← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 126

Sashe 29

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gdy mami tayi ta amsa ta fara ci, zee na zaune duk kamshi ya gama cika mata ciki, tana jira batool ta gama zuba ma mami ta zubo mata,don yunwa takeji, amma ga mamakin ta sai taga batool ta rufe kuloli ta koma ta zauna ,

Mami na lura da ita sarai ta gane abinda take jira, amma taqi saka musu baki , gara abarta da batool ɗin don dama ance , Karen bama shike maganin zoman bana,

Batool da mami dan fira suka shiga yi jefi jefi, can kuma kaman ance mami ta waiga ta hango Aslam na motsi da idanu alamar zai farka,

Da sauri mami ta miqe tsaye tace " alhamdulillahi batool ya farka" itama zee sai lokacin ta lura dan kallon fuskan shi kawai take amma hankalin ta gaba daya yana kan abincin dake kula a rufe,

Mami tace "batool yi sauri ki kira Dr bashir " da sauri batool ta fice tambayar wata cleaner tayi office din Dr bashir , nuna mata layin da office's din doctoci yake,tace tabi zata ga office din da aka rubuta Dr bashir ta shiga nan ne,

Da sauri ta qarasa ta duba cikin sa'a kuwa ba ko wani patient don haka ta shiga,

Har ta bude baki zata fara gaishe , shi idanun su ya sarqe dana juna cikin gwalalo idanu cike da mamakin ganin mutumin ta, a mastayin Dr bashir,

Shi kuma wani irin farin ciki ne ya lullubeshi , nan take yaji wani nishadi na shigar shi na ganin ta ,jiya daidai da second daya tunanin ta bai barshi ya huta ba, duk kuwa da halin da Aslam ke ciki bai hana shi kwana tunanin ta ba,

Daure fuska yayi kamar bai taba ganin ta ba tunawa da yayi wacece batool , yanzu zata zube mai fitsara

Cikin dakewa yace" madam ya zaki shigo min office haka ba excuse , saikace zaki shiga toilet, ai ko toilet ne naga sai mutum yayi addu'a kafin ya shiga"

Saida ta fakaici idanshi ta watsa mai harara ,sannan tace " patient dinka Aslam ya farka"

Duk harare hararen da takeyi yana kallonta ta gefen Ido amma jin abin da ta faɗa , na cewa Aslam ya farka yasa ya miqe da sauri , yana tattara kayan aikin shi ,yayi waje ,rufamai baya tayi,

Koda suka isa dakin ya buɗe Ido tangararas , yana kallon kowa, fita waje Dr bash yace suyi, sannan ya shiga duba shi,

Alhamdulillahi abinda ake buqata komai ya daidaita bugun zuciyar shi ya dawo normal kwakwalwarta shi ya samu Hutun da ake son ya samu, saidai rashin qarfin jiki da kuma ulcer Wanda waɗannan dama sai a hankali zasu daidai ta,

Nurse Dr bash ya aikata yace tace ma mami a haɗa ma Aslam tea , yasha , don cikin shi ya warware kafin yaci abinci yasha magani,

Mami cewa tayi batool taje ta haɗa, don shakkar cewa zee taje tayi takeyi, ganin tun sannun da ya haɗa su jiya har yanzu wani mahimmin magana bai sake haɗasu ba,

Ɗakin ta shiga ta haɗa mai tea mai kauri yana turiri , ta miƙa ma Dr bash Wanda shi zai bashi , cikin rashin sani wuri karban shayin hannun sun ya tabina juna ,

Da sauri ta saki kofin shayin ta shiga yarfe hannu kamar wacce wuta ya lasar ma hannu kokuma wutar lantarki yaja,

Allah ya kiyaye Dr bash ya riqe kofin da sauri da ba abin da zai hana shayin zubewa,

Murmushi Dr bash yayi a zuciyarshi yace lallai ma yarinyar nan , dan hannu na ya taba nata take wannan yarfe yarfen,? Hmmmm zakiyi bayani ne yarinya,

A fili kuma ya watsa mata harara yace" waike me yasa bakiyin Abu a hankali ne for god sake"

Murguda baki tayi sannan ta fice ɗaga dakin,

Haka Aslam ya wuni a asibiti cikin kulawa , kan dare jiki yayi sauqi alhamdulillahi , don sosai mami take takura mai yana cin abinci, yana shan magani, kan kwabo sai gashi har yana zama da kanshi,

Dangi ana ta zuwa dubashi , alhaji baba dai baizo ba, daddy ma jin ya farka kuma jiki da sauƙi yasa bai koma ba ,don har yanzu bai huce da rashin kunyar da yama mahifinsa rannan ba, mummy ma kawaici ya hanata komawa,

Zee kam ganin har sha biyu ba Wanda ya mata tayin abinci yasa ta fita wajen asibitin ta siya abinci taci, da rana ma koda aka mata tayi ƙinci tayi , wai ita tayi fushi, yanda bata damuwa da lamarin su ,haka ba Wanda ya damu da taci ko bata ciba,

Ƴan matan mummy basu samu zuwa asibitin ba sai dare ya kamal ya kwashe su , suka tafi,

suna shiga suka tarad da ya Amir da Dr bash a ɗakin sai kuma zee, dake gefe tana charting,

Jin motsin shigoya yasa Aslam dago kai yakai duban shi ga ,ƙofa akan fuskarta idanun shi suka sauka, itama kuma hakan ne ta kasance a gareta,

Da sauri suka dauke idanuwansu daga kan juna, tsohon miki ne ya tashi, don ji yayi zuciyar shi na bugawa da ƙarfi fat fat fat,

