← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 126

Sashe 123

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan taron suna ya watse baƙi na nesa dana kusa kowa ya koma gida lafiya, a nan family hause Asmah da babies ɗin ta suka ci gaba da zaman jego, basu canza wa yaran wani suna ba da sunan da suke kiran iyayen nasu suke kiran su, wato Mummy, Mami da Ummi. Suna samun kula sosai ta ko wane bangare,kafin arba'in yaran sun murmure sun murtuka wani uban ƙiba dumi dumi dasu gwanin sha'awa idan ka gansu zaka rantse yan 3 month ne, haka itama Asmah tayi wani irin kyau sahihi fatar ta ya ƙara haske da gogewa kamar wata balarabiyar masar idan ka ganta baza ka zata ma tayi aure ba balle har ta haifi ƴaƴa har uku , gyara take samu na musamman daga gurin mummy, abin ba'a cewa komai, tunda jini ya dauke mummy bata tsaya wata wata ba ta shiga gyara parta ciki da bai gyara kuwa bana wasa ba, a cewar ta wai tana da kishiya, dole sai ta tashi tsaye sosai akanta dan bata so ta zama bora a gurin miji, hankalin kwance take jegon ta don yaran kwata kwata basu da rigima madara suke sha basu damu da su sha nono ba, itama bata basu sai taga ya cika yana zuba ko ya fara mata ciwo sannan take basu, ko kuma mummy ta takura mata, Aslam kuwa ya zama abin tausayi kullum kafar shi na gidan ba dare ba rana, duk safiyar duniya sai yazo ya duba su kafin ya tafi aiki, haka ma da yamma idan ya dawo yaje gida ya huta zai sake dawowa tare da little dan shima yaron shegen kulaficin yaran gareshi, sai dare zai tafi,haka zai tasa yaran a gaba ya dauki wannan ya ajiye ya dauki wannan, tsakanin shi da Asmah kuwa sai gani sai hange, gaisuwa kadai ke hadasu, dan mummy ta kasa komai ta tsare idan sunyi doguwar fira to a waya ya kiranta, ba karamin wahaluwa yakeyi da rashin ta ba, duk da ga zee a gefen shi amma baya jin zata iya kashe mishi kishin Asmah, yana maneji sosai da ita yana rage zafi amma fa baya samun yadda yake so ko kaɗan, zee daidai da fruits bata san ta sha da sunan gyara ba, haka nan take kara zube, wai dan ma ana cin me kyau a sha mai kyau kenan da ba'asan ya abin zai kaya ba, kullum cikin lissafin kwanakin dawowar Asmah yake yi, ranar da suka cika kwana talatin da tara a gareshi kamar jajibarin karamar sallah haka yake ji, tuni ya saka an gyara mata part din ta tsab an share ko'ina an kyalkyale sai kamshi da sheki ke tashi, ya ware dakuna biyu ya gyara wa babies, daya an shakare musu shi da kayan wasa da kayan karatu da duk wani tarkace na yara,dayan kuma ya saka musu saitin baby beds da wardrobes har guda uku masu mugun kyau da tsada, ba karamin kudi ya narkar wa yaran nan ba dan harta kayan sawan su sai da ya ciccika musu wardrobes dinsu da shi , washe gari kuwa cike da zumuli ya farkar, tun da sassafe yaje gidan yana sauraren yaji Mummy tace yaje ya dawo ya dauke su shiru bata ce ba har lokacin tafiya aikin shi yayi, jiki a sanyaye ya tafi, ranar daga gurin aiki baije gida ba still nan ya dawo amma har yamma bata ce mai komai ba bai ma ga alamar ana wani shirin tafiyar su ba, haka ya karaci wunin shi a gidan har zuwa dare ba wani alamu, da zai tafi sau biyu yana ma mummy sallama tana cewa a gaida mutanen gida, karshe dai ya gaza hakuri yayi, yaga gara yaje ya tunawa mummy yau ne fa arba'in ɗin koda da wayau ne basai ya fito fili ba, har yakai bakin kofa ya dawo yana sose keya yace "mummy nace ba sai an turo kowa dan gyara ɗakin nata ba nasa duk an share an gyara mata shi tun jiya tunda naga yau ne zasu cika arba'in din." Hararan shi Mummy tayi tace "Waya saka? Da wa kukayi in suka yi kwana arba'in zasu dawo, to bari kaji bazan baka ƴata da kananan yara da basuyi kwari ba har uku, sai sunyi kara kwana biyu zasu dawo zuwa lokacin yaran sun yi kwari sosai." Ji yayi kamar mummy ta kwada mai guduma a kai,tsura mata idanu yayi kamar ranar ya fara ganin ta, harara ta kara watsa mai tace "meye kake kallo na kamar wata sabuwar halitta in kana da magana ne kayi ina jinka." Da sauri ya girgiza kai tare da cewa "ba komai mummy." Tace "to oya a gaida gida." Jiki a sanyaye ya fice, tun daga ranar yake ta zuba ido mummy tace ga ranar da zasu dawo shiru shiru har suna neman kwashe wata biyu, zuwa yayi ya samu Abba ya gaya mai, Asma'u tayi arba'in tun tuni mummy ta hana ta dawowa wai sai yara sunyi kwari, dariya Abba yayi yace "yanzu dai ƙaran mummy ka kawo min kenan ko? Kawai ka fito fili kace mummy ta rike