← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 126

Sashe 16

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe tara da minti goma aka daura auren Muhammad Aslam abdallah, da Zainab Abdussalam, akan sadaki masu yawan gaske,
Masha Allah daurin aure yayi jama'a saidai muyi fatan Allah ya zaunar dasu lpy,

Aslam da abokanshi sun shiga sunyi gaisuwar surukai kamar yadda yake a al'adar mutanen minna,

Direct kuma gida suka wuto in da zasu gabatar da reception kamar yadda Amir ya shirya,

A part d'insu Aslam din suka yada zango, nan ma'aikatan da aka turo daga galaxy hotel, inda akayi order abincin reception d'in suka shiga serving dinsu,

Abinci masu rai da motsi duk abinda mutum keso shi za'a zuba mai, ga drinks kala kala duk Amir ne ya dauki nauyin komai.

Cin abinbin su sukeyi suna firansu group group , kasancewar falon babbane yasa ya dauke su baki d'ayansu.

Aslam na zaune cikin kujera one sitter ya cire babban riga ya ajiye sai binsu yake da kallo, abin duniya gaba daya yabi ya dameshi, shi d'an farin cikin da mutum keyi bayan daurin auren shi, shi neman nashi farin cikin yayi ya rasa, kanshi ne ke matsanan cin ciwo ga kuma hayaniyar da friend dinsa keyi na qara mai ciwon kai, sai tsokanan shi sukeyi irin yadda abokai keyi, yayi shiru yaqi cewa komai saidai d'an murmushin yaqe,
Suma kasancewar sunsan halinshi na rashin son magana yasa basu wani damu ba.

Bacci yakeji sosai kuma yana gani idan har ya samu yayi baccin kanshi zai rage ciwo koma ya bari gaba d'aya, miqewa yayi da nufin yaje upstairs d'akin shi ya kwanta, wani tunani ne ya fado mai a rai, yasan indai ya kwanta a d'akin shi abokanshi baza su bari ya samu bacci yanda yake so ba, don haka rivas yayi daga niyar hawa saman ya nufi hanyar waje, ganin Anas nason tsaidashi yasa ya kara waya a kunnen shi kamar yana amsa call,

Sashen mummy ya nufa, yasan d'akin tane kawai zai samu yayi bacci hankali kwance , kuma su amir baza suyi tunanin yana can ba don ko d'akin mami yaje bai tsira ba tunda sunsan ya saba zuwa, zasu iya cewa bari su duba can in suna Neman shi,

Ganin alamar akwai mata cike da falon yasa yabi ta qofar kitchen ya haye sama ba wacce ta ganshi,

Dakin mummy ya shige ya qure A,c , sannan ya haye kan makeke bed d'inta' ya qudundune cikin bargo, inba mutum ya kula sosai ba bazai san a kwai mutum kwance a wajen ba.

Asmah wankanta ta sheqa sosai a toilet din mummy, bayan ta gama ta d'auki tawul d'aya daga cikin tawul d'in da ta gani a rataye a toilet d'in, ta daura, fitowa tayi kanta tsaye don tasan ba kowa a d'akin,

Aslam jin motsin an bude qofar toilet yasa ga bud'e idanun shi don ganin ko waye, Asmah ya gani ta fito daga toilet d'in daure da d'an,qaramin tawul da bai gama rufe mata cinyoyinta ba
Numfashin shi ne ya shiga seizing gabanshi ya shiga fad'uwa zuciyarshi ya shiga bugawa da sauri da sauri,

Asmah kam direct gaban mirror mummy ta nufa kasancewar tasan duk abinda take buqata na shafa akwai a kan mirror mummy, yasa taga gara ta tayi shafe shafenta anan gaba d'aya, inyaso tana komawa sai dai tasaka kayanta kawai,

Madubin na fuskantar gado ne don haka juyama Aslam baya tayi, kwata kwata bata lura da wani Aslam a d'akin ba,

