nan matsayin virgin bama akai ga maganar ciki ba tukunna, su batool kuwa tafiya sukayi suka kama aikin da zasuyi.

Bayan ummi ta idar ta shafa addu'an bata rai tayi sannan ta juyo ta kalli Asmah, ganin yanayin fuskar ummi saida gabanta ya faɗi, da gani tasan babu wasa a fuskarta, umminsu kenan Zuma ga zaki ga harbi, ita kuma ummi tayi haka ne dan ta samu Asmah ta faɗa mata gaskiyar abinda take son sani don idan ta sake mata fuska zata iya mata karya duk da ba halinta bane karya, zataji kunyar gaya mata wasu abubuwan idan taga dariya a fuskarta.

Cikin dakakkiyar murya tace "wato bakiji maganar dana gaya miki rannan ba ko, wai yaushe kika zama mai kunnen kashi ne Asmah, bansanki da wanna halin bafa" take idanun Asmah suka Tara kwalla, ummi bata saurareta ba taci gaba da cewa "wato ke baza'a miki magana kiji ba ko, kin tsaya shashanci da sunan baki son miji kin manta da abinda ke gabanki ko, waya gaya miki ana wannan yayin yanzu, ko mutanen da, da suke da duhun kai basuyi wannan kauyancin ba balle ku yaran yanzu da kuke a waye, Na gaya miki rannan namiji duk sonda yake ma mace idan bai samu kulawarta ba wlh soyayyar nan bacewa takeyi bat a zuciyar shi, take zakiga ya fara hangen wata, to balle naki ma da yake da wata matar a gefe, wlh idan ya gaji ajiyeki zaiyi a gefe ya dawo da matar shi, shikenan kin shiga uku, keda mijinki saidai hange daga nisa" nan fa ummi ta rufeta da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, don ita duk a tunaninta har yanzu Asmah bata ba Aslam dama bane, tunda gashi har yanzu auren nasu bai cika ba.

Tuni Asmah ta duƙar da kai kasa ta fara kuka harda sheshsheka, jikinta ya ƙara yin sanyi musamman da ummi ta tuna mata da zee, saida taji ummi tayi shiru sannan ta dago kai idanu gaja gaja da hawaye, cikin muryarta mai dauke da amon kuka tace "umminmu wallahi tallahi abinda kike tunani ba haka bane, wallahi ummi tun daga ranar da kikamin magana, komai ya fara daidaita a tsakanin mu" katseta ummi tayi da cewa "rufe min baki karya kikeyi, idan komai ya daidaita mai yasa har yanzu babu abida ya shiga tsakaninku ta fannin auratayya" cikin kuka tace "wallahi ummi ba laifina bane , ba daga gurina bane matsalar wallahi ba daga ni bane" ummi jin ta fara kamo bakin zaren yasa ta kara bata rai tace "to daga waye" ganin ba wasa a fuskar ummi yasa batayi tunanin wani batun kunya ba tace "shine bai taba nuna yanaso ya kusanceni ba" ummi cikin zaro ido jin abinda Asmah tace dan ta ji tsoro kar ace baida isashen lafiya ne tace "ban gane ba kina nufin kodan romance haka dasu dan kiss bai taba yi miki ba" Asmah tace "yana duk wannan amma bai taba wuce haka ba, koni abin Na damuna umminmu"

Gyara zama ummi tayi a bakin bed, tufka takeyi tana warwarewa,a zuciyarta, ta yarda da batun Asmah Na cewa sun daidaita, tun daga yanayin yadda Asmah keta zuba mata rantsuwa, kuma ta gamsu Aslam kalau yake tunda yana da sha'awa, tunda gashi har yana iya wasanni da ita, to daga ina matsalar take ne? Jin amsar da zuciyar ta ya bata yasa ta juyo da sauri ta kalli Asmah tare da tsatsare ta da idanunta masu kaifi a kansu tace,"ya taɓa nuna yana bukatar kusantarki koda so ɗaya ne kin hana" da sauri Asmah ta girgiza mata kai, a fili ummi tace "A'a to meke damun son ne wai" shiru tayi ta dafe kai, cen kuma tace "to ko yana nufin cewa ke zaki fara neman shi" shiru Asmah tayi don bata San amsar da zata bata ba, ganin bata bata amsa ba hakan ya tabbatar mata da cewa bata San amsar da zata bata bane, tace "aiko dai idan ma hakan yake nufi to kuwa yayi wauta dan kuwa hakan bazai taba saɓuwa ba wai bindiga a ruwa inji hausawa, dole shizai fara nemanki don wannan ba tarbiyar mu ta Mallam bahaushe bane, sai kace wasu ƙabilu,zamuyi maganin shi, inyasan wata ai baisan wata ba"
Chapter 81 · 0% Book details