Sashe 59
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gabanta ya tsaya ya nuna ta da yatsa ciki kausassar murya mai cike da amon bacin rai, yace "maryama! na baki nan da 10 minutes ki tattara kibar min gidana ki je gida ki koyo hankali saina nameki, karki kuskura na dawo gidan nan na tarad dake , idan kuma hakan ta faru na rantse miki da Allah na lahira saiya fiki jin dadi," dawo da kallonshi yayi kan atika yace "ke kuma shari'a daga nan har kotun koli nidake ,saikin gayamin dalilin da yasa kika bi matata har cikin dakin ta kika daketa, saina sa an daureki dan ubanki, inga uban daya daure miki gindi a Niger state" fuuu ya juya ya fita yana huci kamar wani mayun wacin zaki.
Jin tashin motar shi yasa farida fitowa daga maboyarta tana zazzare ido kamar na ƙwaɗi, cikin yarfe hannaye take cewa "mun shiga uku yaya Maryama yanzu ya zamuyi yace minti goma ya bamu" atika cikin muryar kuka tace "dan Allah Maryama ki tashi mu tafi karki bari mahaukacin mijin nan baki ya dawo ya taradda mu a gidan nan, na tabbata kashemu zaiyi har lahira" Maryama cikin wahalallalliyar murya take cewa"bazan iya tashi ba atika ya karya mun kafa ya gama dani" jin haka yasa farida cewa"bari na taro mana napep ko kama kama muyi dake yaya kibar gidan nan, shawaran da zan baki kenan, kar kice zakiyi taurin kai ki tsaya kin dai ji abinda yace" fice wa tayi a guje ta nufi get ta fece kiran napep, cikin sa'a tana fita babu bata lokaci ta samu, har cikin harabar gidan ta shigo da napep d'in tara in tara sukayi da maryama suka kawota napep d'in kafa yai tsami bai takuwa atika kam tuni baki yayi sintumtum, amma ita a yanzu wannan bai dameta ba burinta taga tabar gidan kan Barr ya dawo, har farida zata shiga napep d'in ta tsinci muryar Maryama a wahalce tana cewa"farida yarana wlh bazan bar ma maƙiyata ƴaƴana ba ki kwaso su dasu zan tafi," farida tace"kedai anty ki barsu daga baya kyau dawo ki kwashe su,kar yaya Adam ya dawo wlh a tsorace nake kar nima na samu rabona, ke ƙafa atika baki kila ni kuma ido zai ƙwaƙwulemin" ciki zafin ciwo maryama tace"dan uban ki farida ki kwaso min yarana nace" jin haka yasa farida kwasa da gudu part din maryama , a falo ta same su a rakuɓe abun tausayi hanan ta hada Kansu sun dunƙule waje daya sai kuka sukeyi, cikin tsawa farida tace"hanan tashi dan ubanki ki hado kan kannenki mu tafi" hanan cikin muryar kuka tace "anty farida ina zamu tafi" "tsaya kina tambayata karki taso dai" "anty gsky mu baza muje ko ina ba daddyn mu yace mu jira shi yana zuwa yanzu" bata tsaya jin karshen zancen ba ta finciko Ahmad da anisa, ta kama Jan hannunsu zatayi waje dasu, take hanan da suhail suka bita suna jan yan uwansu, kin sakesu tayi a haka suka fito har coumpound d'in gidan daidai nan kuma motar Barr ya shigo gidan.
Gaba dayan su saida hantar cikin su ta kada, atika hannu ta daura aka tace"mun shiga uku yau shikenan mun mutu sai gawa, mai napep dan Muhammadu rasulullahi kaja mu tafi" mai napep kam dayake irina na ne akwai son ganin kwan zomo gyara zama yayi abinshi zai ba ido hakkinsa😅.
farida kam saida fitsari ya fara kufce mata a wando tsabar razana.
Parking yayi ya fito a fusace hango yadda farida ke jamai ƴaƴa kamar wasu ukuyoyi, gadan gadan ita ya nufa.
(dama dazu bai samu ya sassaɓeta ba ita😁)
Ganin haka yasa ta saki hannun yaran ta fara ja da bawa, tana matsawa yana matsota saida suka ƙule a bango,kafa mata idanunshi da suka rine sukayi jajur yayi kafin cikin razananniyar murya mai firgitarwa, "ina zaki kaimin ƴaƴana" shiru tayi tana kara mannewa da bango kamar zatabi ta cikin bangon ta wuce, gani taki bashi amsa yasa ranshi ya kara ɓaci ware hannu yayi ya wanka mata mari, sannan cikin daka tsawa ya kara cewa"nace ina zaki kaimun ƴaƴana" still shiru kara kai mata wani Marin yayi Wanda yafi na farkon gigi tata, take ta saki sauran fitsarin da ya fara kufce mata ɗazu, ganin ta kara mai shiru yasa ya kara kai mata wani, tare da cewa cikin tsawa "baza kiyi magana ina zaki kaisu nace" tuni nunfashin farida ya fara sizing, bai damu ba kara kai mata wani marin yayi saidai yanzu kafin ya sauka a fuskarta yaji an cebe mai hannu ta baya, ganin haka yasa farida kwasa da mugun gudu ta nufi napep d'in su, tana shiga atika tace "dan kutumar uban ka mai napep kaja mu tafi, kar ya juyi kanmu wlh baida hankali idan yazo nan har kai zai hada" jin baida hankali yasa mai napep , shiga taitayin shi, ya tada napep din suka bar gidan, dan shima yaga alamar mutumin kamar baya cikin hayyacinsa.