Qurama bayanta ido yayi qur baya ko qaftawa, tun daga sama hara qasa yake qare mata kallo, dogon baqin gashinta dake kwance a bayanta, yabi da kallo kasancewar ta wanke kai yasa gashin kwanciya luf luf a kafad'unta ,sauko da idanun shi, yayi kan mazaunanta da suke nan masha Allah dasu,ga wani irin lafiyayyen hips da Allah ya hore mata kamar wata babban mace,

Tunda yake bai taba sanin haka qirar yarinyar nan yake ba, bai taba sanin haka take da kyawun diri ba sai yau , irinta ne maza kema laqabi da mai coca cola shape wasu kuma suce figure 8,

Yana wannan tunanin ne yaga ta sauke tawul d'in ta daurashi a qugunta taci gaba da shafa manta hankali kwance, baya ganinta ta cikin madubin kasancewar fitilar dakin bamai haske bane sosai,

Tana gama shafa mai a jiki yaga ta miqa hannu zata sauke tawul d'in qasa gaba daya donta shafa mai a qasanta ,

Wani munafikin tarine ya sarqe aslam wanda baisan daga ina ya fito ba , jinshi kawai yayi yana tarin ,

A firgice Asmah ta juyo jin tarin mutum a bayanta, idanunta ya sauka akan Aslam dake duqunqune cikin bargo, yayinda shi kuma idanun shi ya sauka akan tsayayyun madaidaitan breast dinta da suke cike tam tam a qirjinta, Wanda tsabar tsoratan da tayi jin motsin mutum a bayanta yasa ta juyo ba tare da rufesu ba, don ita duk zatonta gamo tayi,

Wani gigitaccen qara ta saki tare da tsugunawa ta qamqame jikin ta a wurin tana maqerqerta, gaba daya kwakwalwarta tsayawa yayi da aiki a lokacin, tama rasa me zatayi donta kare kanta, banda tsugunawar nan da tayi ta dunqule wuri daya kasa aiwatar da komai tayi,

Aslam kuwa lokacin daya juyo tsayayyun breast d'inta ne suka fara mai sallama,wani Yarr Yarr yaji a jikinshi kafin kuma wutan kanshi ya dauke dif ,na wucin gadi, daga bisani kuma ya miqe kamar an tsikareshi ya buga wani uban tsaki, cike da borin kunya yabar d'akin, ta qofar kitchen din daya shigo tanan ya bi ya fice daga part din jiki a sanyaye🚶‍♂️🚶‍♂️🚶‍♂️🚶‍♂️

Karku manta comment d'inku shike qaramin qaimi wajen sambad'a muku typing🥰

Oum ummetarh
07041130088

Share
And
Comment🙏🏻
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Page 41 & 42

Asmah jin qarar qofa alamar ya bar dakin, ta tashi da sauri ta rarumi hijabin mummy data gani, ta zura akan tawul din jikinta ta fice daga dakin itama duk ilahirin jikinta rawa yakeyi,

Saida ta tsaya a qofar dakinsu ta saisaita kanta sannan ta shiga, samunsu tayi suma duk sunyi wanka suna shiryawa, wucesu tayi ta fada kan gado rigingine,

Kallon kallo su zahra suka shigayi a tsakanin su, Amira ce tayi qarfin halin qarasawa bakin bed d'in, ta dago kan Asman ta daura kan cinyarata, sannan tace, "lafiya sister meya sameki" alama Asmah ta mata da hannu kanta ke sara mata,

Batool ce ta qaraso da sauri ta zauna kusa da ita tace " ayya sannu Asmah, sannu kinji, kwanta ki huta qila aikin hada breakfast d'in da mami ta saka mu dazu ne, yasa mata ciwon kai kunga ita ta zage taketa aiki sosai , kunsanta da rashin ganda,"
Zahra tace barinje na dauko miki maganin ciwon kai a d'akin mummy, girgiza mata kai tayi alamar ta barshi bazata sha ba,