maka mata." Zaro ido yayi tare da cewa "A'a Abba wlh ba haka nake nufi." Cikin dariya Abba yace "ɗan nema bari zan samu daddyn ka da maganar in sha Allah za'asan abin yi." Da taimakon Abba da daddy aka samu mummy da'ker ta bari Asmah ta koma ɗakin ta, ba haka taso ba taso ne sai sunyi wata uku cur sannan su koma, itama Asmah a nata ɓangaren kewan mijin ta take amma ko shi bata taba nunawa ba bare kuma mummy. Saka ranar komawar mummy tayi jibi, Aslam kamar ya taka rawa dan murna sai wani rawan jiki yake yi magana daya biyu Asmah, motsi kaɗan Asmah har sai da zee taji abin ya sosa mata zuciya, a cikin satin babu abinda Asmah take sai kai ziyara gidajen yan uwa, da abokan arziki, har gidan su batool da Khadijah da Amira duk taje, Allah sarki zahra ita kadai ce bata kusa. Ranar da mummy ta saka zasu dawo da sassafe yaje gidan wai yazo daukar su, mummy tace yaje ya dawo sai da daddare kamar yayi kuka, fushi yayi ya tafi yana surutai a zuciyar shi, harda su rantsuwa in suka koma basu ƙara zuwa gidan sai bayan wata biyar. Ko kafin ya dawo da daddare sun gama shirin su tsab shi kadai suke jira, ana isha'e kuwa sai gashi, already ta riga tayi sallama da kowa na gidan su Mami da Abba, hajiya mama Alhaji baba daddy duka ba wanda bata sallama ba, yana zuwa kawai da mummy suka ƙara sallama ya dauki mummy karama ita kuma ta goya Ummi ta dauki Mami a hannu suka tafi, suna isa zee tazo ta tarbe su da murnanr ta suka rungume juna cikin farin ciki gaskiya tayi kewar Asmah abokiyar zama ta gari, duk da kishin da ke dankare a ranta hakan bai hanata nuna mata zallar farin cikin ta da dawowar ta ba. Har part din ta, ta raka ta tana dauke da ummi data sauke daga bayan ta, little sai tsalle yake yi yana murna mummyn shi da ƙannen shi sun dawo, rungume shi tayi itama tana karajin son yaron a ranta duk da ta haifi nata ko kaɗan son da take ma yaron bai ragu a zuciyar ta ba sai ma karuwa da yayi, saboda yadda yake nuna son nata ƴaƴan shima, basu wani zaunar ba zee ta kama hannun little tace su tafi sai da safe yaron harda kuka Asmah tace " ki barshi mana anty zee yaro da ɗakin mummyn shi." Zee tace "ba yau ba anty Asmah sai kin gama cin amarci." Ta karashe zancen cikin zaulaya da ɗan murmushin ta na yake a fuskar ta, da sauri ta sa kai ta fice daga dakin, ko rakiya Aslam bai mata ba dan zumuɗi, Asmah ce tamai singnal da ido alamar yaje ya rakata mana, shima da idon ya mata alamar bazai je ba, hararan shi tayi ta haura sama dan ta watsa ruwa ta na shigewa ya maida kofar falon ya rufe da key alamar ya gama fita kenan, ya kwashe yaran ya kaisu dakin su ya kwantar tunda duk a koshe suke ya shiga jijjigasu ba bata lokaci kuwa suka yi barci, dama haka suke yi idan barci zasuyi a tare sukeyi haka ma kuka da daya yayi abu sai sauran su kama suma. Ta samu dakin ta fes sai kamshi ke tashi yasha gyara sosai an shimfede bed din da Sabon zanin gado fari kal mai shegen taushi,kayan ta, ta tube ta daura tawel ta shiga toilet ta watsa ruwa, tana fitowa, ta tsaya gaban mirror ta shafa mai tare da shafe jikin ta lungu da sako da turaren da mummy ta bata a dan kwalba yanzu da zata dawon tace tayi amfani dashi yau idan taje gida ita karan kanta kanshi turaren ya kashe mata jiki, lokaci guda ya saukar mata da kasala tare da wani irin feeling mai zafi dama ga gyara ta sha harda na fitar hankali ,kayan barci ta dauka masu kyau riga da wando irin na turawa ta saka tazura silifas d'in ta na d'aki ta doshi falo da nufin ta dubo Aslam da yara, wayam taga falon ba kowa, cike da mamaki ta karaso tsakiyar falon, sai kawai gani tayi an kashe wuta lokaci daya ko ina yayi dumɗum da duhu, ita uwar yan tsoro take hantar cikin ta ya kaɗa, ta fara jero addu'o'i, tare da laluben hanya, ji tayi an taɓa kafaɗar ta ta baya, kara ta saki tare da juyowa ta bayan, tana juyowa ta sake ji an kuma taɓa ta, taƙarƙarewa tayi zata zunduma ihu, da sauri ya saka hannu ya rufe mata baki, tare da rungumota gaba daya jikin shi, jin haka yasa ta shiga zazzare ido daidai nan kuma wutar falon ya dawo, sake mata baki yayi yana mata dariya, ganin shine yasa ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya tare da fashewa da kuka shagwaba tana dukan shi a kirji, hada hannayen ta yayi ya rike yana sunsunar jikin ta yana lumste idanu, ganin haka yasa ta shiga mustu mutsun kwacewa, surar ta yayi bai dire a ko ina ba sai bed room ɗinshi,
Chapter 123 · 0% Book details