← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 126

Sashe 109

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A bangaren Aslam da Asmah kam yau suma haka suka kwana, kadaran kadahan, duk da Aslam yayi iya yin shi dan ganin ta saki ranta amma abin ya gagara, ya mata uziri yana ta binta yadda taso, har zuwa safiya bata cikin walwala, ganin yadda duk yabi ya damu sai wani lallaɓa ta yake yi, yasa taji ya bata tausayi dole ta aro walwalan karya ta yafa wa kanta, idan yayi wani abin dan ya saka ta dariya tayi murmushin yaƙe, hakan kuwa ya mai daɗi ganini haka ya samu karfin halin fita office duk da bai daɗe ba sha biyu ya dawo.

A haka suka kwashe kwana uku, zuwa lokacin Asmah ta sake sosai ganin ko kaɗan Aslam bai canza mata ba sai ma wani ƙarin kulawa da tattali na musamman da yake nuna mata, tuni ta ajiye batun wani kishi da wata zee suka bude sabon shafin soyayya, kuma har tsawon wannan kwanakin daga ita har Aslam din babu wanda ya saka zee da little a idanun shi, Asmah tana sane da hakan don lokaci lokaci sukan faɗo mata a rai, sai dai tana tsoron ta saka musu baki dan tana gani wannan tsakanin su ne matsalar su ce su ta shafa, kullum Aslam na part ɗinta bai taba cewa zaije wajen su ba, yadda ma yake yi kamar ya manta da wasu halitta a gidan, itama bata ce yaje ba, sai dai fa a can ƙasan zuciyoyin su tunani da kewar little ya hana su sakat, so ɗaya ta taɓa saka yaron a idanun ta amma ya kama zuciyar ta fiyye da yadda bata yi zato ba, shima Aslam ɗin haka kullum da tunanin yaron yake kwana yake wuni sai dai yaki zuwa gareshi saboda wani dalili da shi kadai ya bar wa kan shi sani, amma fa daure wa kawai yake yi. A bangaren zee kam duk fitar shi da shigar shi akan idanun ta, takan kwana kuka kamar hawayen ta zasu kare, little yayi ta rarrashin ta idan taki yin shiru shima sai ya fashe da kuka, daga karshe ta yanke shawaran da take ganin shine zai ɓullar da ita kan hanya, zatayi amfani da nata kalar hikimar ta karkato da hankalin mijin ta gare ta, bada tsiya koda tashin hankali ba, domin idan wannan tace zata yi a halin yanzu ita ce baza taci riba ba, dan ta riga ta sadakar Asmah ta sha gaban ta, ta ko wanne fanni.

Yau da ta kama kwana biyar da dawowar ta gidan komai na ɗan kayan abincin da ta aiki megadi ya siyo mata sun kare hakan ya saka bayan tayi wanka sun karya ita da little ta laɓe a abakin window kamar yadda ta saba, tana kallo har Aslam ya bar gidan, yana fita kuwa ta zaro galenta ta riko hannun ɗanta suka fito so take ta sake aikar megadi ya kara siyo mata kayan abinci. Daidai sunzo kofar part din Asmah, ita kuma ta buɗe kafar ta fito hannun ta dauke da kwandon shara da alama shiya fito da ita dan ta juye a babban drum dake waje, turuss suka ja birki dukan su suna bin juna da kallo, zee ce tace ta kawar da kallon ta hanyar sakar mata wani irin kyakkyawan murmushi, tana ƙarasowa wajen ta tace "manya idanun ku kenan, kun shige ciki shiru ba ajin ko motsin ku, to yau dai gashi mun haɗu ina kwana ya gajiya ya zaman shiru." Sororo ta tsaya can kuma ita ma
ta sakar mata murmushin yaƙe tace "ina kwana." Kama basken ɗin sharan zee tayi tace bari na taya ki zubar wa, saboda tsabar mamaki bata San ta sakar mata kwandon ba. Zee na tafiya ta mai da idon ta kan little da ke tsaye yana kallon ta, wani irin sanyi taji a zuciyar ta ta wahalu da kewar yaron, tsugunawa tayi ta maida tsawan ta dai dai nashi tace " zo my boy." Ta faɗa tana mika mishi hannu, sai da ya kare mata kallo sannan a hankali ya isa gare ta samun kanta tayi da saka shi a jikin ta ta rungume tsam, tana sauke ajiyar zuciya, zee data gama juye sharan kamar ance ta juyo, idanunta ya sauka akan abin da ke faruwa, da sauri ta dauke kanta tana sakin murmushi, abin ya burge ta lallai yarinyar bata da damuwa da alama. Gurin megadi ta ƙarasa ta bashi saƙon daya fito da ita koda ta juyo samun su tayi a gurin suna fira little sai dariya yake yi ko me take ce mishi oho. Tana isowa tace "iyyee mummy and son anata fira to me ake cewa nima a gaya min." Dagowa tayi wannan karon da murmushi gaske bana yaƙe ba ta kalle ta, taji daɗin yadda zee ta kira ta da sunan mummyn yaron, tace "sannu anty zee nagode." Zee tace."Ba komai anty Asmah." Sai kawai suka kwashe da dariya kamar sun saba da juna, zee tace "bari mu karasa ciki." Ta faɗa tana kamo hannun little maƙe kàfada yayi tare da lafewa a jikin Asmah duk dariya suka suka mai zee tace"iyee lallai yaro yaga mummyn shi na asali, to bari na barka a gurin ta zuwa anjima." Ta fada tana kallon Asmah, cikin jin dadi Asmah tace "ai kuwa nagode na samu dan taya hira." Cikin dariya zee tace "kin samu dan saka surutu dai." Kallon shi tayi tace "wai haka my son." Make kafaɗa yayi, zee tace "ai dama bazai ce eh ba sai kunje zaki gane nufi na, nidai nayi nan." Ta fada tana wucewa part din ta, Asmah ma daukar shi tayi suka shige nata part din.

