Sashe 9
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ya kamal ne yayi sallama a qofar falon tare da shigowa fuskarsa dauke da murmushi kamar ko yaushe ,yasha kwalliya cikin qananan kaya shima sai zuba kamshi yakeyi , kusan hada baki sukayi gurin amsa mishi sallama tare da fara gaishe shi , amsa musu gaisuwar ya shigayi da sakin fuska kamar yadda ya saba musu , zaida kallonshi yayi akan zahra kasancewar yafi d'asawa da ita yace "sisto me zan samu a nan ne na breakfast" ya fada yana shafa cikin shi alamar yunwa, yaci gaba da cewa"wai tea suka sha, ni kuma wlh na gani da tea dinnan "
Murmushi zahra tayi tace "aiko ya kamal kai kai taki sa'a yau dan yau Asmah ne ta mana masan nan nata mai shegen dadi da shi muka karya , kuma naga akwai saura bari zubo maka " murmushi kamal yayi jin abinda zahra ta fada sosai yake daukin cin masan badan masa ta dame shi ba saidan jin cewa Asmah ce tayi masan, . ...don wannan karon ya shirya tsab ba gudu ba ja da baya , bazai qara maimaita kuskuren daya , bazai yarda ya sake aikata iri sakacin daya aikata a baya ba, duk da cewa har cikin zuciyarshi baiji dadin abinda Aslam ya aikata mataba , amma shi a ganinshi wata dama ta biyu ne ya sake bashi akanta , kuma bazai yi wasa da damarshi ba , ... Zahra ce ta katsemai tunani ta hanyar ajiye mai filet din masan datayi serving dinshi a gaban shi, kamshin miyan taushen da yaji naman rago, hade da kamshin soyayyen Masan shinkafa ya daki hancinshi lumshe ido yayi tare da budesu akan Asmah sake zaune kushin din dake kallon nashi, filet din Masan ya daga sama yanaci yana Kallonta a fakaice , yana jin wani irin soyayyarta na qara narkar da zuciya, yayinda ita gaba daya hankalinta baya kanshi, yana kan amira da batool daketa musu akan wani Indian series da take haskawa a TV tashar Bollywood...
9:00am dai dai Aslam ya farka daga baccin safen daya koma bayan asubah, miqewa yayi ya shiga toilet yayi wanka , shiryawa yayi cikin jeans da t-shirt baqaqe masu kyau , main falo ya sakko yana shafa cikinsa yana yamutsa fuska alamar yunwa na sakad'arsa, frige ya bude ganin babu wani abun tabawa yasa dole ya fito direct kuma part din mummy ya nufa , daidai lokacin da kamal ke cin masa yayinda yan matan mummy ke zaune suna kallo....
Kuyi manDate: Oct 10, 2022
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
page 27 & 28
Gaidashi su zahra suka shiga yi, a daqile yake amsawa ganin haka yasa Asmah qin gaisheshi,...kamal ne ya miqa mishi hannu suyi musabaha da'ker ya mika hannunshi sai wani babbata rai yake, haka kurum yaji yana jin haushin kamal din, ...shiko baima San yana yi ba ci gaba da cin abincinshi yayi, yana yi yana kallon sahibarsa,.....
Sake maida kallonshi yayi kan Asmah ganin kowa na gaishe shi ita ta dauke kanta kamar bata ganshi,..gyaran murya yayi "uhummm" dago kai tayi ta sauke idanunta cikin nashi , dukansu saida gabansu ya fadi , ...rabonshi da ganinta tun ranar da yasa mummy ta turo mishi ita part dinsu, gabanin Bikin nan ranar da ya mata warning da wuqa , da idanun shi ya mata alamar kallon fa, dauke kanta tayi daga kallon shi ta mayar kan tv still bata gaishe shiba, a zuciyarta tana cewa "wlh wannan ba Asmah da ka Sani da bace , eheeee wannan wata sabuwar Asmah ce da take daidai da rashin mutuncin ka, wacce kana ce mata kule zata ce maka cassss, don yanzu ba tsoranka nakeji, don duk wani girmanka a idona ka zubar ni kuma nasa qafata na taketa" duk wannan a zuciyarta take fada ,...shiko Aslam mamakinta ne ya kamashi ganin yadda ta dauke kai daga kallon shi kamar taga wani banza, ba wannan rawan jikin da tsoron shi dayake gani kullum a tattare da ita , shi sai yake ganima kamar kallon tsana take jifanshi dashi ma, ...kwafa yayi yana girgiza kai ya nufi dakin mummy ganin bai ganta a falon ba, ,a zuciyarshi kuwa yana aunawa Asmah zagi, mayya kawai mai idon mayu kurwata kur wlh, haka kawai da sassafen nan tasa gabana nata faduwa,.shiga dakin mummy yayi bai ganta ba. falon ya sake dawowa,batool ya kalla tare da cewa "kee mummy fa" da sauri batool ta amsa mai da tana part din daddy , hanyar fita falon yayi tare da ce mata "ki kawo min abinci part dina yanzu" ya fada fuskar nan a murtuke cike da isa, ya fice a falon, bai cewa kowa komai ba, batool ce ta mike cikin zumbura baki ta nufi kitchen, ta hado mai koma da komai a tire ,... Dukkansu basa son zuwa aikensa , saboda sunsan ba,a wanyewa dashi lpy karshenta mutum yasha rankwashi ko mari, yamafi Aiken amira duk cikin su, a cewarshi tafisu hankali da nustuwa ,...
