Sashe 113
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hira suka shiga yi kamar yadda suka saba, fuskar kowacce su a sake, sai dai fa a karkashin zuciyoyin su kowacce da abin da take ji game da yar uwar ta, tana sane tayi banza da shi ta share shi bata je gare shi ba, shikuma yana can yana ta faman jiran ta, ganin bata da niyar zuwa yasa ya lalubi number ta ya kira, wayar ta dake kan hannun kujeran da zee ke zaune ne ya fara kiɗa, da jin ringing din tasan shine domin kuwa ringing ɗin shi na musamman ne a awayar ta,dukan su kallon wayar suka yi zee da yake tafi kusa da wayar yasa idanun sa suka sauka akan sunan da ta saka mishi, honey boo💕 sai da gaban ta ya ɗan faɗi amma a fuskar ta bata nuna komai ba sai ma murmushi da ta sake tare da cewa "kaiii! anty Asmah kin share honey boo ɗin ki gashi ya gaji da jira yana kira fa." Ta faɗa tana miki mata wayar, kamar kar ta karɓa amma ta daure ta karɓan tare da ɗagawa ta kara a kunne "ki same ni a ɗaki na." Shine kawai abin da ya faɗa a dake dan karma ta kawo mai wargi, kallon juna suka yi da zee suka sakar wa juna murmushi "Bari na tafi tun kan oga yazo yayi ƙasa ƙasa dani, yace ni ce na tsare mishi ke." Hararan wasa Asmah ta mata tare da cewa "kaji anty zee dai da wani zance." Cikin dariya tace "wani zance ko gaskiya." Miƙa wa little hannu tayi alamar yazo suje cikin sa'a kuwa ya je gare ta alamar zai bita, daukar shi tayi sukayi hanyar ƙofa tana cewa "to anty Asmah bari naje na ɗan kwanta wlh barci nake ji sai anjima." Bada wani manufa ta fadi wannan maganar ba har ga Allah, don da tasan yadda Asmah zata fassara shi da bata fada ba,Kamar saukar aradu haka maganar zee ya doki zuciyar ta, take jikin ta yayi wani irin sanyi kalau kasa tashi tayi ta mata rakiya kamar yadda ta saba, me take nufi da zata dan kwanta barci ma take ji? Zuciyar ta ta bata amsa da cewa jiya da dare bata samu barci ba kenan suna tare da ya Aslam ɗin ki yana mata abin da yake miki, hawayen tausayin kanta ne suka ziraro mata, shike nan yau ya tabbata ta raba Aslam din ta da wata macen duniya abinda in da wani ne ya bata labarin cewa nan gaba zai faru har tayi karfin halin iya jurewa baza ta taba yarda ba, ringing ɗin da wayar ta ya sake yi ne ya dawo da ita hayyacin ta, da sauri ta shiga share hawayen ta tare da daidai ta fuskar ta don kar ya gane halin da take ciki. Sallama ta yi a bakin kofar dakin , amsa mata ya yi daga ciki, hakan ya sa ta shiga abin ta kai tsaye tare da mai da ƙofar ta rufe, ɗakin babu wadataccen haske, ware idanun ta ta shiga yi tana neman ta inda zata hango shi, duk hange hangen ta bata hango shi ba, kiran sunan shi ta shiga yi , amma shiru ba amsa, take mamaki da tsoro suka bayyana a fuskar ta, kofar toilet tayi da nufin ta duba ko yana nan, nan ma dai bai nan,mamakin ta ne ya ninku da sauri ta nufi haryar ƙofar fita dan ta fara tsorata tun da dai ita tabbas taji muryar shi a ɗakin ya amsa mata sallama, tsam taji ya rungume ta ta baya ya kwantar da kanshi akan dokin wuyan ta, ajiyar zuciya suka shiga sauke wa a tare cikin wani irin kasallalliyar murya yace "nayi missing ɗin ki sosai husnah ta." Bata tanka shi ba dan haka kawai zuciyar ta kece mata karya ya ke yi ba wani missing ɗin ki da yayi, jin tayi shiru yasa ya juyo da ita da sauri, ta gaban shi tare da cewa "ke bakiyi kewa ta ba ko husnah ta." A maimakon ta tanka sai hawaye sharrr "subhanallahi, dan girman Allah ki bari, wanda kika yi jiya da dare ma ya isa haka." Ya faɗa tare da mika yatsa yama share hawayen dake zubowa, amma ina yana share wa wasu na zubowa kamar an kunna famfo, ganin haka yasa ya nufi bed da ita ya kwantar, tare da saka harshen shi yana tsotse hawayen dake zubowa, sai da ta gaji dan kanta ta bar kukan jin haka yasa ya mai da akalar tsotsar shi kan bakin ta, lukuss tayi tana karban sakonnin shi, tun daga kan kumatun ta zuwa wuyar ta yake tsotse wa yana hura mata iska a kunne cikin ƙwarewa ganin yadda tayi lukuss yasa a hankali ya raɗa mata "shine jiya Bayan na wuce kike ta kuka ko? Kuma da safe da kika gan ni kika share ni kamar baki gan ni ba ko, kika barni ina ta jiran ki, cikin shehsheka me haɗe da shagwaba tace "ba Kaine ba jiya ka kwana gurin anty zee shine kuma da safe