Kwantar da ita Amira tayi suka ci gaba da shirin su, sunyi suna mata sannu,rintse idanuwa tayi kamar mai bacci, take abubuwan da suka faru few minutes da suka wuce,suka shiga dawo mata fresh a kwakwalwarta, innalillahi wainnailahi rajiun ta shiga maimai tawa acikin zuciyarta, gaba d'aya ranta a jagule yake, gsky Aslam ya cuceta , kuma Allah ya isa ganin jikinta da yayi, bata yafe ba,

A hankali ta fara samun relief a cikin zuciyarta , saida ta kwashe kusan fourty minutes a haka kafin ta yunqura ta miqe, ganin tunanin ba abinda zai haifar mata sai qarin takaici da damuwa, tunda abinda zai faru ya riga ya faru , sai a kiyaye gaba,

Zuwa lokacin su Amira sun gama shiryawansu tsab da su sunsha makeup kowacce ta kashe daurin zamani kamar sune amaren,

Ganin ta miqe yasa suka shiga jera mata sannu, tare da tambayar ta ya kan, da sauqi tace musu ta shiga toilet ta wanko fuskarta, tazo ta zauna itama batool ta tsantsara mata makeup, tayi kyau kuwa sosai kamar wata balarabiya, Amira ta miqo mata nata kayan tasanya,

Wow masha Allah Asmah kam tana da kyau sosai tun daga kyawun fuska, kyawun diri, uwa uba kyauwun hali da kyawun zuciya,

Kashe dauri tayi itama suka fantama cikin gida akaci gaba da yinin biki dasu,

Asmah kam jikinta a sanyaye yake, tun abinda ya faru dazu amma haka ta daure taci gaba da harkokin gabanta, har zuwa dare inda nan suka kuma caba wani adon cikin ankon su na dinner.

Aslam kam yana barin part din mummy, parky lot ya wuce ya bude motarshi ya shiga back sit ya zauna , tunanin abinda ya gani few minutes ago ne ya shima mai yawo filla filla a cikin brain dinshi, yana kisima kyau da tsaruwar halittan yarinyar, tunanin daya dinga yi kenan har baisan tsawon lokacin daya dauka yana zaune cikin mota yana tunanin ba , baccin dai da bai samu yayi ba kenan,

Can kuma kamar daga sama yaji wani bangare na zuciyarshi na kwa'banshi da cewa, meye haka kakeyi Aslam, ka zauna kana bata lokacin ka a banza kana tunanin wannan mayyar yarinyar, me take dashi da har zaka tsaya kana tunanin ta, kaida kake da amarya kamar zee babban yarinya meye na jikin wata mace zai rudeka, har ka zauna kana 'bata time d'inka a banza a hofi, tsaki yaja a fili tare da fitowa daga motar ya nufi sashen su, yana isowa kuwa ya taradda wasu friend d'insa nata neman shi sumai sallama, zasu wuce, yayinda wasu da dama sun riga sun wuce saida a had'u wurin dinner anjima.

A mooris event za a gudanar da dinner Wanda za,a fara 9 a gama 1am,

Misalin 9:30 na dare yammatan mummy na hango zaune a falon mummy sun sha makeup, sai zuba kamshi sukeyi,kamar wadanda zasuje gasar zabar sarauniyar kyau, su biyar ne yau harda Khadijah da suka zo d'azu da mamanta, mamanta bazata kwana anan ba gidan alhaji Mallam zata kwana, ita kuma Khadijah tace anan zata kwana don tana son zuwa dinner, da'ker mama ta barta saida mummy ta saka baki,

Itama Khadijah taci kwalliyarta cikin lece dinta milk colour kasancewar ita batada ankon su Asmah

Kamal ne yayi sallama yace su taso suje, dama shi suke zaman jira, don yace in sun shirya su jirashi ya zo ya daukesu.
Chapter 16 · 0% Book details