Sashe 121
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
ba editing ayi hakuri
Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasaukar da wannan book ɗin ga duk wacce ta rasa hahaifiya Allah kajiƙan iyayen nu.}
Page 132
Wani irin haihuwa Asma'u tayi mai ban mamaki gaba d'aya da tasowar na'kudan da haihuwar tayi shine cikin abinda baifi minti biyar ba, tsabar rud'ewa mummy rasa me ya kamata tayi, tayi ,kukan jinjiran daya karad'e kunnenta ne ya yasa ta dawo cikin hayyacinta da wani irin sauri ta fice daga toilet d'in jakar da suka had'a kayan haihuwa ta bud'e, zazzage shi tayi ta d'auki kwalin reza da sauri ta koma toilet d'in, yanke cibiyan tayi ta d'auki zanin ta da Asmah ta rataye ta raba shi uku ta nad'esu a ciki ta kaisu kan bed ta jere su, ta koma toilet d'in, heater d'in ruwan zafi ta kunna ta daidaita shi cikin abin da baifi awa d'aya ba mummy ta gama gyara Asmah da babies d'inta ba tare da kowa a gidan ya sani ba,Asmah tuna barcin gajiya ya kwashe ta babies d'in ma da suka ji ruwan zafi shiru sukayi basu sake kuka ba tunda suka yi tunda sukayi na fadowa duniya wanda yake wajibi. Sai da ta tabbatar komai ya daidai ta sannan ta d'auki wayar ta daddy tafara kira, dan shaida wa wannan daddad'an labarin mai dauke da abin al'ajabi, yana zaune a office ya ga kiran mummy ya shigo sai da gabanshi yadan fad'i kasancewar yasan ya barta da mai lalura a gida , da sauri ya d'aga dan dama shima yana jiran ya d'an samu saukin aiki ne ya kira su yaji ya Asman take, haka yakeyi kusan duk inya fita bayan wasu y'an awanni sai ya kira yaji ya take, ko amsa sallaman ta na kirki baiyi ba ya shiga tambayar ta Asmah da lafiyar ta, murmushi tayi mai sauti tare da cewa "To daddyn Asma'u kyakkyawan labari, amma sai an bani goron albishir." Jin yadda take ta sakin murmushi yasa ya tabbatar lallai abin mai girma ne, cikin d'an yanayin za'kuwa yace "fad'i duk abin da kike so zan baki." Tace "ka tabbatar." Yace "In kina so sai na rantse." Tace "ba sai ka ranste ba, goro na shine (No kishiya in my hause)." Dariya yayi yace "har kullum kedai zancen ki kenen, kuma na sha fad'a miki tunda kuruciyar mu kin isheni riga da wando rayuwar duniya A'isha ta." Dad'i taji ya mamaye mata zuciya cikin yanayin farin cikin da take ciki a yau tace "nagode sosai mijina abin alfaharina." Yace "yanzu dai duk ba wannan ba, ki Adana min wad'an nan dad'ad'an kalaman naki sai na dawo gida, fad'a min albishir dina dan wallahi na 'kagu naji." Dariya ta shiga yi mai, cikin son taja mai rai, sai da taga ya koma rok'on ta cikin marairaice murya kamar zaiyi kuka, sannan tace "Asma'u ta haihu." Zaro ido yayi tare da cewa "wacce Asma'un, kee! A'isha bana son irin wannan tsokanar, dan Allah." Tace "wallahi ta haihu kuma yaya uku rerass." Nan fa Daddy ya k'ara yarda cewa lallai tsokanar shi take, duk da yasan cikin Asmah ya wuce watan haihuwa bai taba bata haihuwa yau ba, saboda garau ya baro ta gida baiga wani alamar nak'uda a tare da ita ba, kuma da fitar shi da kiran wayar mummy tace mai Asmah ta haihu duk baifi awa biyu ba, jin shi shiru yasa mummy katse kiran ta, tasan dole zai kira kokuma ya biyo baya dan ya tabbatar, bayan daddy Ummi ce