ba kazo da wuri na gan ka ba kuma kasan da kewar ka na kwana da'ker barci ya dauke ni." Yace "innalillahi dan Allah kiyi hakuri my hussy daga yau bazan sake zuwa wani waje kwana ba, tare zamu ringa kwana abin mu kamar yadda muka saba." Tace "nifa ban ce ba kawai cewa nayi baka zo da wuri ba da safe ka barni ina ta kewar ka." Yadda take maganar cike da shagwaba da salon jan hankali yasa yaji gaba daya hankalin shi na tashi wani irin sha'awar ta na bijiro mishi, hannu ya miƙa a hankali ya shiga laluɓe ta, jin yana shirin wuce gona da iri yasa tayi sauri damke hannun shi kallon ta yayi da idanun shi da suka fara juyewa cike da sha'awa, girgiza mai kai tayi , a hankili tace "yau fa ba kwana na bane kwanan anty zee ne." kamar ta caka mishi wuka haka yaji maganar ta ta daki zuciyar shi, cikin zaro ido yace "waye ya gaya miki kwanan ta ne yau." Tace "ba sai an gaya min ba, kwana 2-2 zamu din ga yi kayi daya saura da..." Bai bari ta kara sa ba ya katse ta da ɗan ƙarfi "ban amince ba ni kwana 1-1 zaku ringa yi nama riga na sanar mata, dan bazan iya jure yin har kwana biyu ba tare da ke ba." Tace "saboda me naga duk abin da zaka samu gare ni zaka same shi gurin anty zee har ma fiye da yadda zaka samu gare ni." Numfashi ya sauke "hmmm baza ki gane bane husnah ta." Mika ɗayan hannun yayi da nufin ya ci gaba da abin da yake so , sake rike dayan hannun tayi tare da cewa "to ai ba yanzu zan karɓe ka ba sai dare, har yanzu kana dakin ta ne, idan kana da bukatuwa ne kaje gare ta dan Allah." Kwace hannun shi yayi ya tashi yazauna bakin bed tare da dafe kai, ganin haka yasa ta dauka ko fushi yayi, hankalin ta yaɗan tashi, amma a ranta ta ayyana, wlh bazan baka daman da zaka faɗa halaka ba, in sha Allah bazan zama silar da zaka tashi da barin jiki a shanye ba ranar alkiyama kamar yadda mata da yawa a zamanin nan suke yi suna sane miji ba daidai yake aikatawa ba amma baza su taba hana shi ba su a ganin su hakan so ne, to wlh cuta ne tunde kema da aka haɗa kai dake aka zalinci wata Allah bazai barki haka ba.
Daga bayan shi ta tsaya ta fara shehshekan kuka irin wanda tasan zai tada mishi hankali, ai kuwa a sukwane ya juyo ya jawo ta ya shiga rarrashi, cikin shehsheka tace "dan Allah kar kayi fushi dani ya Aslam, wlh ba wai na hana ka kaina da gangan bane, idan na bari ka aikata hakan mun shiga hakkin anty zee kuma Allah bazai barmu ba,bana son ka zama mara adalci a tsananin mu tun kafin tafiyar tayi nisa." Tana maganar tana kara matsar kwallah, take yaji babu dadi a zuciyar shi cikin muryar rarrashin yace "ya isa haka my hussy, na fahimce ki, kuma in sha Allah zan dage sosai nayi abin da kike nusar dani, ke ta dabam ce a cikin mata husnah ta, Allah ubangiji ya miki albarka." Rungume shi tayi sosai ta kwantar da kanta a jikin shi.
A part ɗin ta yayi shirin zuwa aiki tunda a nan kayan shi suke, har falo ta rako shi tana rike da jakar laptop din shi, a falo ta mika mishi ba yadda baiyi ba ta raka shi wurin mota ta ki, a cewar ta zee zata hango su kuma baza taji dadi ba tun da ba kwanan ta bane, sai da ya biya part din zee ya sallame ta ita ma sannan ya dauki hanya.
Daga bayan shi ta tsaya ta fara shehshekan kuka irin wanda tasan zai tada mishi hankali, ai kuwa a sukwane ya juyo ya jawo ta ya shiga rarrashi, cikin shehsheka tace "dan Allah kar kayi fushi dani ya Aslam, wlh ba wai na hana ka kaina da gangan bane, idan na bari ka aikata hakan mun shiga hakkin anty zee kuma Allah bazai barmu ba,bana son ka zama mara adalci a tsananin mu tun kafin tafiyar tayi nisa." Tana maganar tana kara matsar kwallah, take yaji babu dadi a zuciyar shi cikin muryar rarrashin yace "ya isa haka my hussy, na fahimce ki, kuma in sha Allah zan dage sosai nayi abin da kike nusar dani, ke ta dabam ce a cikin mata husnah ta, Allah ubangiji ya miki albarka." Rungume shi tayi sosai ta kwantar da kanta a jikin shi.
A part ɗin ta yayi shirin zuwa aiki tunda a nan kayan shi suke, har falo ta rako shi tana rike da jakar laptop din shi, a falo ta mika mishi ba yadda baiyi ba ta raka shi wurin mota ta ki, a cewar ta zee zata hango su kuma baza taji dadi ba tun da ba kwanan ta bane, sai da ya biya part din zee ya sallame ta ita ma sannan ya dauki hanya.