Ajiye Tiren batool tayi a kan table din dake tsakiyar falon, murtike fuska tayi exactly yadda Aslam ke murtuke musu fuska , gyara tsayuwarta tayi ta fara irin tafiyan shi, d'akin mummy ta nufa cikin kwaikoyan irin tafiyanshi, duk ido suka bita dashi yuuu suna kallonta, fitowa tayi daga d'akin mummy tana ciccin magani kallon zahra tayi tace "kee mummy fa" tana 'kwai'kwayan muryan shi, aiko gaba d,aya suka kyalkyale da dariya jin yadda ta kaurara murya irin na bosawa wai ita tana kwaikwayan muryan Aslam, itako batool bako alamar murmushi a fuskarta ta dake abinta, qara kallon zahra tayi dake kwasan dariya , ta sake cewa cikin 'kwai'kwayan Aslam "ki kawomin abincina part dina yanzu "ta fada exactly yadda ya fada tana mai fita a falon cikin irin takun shi , amira cikin dariya tace"Allah yasa kina leqawa Ku had'a ido" aiko dai tana leqawa ta hangoshi , Allah yasota ya juya baya bai ganta ba , da gudu ta kwaso ta dawo ciki tana haki tace"wlh amira bakin kai shegen kaifi gare shi "dukkansu qara kwashewa sukayi da dariya zahra tace"yar banza ga tsoro ga mugun aiki" ...."eh din "batool tace tare da kinkiman tiren tayi hanyar waje don kai mai abinci,....kamal daya gama shan dariyar diraman batool ya miqe tare da kallon Asmah yace "sister anjima da yamma zaki rakani shopping , inason inma budurwata shopping , kuma kinga ni bansan kan kayan mata ba ," ya fada yana langwabar da kai yayi fuskan tausayi don kar tace baza taje ba , murmushinta mai narkar mai da zuciya ta sake tare da cewa "to ya kamal Allah ya kaimu anjiman, zan sanar ma mummy inta amince"... Amira tace "Allah sarki ya kamal zanje nima" zahra tace "nima haka ya kamal don Allah" harara wasa wa watsa musu tare da cewa "Allah ya kiyaye wa zai fita da Ku, yara sai shegen rawar kai kaman ana kadaku da ruwan hanji, Ku bari gobe bello ya kai Ku," ya fada yana ficewa a falon don karma su qara hada shi Allah,... Yana fita Asmah ta tashi tana kwaso shoki tana musu gwalo, filon kujera amira ta dauka ta bita dashi, kwasa tayi da gudu hanyar qofa , saiga mummy ta sawo kai saura kadan suyi karo Allah ya kiyaye, ...mummy tace"ya haka amira mekefaruwa "langwabe kai amira tayi tana turo baki cikin shagwaba tace "mummy gwalo fa take mana " mummy tace"gwalo akan me" zahra ce ta labartawa mummy abinda ya faru,... gwalesu mummy tayi da cewa "aikam dai kamal yana da gaskiya, inya kwasheku ai sai kusa aje ata nunashi ana dariya, tsabar rawar kanku gara dai yaje da Asmah don itace ma dan dama dama a cikin ku'......
Da misalin qarfe hudu da rabi yan matan mummy ne dukkan su a cikin makeken dakinsu dake part din mummy , daki ne babba mai dauke da madaidaitan gadaje har guda biyu, iri daya da kuma maka makan wardrobe mai qofa shida shida shima har biyu , da kuma madubi babba guda daya shaqare da kayan kwalliya na mata da turaruka masu tsada kala kala, wannan duk aikin mummy ne,...
Komai na dakin pink and milk colour ne idan ka cire fridge da kayan kallo da suka kasance baqaqe, hatta painting dakin pink and milk ne, dakin ya hadu sosai gwanin birgewa ,.