next da mummy ta kira sannan Mami, duk wanda ta gaya wa Asmah ta haihu sai ya karya ta, Mami ma ko katse wayar basuyi ba sai gata a part d'in mummy da ta diro kamar daga sama, tana tabbatar wa kuwa ta shiga murna tana hamdala kamar ta taka rawa dan farin ciki a wani bangaren kuma tana al'ajabin yadda wannan lamarin ya kasance, can kuma ta shiga kiran su batool d'aya bayan d'aya tana fad'a musu. Mummy da kanta ta je ta sanar wa hajiya mama da alhaji baba, aiko tare suka dawo part din ta da hajiya mama, kan kace kobo magana ya karad'e family Asmah ta haihu yan uku, duk wannan bidirin Aslam bai da labari dan mummy bata kira shi ba Mami kuma tayi tunanin mummy ta gaya mai shi yasa bata kira shi ba. Ya gama shirin shi na tafiya office kenan suna sallama da zee yana ce mata zai biya yaga jikin Asmah kafin ya tafi, ita kuma tana bashi sallahun gaisuwa wayar shi tayi ringing, Amir ne mai kiran hakan yasa bai bata lokaci ba wajen daga wa, daga can bangaren Amir yace "angon k'arni angon k'arni congratulation d'an uwa, yanzu Abba ke kira na wai Asmah ta sauka, gaskiya baka da kirki shine ka kasa kira na sai Abba ne ke gaya min." Duk wannan surutan na Amir tuni Aslam ya dena fahimtar shi dan karshe ma dauke wayar yayi daga kunnen shi yana sake maimai ta kalaman Amir, wai Asmah ta sauka, sai ya rasa ma wani irin sauka yake nufi to, bai gama wannan mamakin ba wani kiran ya sake shigo wa daga Dr bash shima dai congrat yake mai, wannan karan dai dakatar da Amir yayi da cewa "kai dan uban ka yi min dalla² wacece ta haihu wai kuke ta rigar rigen kira na zaku rudar dani." Daga cen bangaran Dr bash yace "wai kai a komai saika saka iskacin ne? kana da wata mata Asma'u ne banda Asmah bamu sani ba, nima ina hospital yanzu teema ke kirana wai Asmah ta haihu yan uku yanzu Mami ta kira ta itama ." Duk wannan bayanin na bash ma iska yake yi, dan tuni Aslam ya katse kiran ya nufi gurin mota cikin sassarfa yama manta tsaye suke da zee da little sai da yaga sun biyo bayan shi, bai amsa tambayar da zee ke mai na cewa meke faruwa ba sai cewa yayi ta shigo su tafi. A tare suka iso da Daddy, bayan sunyi parking gaisawa suka tsaya yi har kasa zee ta tsuguna ta gaida da daddy a mutumce shima cike da kulawa ya amsa mata tare da kamo hannu little mikewa tayi ta nufi part fin Mummy inda tasan Asmah take, gaisawa sukayi da Aslam bayan tafiyar zee, daddy yace "baka tafi office d'in ba bayàn wannan uwar lattin da kayi, har kullum kai baza ka canza ka daina wasa da aikin ka ba. Wanan inda a wani wajen kake aiki ba gida ba da tuni sun manta sun Dade da korar ka." Yana Sosa keya yace "Ayi hakuri daddy wlh wani labari naji mai kama da almara shine na biyo dan na tabbatar." Daddy yace "Au harda kai takira Ashe , to mu karasa ciki muga zahiri." Falon mummy cike da mutane tuni batool, da Khadijah, sun karaso kowacce da danta yayan sun zama yan samari dan suna neman shekara bibbiyu kenan, ga hajiya mama ga Mami ga Abba ga kamal ga ya Rabi'ah kai falo dai cike da mutane ga kuma makota ga kawayen mummy na kusa, zee na shiga batool ta d'ebe ta ta watsar tare da maida kai gefe har gobe bata kaunar zee duk da kuwa irin yadda zee din ke nuna mata