← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 126

Sashe 60

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryama kafa yaki takuwa fah jama'a, ga farida itama ta kanta take balle ta taimaka mata su shiga gida, Allah ne ya turo wani kaninta namiji, irin yan oyya dinan da ganin shi ma yana bushe bushe, zai shiga gida ya ganta yace"A'a hajiya Mairo kece, sannu da zuwa, zan samu na sigari nan " cikin muryar azaba tace "gali dan Allah taimakeni ka kama ni na shiga gida" sai lokacin ya lura da kafarta yadda ya kumbura, dariya ya kwashe dashi, tare da cewa "ke kuma wa miki eyane a kafa haka," tace "bansan surutu gali dan Allah ka kamani" yace"zan taimaka miki amma a nawa dan kinsan yanzu gwamnati ta hana aikin banza, zaki bani dari biyu in samu na korawa anjima" ba yadda ta iya dole haka ta ciro dubu daya ta bashi ya dawo mata da canji, sannan ya taimaka mata ta shiga, farida dama tuni ta shige, a tsaye suka tarad da mahaifiyar su sai sallallami takeyi ita kuma farida na zaune kan wani tsohon tabarma tana kuka, tana hango maryama ta kara karfin salatinta tana direwa tace "shike nan kin kaso auren kinji dadi sai kizo ki zauna ai ga duwawuna ga naki" tana gama fadin haka ta shige dakinta dake nan ciki daya bata kara fitowa ba kuwa saida mahaifin su Maryama Wanda suke kira da Dada ya dawo, yayi mallakin ganin Maryama a gida har war haka dan bata taba kaiwa ba in tazo inta dade awa biyu, kuma ko ruwan gidan bata iya sha, balle abinci, mamakinshi bai girmamaba saida yaga kafarta a kumbure ita kuma farida ido daya a kumbure yana Neman likewa.

Mahaifiyar su wanda suke kira da mama ta fito ta tare shi bayan ya huta yake tambayar lafiya mai ya samu Maryama da farida mai Maryama keyi a gida har yanzu bata koma ba, labarta mai abinda farida ta gaya mata " ashsha " yace tare da girgiza kai daga haka kuma bai kara cewa komai ba.

Bayan Dada ya fita sallan isha'i ne ya shigo tare da wani dan unguwar su surajo mai gyaran targade, surajo na ganin Maryama za'a ma gyara ya cije baki yana girgiza kai, surajo irin mutanan nan ne masu shegen ruko,dan tun Maryama na budurwa wani sabani ya taba hadasu, har kanin ta gali ya kira yan kaura suka mai duka, duk da a lokacin ya rama dukan da su gali suka mai dan kwana su kusan goma a cell, amma duk da haka yana nan kullace da maryama, yau kuwa gani zai mata gyara yasa ya kudiri aniyar ramawa.

Dada yace "Maryama ki gyara ga surajo na kira ya duba miki kafar nan taki, da alama targade ne" ba yacce ta iya da'ker ta mike kaɗan, surajo na tabawa ta tsallara ihu, dagowa yayi yacema Dada "wannan fa baza ta tsaya ba a samo katti su riketa " karaf a kunnen gali da abokin shi baure da suka zo daukar tuwon dare, gali yace "gamu nan mune nan kattin mu zamu daddaneta inta kamama mu ɗaɗɗaureta Allah wlh, kai shege baure matso tanan operation ya samu" magana yakeyi cikin muryar su ta shiryayyu, banace ba shiryayyu.

Baure yace "A'a'ah mairo sannu mairamu" ba tausayi haka suka rirriketa, tana ta zabga ihu ga kannenta ta nan rututu kusan rai goma maza da mata don itace ta farida gidan daga ita sai gali sai farida, Allah ne ya taimaketa ya tsamota ya hada ta da Barr ya aure ta,surajo ko tunda ya duke ya damki kafar saida ya gama luguguce shi tana ihu na kusan minti goma sannan ya fara mata gyaran tsakani da Allah.

Wayyo maryama dan azaba harda su fitsari a wando, su baure kuwa sai dariyar keta suke mata, saida aka gama gyaran, suka sake ta tare da lalemata yar wayar ta da dan kudinta da tazo dasu har ATM card dinta don pos din gaba daya suka dauke.

Bayan mama ta gama tuwo ta zubo mata miyyar kukan nan Kore shar yako ji daddawa sai kamshin shi ke tashi, da tuwan jan dawanta da aka tukashi tun wurin azahar duk ya sassandare.

Ko kallon abincin maryama batayi ba, haka ta hakura zata kwana da yunwa, bata raina kanta ba saida suka zo kwanciya, innalillahi daki daya dan karami ita da kannenta mata su kusan bakwai, gashi mutum hudu a cikin su na fitsarin kwance, wani yagalgalallan katifa ne a dakin Wanda farida dame bi mata suke kwana akai sauran kuma suyi shimfida a kasa su kwanta, da'ker farida da hansai suka sauka suka bata katifar, hansai kuwa datafi farida tsiwa sai yaɓa mata magana takeyi a kaikaice kamar zata zageta dama basu ɗasawa saboda rashin kunyarta sunfi shiri da farida.

Washe gari Dada ya nemi ganin Barr donji ta bakin shi, don baice ma Maryama komai ba tukun sai yaji ta bakin Barr da yake Dada tsohon karki ne kuma yasan mutunci sosai.