Ranar tayi wunin farin ciki sai wasa take mai ta dafa mai indomie ta bashi a baki ta bashi wannan ta bashi wancen karshe har ya gaji yayi barci ta kaishi dakin ta ta kwantar, har yamma yana gurin ta, gashi ranar Aslam bai dawo da wuri ba, dan tun 2 take ta zuba ido shiru, wanka ta mishi itama tayi da yamma taci kwalliyar ta bata da kayan yara don haka tace bari taje ta amso gurin zee, koda ta fito falo ta samu ana knocking da sauri ta karasa ta bude duk a tunanin ta Aslam ne duk da bata ji diran motar shi ba, sai dai ga mamakin ta zee ta gani a bakin kofar murmushi suka sakar wa juna, Asmah tace "laa anty zee dama gurin ki nake shirin zuwa yanzu na amsar wa my son kaya sai kuma gaki shigo daga ciki mana kin tsaya a waje." Ta fada tana kauce wa ta bata hanya, zee tace "A'a anty Asmah ba sai na shigo ba naga yamma yayi nace bari na zo na dauke shi, Allah yasa dai bai miki rigima ba." "Ba wani rigiman da yayi min wasan shi ya dinga yi, yaron yana da saurin sabo ai." "Hmmm make dai kawai yayi ma haka, nima nayi mamaki sosai yadda ya aminta da ke lokaci daya yaron dake da shegen kyuyan tsiya." Murmushi tayi tace"Ki shigo mana anty zee." Zee tace "kin dai dage kar mai gidan yazo ya same ni." Dariya ta kwashe dashi tace "kaji anty zee dai to sai me idan ya ganki a nan ɗin ai abin da yayi kara shi yayi ciyawa."

Zama tayi tana ƙarewa falon Asmah kallo, masha Allah komai yaji dan babu abin da nata zai nuna ma wannan ɗin ita sai take ga kamar wannan ɗin ma yafi nata tsaruwa, ruwa da darinks ta gabatar mata, sannan ta zo ta zauna, kan kace kobo fira ya barke a tsakanin su, kamar wasu wadan da suka daɗe da sanin juna, duk rabin firan dai a kan little ne, hankalin su ya tafi har basu ji Duran motar Aslam ba sai karan doorbell suka ji, gaban zee ne ya yanke ya fadi, take ta zazzaro ido waje kamar wata mara gaskiya, yayin da Asmah ta saki wani kayataccen murmushi, mikewa tayi da sauri ta nufi kofar fuskar ta dauke da madaukakin farin ciki. Tana bude kofar ya shigo baiko lura da su zee ba ya jawota ya rungume, lumshe idanu yayi yana sauke ajiyar zuciya kicin kicin kwacewar data shiga yi ne yasa shi saurin bude ido jin wani sabon abu yau, kasancewar shike facing cikin falon hakan yasa idanun shi suka sauka akan little kafin ya gama tunanin wani abu kuma ya hango zee zaune tayi kasa da kanta, sake ta yayi tare da hade rai yayi kicin kicin kamar bai taba dariya ba, duk walwala da anashuwar daya shigo dashi kan fuskarta shi take ta bace fat, ita kanta Asmah sai da ta firgita gani yadda ya juye lokaci guda, raɓa ta yayi ya haye sama abin shi ya bar ta anan sake da baki.
Chapter 109 · 0% Book details