Qrasowa sukayi cikin dakin , gaidashi suka shiga yi tare da tambayar sa ya jiki,cikin jimla ya amsa musu da,"da sauƙi" hannu kamal ya miƙama su Amir da bash suka gaisa,

Zahra CE ta dubi gefen zee tace "ina wuni anty zee " amira da Asmah ma suka gaishe ta , batool kam dauke kai tayi kamar bata ganta ba ta juya fuskan ta gefe tana tabe baki,

Tun shigowar su sai lokacin ta dago kai daga charting dinta don ganin su wanene ma , idanunta ne ya sauka akan Asmah , aiko ji tayi zuciyarta tayi baƙiƙirin kishi ya motsa , wani mugun kallon sama da qasa ta watsa musu kafin taja wani mugun tsakin da saida ya jowa hankalin kowa na dakin kanta,

Mursisi yayi ta dauke kallonta daga garesu taci gaba da charting dinta,

Jiki ba kwari suka nemi guri suka zazzauna , Amir ne ya tashi ya fita yace musu yana zuwa, can harabar asibiti yaje ya nemi guri ya zauna, wayar shi ya laluba ya danno lambar Amira da yayi saving da baby,

Suna zaune a dakin kiran ya shigo wayar ta , ganin ya Amir ne ke kira yasa ta daga , cikin magana kasa kasa yadda ko Asmah dake kusa da ita bataji me take cewa ba tayi sallama, magana sukayi na yan sakonni ta ajiye wayar tana murmushi,

Minti uku ta qara kafin ta miƙe tace "sisters ina zuwa, " zahra tace "sai ina " tace "nan waje", ta fice da sauri dan kar su ƙara tambayar ta wani abin,

Samun shi tayi a inda ya mata kwatance nan suka zauna suka shiga firan su na masoya da tsare tsaren bikin su hankali kwance,

Kallo daya zakasan wadannan masoyane da suke cike da tsantsar kaunan juna da shauɗin juna,

A can dakin kam Aslam tun bayan kallo dayan da ya mata ya zame a hankali ya kwanta,zuciyar shi na buguwa , kishi mai tsanani yana taso mai ji yake kamar , ya tashi ya shaƙe kamal har sai ya dena nunfashi, zuciyar shi ce ta dinta tunzura shi, amma cikin ikon Allah ya shiga maimaita innalillahi wainnaialahi rajiun, lamo yayi ya lumshe ido kamar me bacci , da haka har baccin gaske ya kwashe shi kasan cewar yasha magunguna masu ɗarfi,

Fira aka shiga yi a dakin tsakanin kamal da Dr bash sai jefi jefi su Zahra na saka musu baki,

Zee jin sun dameta yasa ta miƙe tare da jan tsaki ta fice daga ɗakin ,

Harara batool ta rakata dashi kafin ita ma ta ja nata tsakin ,

Dr bash da dama duk abinda yakeyi hankalin shi na kanta , a zuciyar shi yace " yawwa dama nasan ko kowa bai tanka ba , ai hajiya masifatu ta tanka,"

CI gaba sukayi da hira, can Dr bash yace "subhanallahi wlh na manta akwai wani allura guda daya da za'amai cikin dare gashi bamu dashi anan sai anje pharmacy a waje an siyo" kamal yace"ayya to kawo na siyo mana"

Rubuta mishi sunan alluran yayi ya miqa mishi, amsa yayi ya miƙe har yakai bakin ƙofa ya juyo ya kalli Asmah, yace asmy ba rakiya, cikin dan jin kunya ta watsa mishi hararan wasa , tana murmushi, hannu ya haɗe mata alamar roƙo yayi fuskar tausayi, saida ta ja mai aji sannan ta miqe tabi bayanshi,

Dakin ya rage daga batool da zahra sai Dr bash, sai aslam dake bacci,

Dr bash ya dubi zahra yace "kanwata zahra ya makaranta ya karatu," cikin murmushi ta amsa da "makaranta alhamdulillahi , karatu kuma akwai wuya ya bashir" bash yayi murmushi yace "karatun ma balle irin namu sai mai ƙoƙari, kuma ke da gani zakiyi ƙoƙari, ganin yadda kike da nutsuwa da hankali , ba kamar wasu yan matan ba da zaki gansu kullun cikin guje guje kamar yan nursery,"

Dagowa batool tayi da sauri ta kalle shi jin abin da take cewa ,ko ba'a fad'a ba tasan da ita yakeyi,

Zahra ko cikin jin dadin yabon da aka mata, tace " nifa ya bashir bani da wani qoqari saidai taimakon Allah kawai, dama batool kace itace mai kokari don duk cikin mu ta fimu ƙoƙari," cikin son ya tsokani batool yace"kai zahra wannan shirmammiyar yarinyar da ganin ta baza tayi wani qoqari ba, irinsu ne fa masu yin espo a class, da ganin idonta na rashin kunya ta kware a iya espo"

Kan uba aiko dai ya taro masifa don dama tun dazu daurewa kawai takeyi amma a cike take fam dashi kamar zata fashi,

Aiko nan ta shiga zazzaga mai ruwan rashin kunya tanayi tana murguda baki, ta inda take shiga ba tanan take fitaba,

Aiko dai Dr bash mutuwar zaune yayi yana kallonta , ɗan bakinta da take masifa tana mugudawa yake bi da kallo , gaba daya masifarta burge shi yakeyi, abin na mishi ɗaɗin kallo yana sakashi nishadi,

Saida tayi mai isar ta tayi shiru, zahra kam tagumi tayi da hannu bibbiyu tana kallon ikon Allah , don tun ɗazu take ce mata ya isa amma taqi kulata , ganin haka yasa ta yi tagumi tana kallonta,
Chapter 29 · 0% Book details