Brr bai bata lokaci ba ya same shi har shagonshi a sabon kasuwa, don nan hace yaje ya sameshi, bayan sun gaisa Dada yace"Adam abinda yasa na kiraka nan, in son miyi magana a sirrance, ka gayamin gsky tsakanin ka da Allah mai ya hada ka da matarka Maryama har kace taje gida saika neme ta"sauke kai Adam yayi komai na dawo mai fresh a ido kamar lokacin abin ke faruwa, bai boyema Dada komai ba kuwa ya zayyane mai abinda ke faruwa tun daga lokacin daya fara Neman aure har zuwa abinda ya faru jiya.

Jinjina kai Dada yayi yace"sannu Adam da hakuri Ashe haka kata fama da rashin hankalin wannan yarinya maryama, Allah ya maka albarka kayi abinda ya dace kuma ko nine iya abinda zanyi kenan, nasan ta kaika iyaka ne yasa kace taje gida, ka kuwa kawo kuka gidan mutuwa, insha Allah Maryama baza ta dawo gidan ka ba sai tayi hankali, ka barta a gida na tsawon wata uku kwarara karka wawwayeta koda wasa, ni kuma zan idasa maka aikin, idan tayi hankali da kaina zan nemeka kazo ka tafi da ita" godiya Adam ya shiga zubawa da zai wuce ya kawo dubu goma ya bashi da'ker ya amsa sukayi sallama.

(Nawawooo Maryama kinshiga uku😤 sai Adam da babynshi sun gama cin amarci zamu lekoki muga wani hali kike ciki, Dada good job Allah ya kara girma)

Jinshi yakeyi wasai wlh kwana biyu daba Maryama har ƙiban shi yadan fara dawowa, haba wlh masifa bata da dadi ko kanɗa😔

Yau kimanin sati guda kenan cif da faruwar wannan lamari, misalin karfe bakwai da rabi na dare fitowa shi kenan daga masjid din kusa da gidan shi, dawowa shi kenan yau tunda ya fita tun safe bai samu dawowa gida ba sai yanzu wani baban uzirine ya rikeshi.

Motar shi ya shiga ya karaso gidan shi mai gadi ya wangale mai get ya shigo ciki, parking yayi a inda a parking lot, fitowa yayi ya bude bayan motar ya dauki ledodin shi na tsaraba daya siyo ma zahra da yaranta, ya nufo part dinta fuskarsa dauke da kayataccen murmushi.

Zaune suke a falo bayan sunyi sallar ishan su,sunyi dinner, sanan sukazo suka zaune zahra na koya musu musu karatun alkur'ani, Hadda sukeyi danda kai take musu, jin dirar motar Barr, daga ita har yaran ba'asan wa yafi ɗokin ganin shi, duk da karatu sukeyi kowannen su saida farin cikin hakan ya bayyana a fuskar shi, sallama yayi cikin daddaɗan muryassa sannan a hankali ya dago labule ya shigo falon, amsawa kawai sukayi fuskar su dauke da madaukakin farin ciki,ba daman su tashi sumai oyoyoooo tunda suna karatu, Ahmad da anisa kam da yake kananane kasa jurewa sukayi saida suka tashi suka nufe da gudu, da sauri cikin zakuwa ya tare su ya cira Ahmad sama, bubbuga kafa anisa ta fara yi zatayi kuka saura ita, ajiye Ahmad yayi itama ya dagata sama take ta shiga babbaka dariya, suma su zahra dake kallon su saida suka dara.

Rike hannun yaran yayi suka karasa inda su zahra suke zama yayi a kusa da ita kan 3 sitter yayinda su hannan ke zaune a kasa sun lankwashe kafa suna daukar hadda.

Ganin ya dawo yasa suka dakata haka addu'a tayi musu suka ansa da amin harda Barr, suna ashafawa hanan da suhail suma suka tashi suka rungume daddyn nasu suna mai sannu da zuwa, amsa musu yayi yana tambayar su ya gida, suhail yasa rigima wai shima a ɗaga shi kamar yadda akama su Ahmad, ɗaga shi Barr yayi, ganin haka hanan dake gefe taba murmushi tace "daddy nima" dariya suka sa mata zahra tace "harda ke ƙatotuwa dake 13 years fa aikin wuci ɗauka" Barr cewa yayi"zo oh daughter na ɗagaki ni a gurina baki wuci ɗauka ba, har itama data girmeki zan iya daukarta, balle ke"zuwa kuwa tayin ya dagata itama, barin su yayi nan falo ya mike zahra zata bishi yace ta zaune da yara zai dan watsa ruwa ne yana zuwa, bata son musu dashi don haka ta zauna din suka ci gaba da hira suna wasanni, gwanin sha'awa.

15 minutes ya kwashe sannan ya fito sanye da jallabiya, yayi wanka ya rage kaya masu nauyi,zuwa lokacin tuni Ahmad da anisa sunyi barci su hanan suma sai hamma sukeyi, ganin haka yasa yace su tashi ya rakasu su kwanta gobe akwai school.

Har dakinsu suka rakashi shida babynshi, addu'an bacci zahra ta musu ta tottofa musu, sannan suka musu sallama suka kashe musu wuta suka ja musu kofa.

Falo suka dawo tana gaba yana bayanta, sun iso daidai tsakiyar falon taji ya mata wani irin wawan runguma ta baya ya manna kanshi a dokin wuyanta, a hankali ya rada mata a kunne "na dawo kowa ya rungume amma banda ke ko," murmushi tayi tace "kayi hakuri hubby naga idanun yaran mu ne shiyasa, amma next time zan kiyaye" ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya sake ta ya kama hannun ta suka nufi dinning , yau gaba daya jinshi yakeyi wani iri, feeling ne mai tsanani yake damunshi, tunda safe daurewa kawai yakeyi.
Chapter 60 · 0% Book details