Kallon kanin shi Dr Ali daya rike mai hannu yayi, girgiza mai kai Dr yayi yace"ya isa haka yaya kayi hakuri" bai iya amsawa Ali ba sai idanshi daya mayar kansu hanan dake ta faman risgan kuka , kamo su yayi ya rungume,yana sauke ajiyar zuciya ya dade a haka kafin suka dunguma zuwa part din zahra, har dakinta suka shiga dukkan su har Dr dan kuwa shakikin shi ne, koma ba wannan ba lafiya ya wuce wasa.
Tana kwance yadda ya kwantar da ita, hawaye na zuba a idanunta wani kan wani, abin tausayi, duk hayaniyar da akeyi a kunnenta , saidai bata jin zata iya motsa koda dan yatsa a halin da take ciki.
Cike da tausaya wa Ali yace"sannu anty zahra" jin haka yasa hanan itama tace"sorry anty zahra" su Ahmad ma suka dauka, karfin gudun hawayenta ne ya karu, Barr kam gaba daya tausayin ta ya gama cika shi saida ya fakaici idanun su ma ya share hawaye, yanzu duk akan shine zahra ta shiga wannan halin, ya rabota da garinta ya kawota inda bata da kowa sai Allah sai shi, gashi kuma ya kasa kareta daga shiga irin wannan yanayin gaba daya sai ya dauki laifin ya daura ma kanshi.
Cikin sanyin murya yace "kiyi hakuri faɗima, duk abinda ya faru lefi nane, amma na miki alkawarin zanyiwar tufkar hanci, Abu makamancin hakan bazai kara faruwa ba, ga Ali nan zai duba ki"wani kallo tabi shi da shi Wanda mai wuyar fassaruwa Wanda ita kadai tasan ma'anar kayanta.
Dubata Dr Ali yayi kuma alhmdllh ba wani babban Marsala saidai tsamin jiki, nan ya rubuta mata maganin da zai warwrar mata dashi, yace tayi wanka da ruwan dumi sosai zuwa gobe zataji garau.
Ranar kwana sukayi Barr yana jigilar kula da ita motsi kwakwkwara tayi saiya taso a zabure yana mata sannu, har saida ya far ba zahra tausayi, ta tabbatar ba karamin so Barr yake mata ba, abinci abaki ya dinga bata wanka ma shiyaso yi mata amma taki yarda badon yaso ba ya kyaleta ganin ta dage, dakin dake kusa da nata ya nuna masu hanan a kwai makeken bed a cikin dakin,kai suka hau suka kwanta ita da yan kannenta, bayan ya musu takeaway sunci sunyi nak, dan ya hana zahra shiga kitchen duk da taso tayi musu ko jellop din spaghetti ne ya hana.
Kwanan ta biyu ta ware ta dawo daidai kamar ba abinda ya faru, su hanan kuwa a iya kwanaki biyu dinnan sunyi wani irin mugun sabawa da ita saboda sakewar da tayi da su da yadda take mu'amalantar su ko mummyn su bata masu haka, ba wanda ya tuna da wata maryama a cikin su sai Ahmad da yake shi karamine, yakan ambaceta jefi jefi, dan yanzu yadda ya saki jiki da zahra ko maman shi bai saki jiki da ita haka ba, bacci kawai ke rabasu, shima a jikinta yake yi, idan yayi nisa take daukar sa ta kaishi dakin su da aka ware musu shida yan uwan shi, tamaso ya dinga kwana a wurin ta Barr ya hana.
Tsakanin ta da barrister kuwa yanzu duniya sabuwa, soyyaya suke sha na bugawa a jarida, ya sangartata sosai da salon shi, gaba daya ta gama mika wuya, shi karan kanshi ya lura da haka, amma ya bari ta kara warware da kyau, duk da ta gaya mai ta warware sosai, shi karan kanshi a matukar takure yake, dan wasannin basa mishi, amma haka yake daurewa, don gani yake yi har yanzu bata gama warware ba.
Maryama kam mai napep bai dire su ko inaba sai kofar wani karamin gida , a wani unguwa na yaku bayi, yana tsayawa suka sauka ita da farida, atika kam cewa tayi mai napep ya kaita general hospital, ko kallon su Maryama batayi ba mai napep yaja suka wuce.