kulawa, Mami ce ta fara mata lale da barka tana ga uwar yan uku ta karaso, itama wurin mamin ta nufa dan a nan taga fuska, a mutumce ta gaggaisa da mutanen falon gaba daya harda su batool daya kamata ace su suka gaishe ta, yadda tayi gaisuwar a mutunce haka suka amsa mata da kulawa suna yi mata barka masu tsokanar ta nayi irin su hajiya mama da Mami, ita dai amsa barkan kawai takeyi ba tare da tasan na menene ba, cikin haka Aslam da daddy sukayi sallama nan kuma aka shiga wani sabon gaisuwar da barka barka ,daddy yace "wai kuna nufin da gaske ne kenan Asma'u ta haihu." Hajiya mama tace "kwarai kuwa d'an nan ga zahiri kana gani, Allah ya amshi addu'a ya kawo wa yarinya abu cikin sauki haka lamarin gwanin dad'i." Daddy yace "Allahu akabar Allah muna gode maka daka amshi addu'an mu, ina dan tselan uwan yake na zuzzuge shi da carbi ladan wahalar min da y'a da yayi duk da dai a karshe an rabu kalau." Mummy tace "d'an tselan uwa ko yan tselan uwa, suna ciki suna baccin gajiya, to an zaunu a ciki wata goma sha d'aya fa." Zaro ido daddy yayi yace "wai kina nufin da gaske ukun ne ba zolayata dama kike yi ba." Yadda yayin ne gaba d'aya ya basu dariya suka shiga darawa. kamal ne ya budo hotonsu da Khadijah ta dauka d'azu da ta shiga ganin su ya mik'a wa daddy, kabbara da kirari daddy ya shiga jerowa ubangiji yana kara gode mai a bisa wannan gagarumin kyauta daya basu, first in history a zuri'ar su, an haifi y'an uku, yana kara kallon su yace "to wai wasu iri ne naga dai wannan mai d'an kumatuttukan nan kamar fanke, kamar macece." Ya fada yana pointing d'aya daga cikin su a jikin screen din faskeken wayar kamal, dariya duk suka saka mummy tace "wato itace amaryar tawa kenan ko? To duka yan mata ne kwantar da hankalin ka, sai ka darje." Aslam kam tunda suka shigo falon yaga an shiga haya baya ya samu ya lallaba yashige dakin Asmah ba tare da kowa ya kula da shi ba, suna kwance daga ita har yaran barci suke yi, tunda ya tura kofar ya hango su, zuciyar shi ta shiga dukan uku uku ji yake kamar a kan iska yake tafiya lokacin da yake karasawa gaban gadon dukewa yayi ya zuba musu ido kamar bai ko keftawa kamar wanda ya warke makanta kokuma wanda bai taba ganin jarirai ba, a fili ya furta "yanzu wadannan duka nawa ne ni Aslam, duka nan mallakina ne." Sai kuma yaji hawaye farin ciki ya ziraro mishi, durkusawa yayi a gurin ya gabatar da sujudulsh- shukur, yana dagowa ya koma gaban yara ya tsura musu idanu yarane kyakkyawan gaske kamar y'ay'an larabawa kama suke yi sak da juna kamar an tsaga kara manya dasu kamar ba yan uku ba, a hankalin ya ringa ba kowacce peck a goshi yana yi mata addu'a yana tofawa, sai da ya gama dasu ya maida kallon shi kan Asmah tana kwance tayi fiyaut da ita, wani irin haiba da annuri yake gani yana fitowa daga fuskar ta, sai ya ga ta wani kara mishi kyau sosai a idanun shi, karasawa yayi daidai saitin face din ta, a hankalin ya shiga saukar da kanshi yana son ya subaci labbanta da yaga sun kari yi mai wani pink kamar ta shafa jambaki, bai kai ga hade bakin nasu ba mummy ta turo kofar ta shigo da sauri ya janye fuskar shi, amma abinka da mara gaskiya ganin yadda yayi wuri wuri yasa ta harbo shi a kallo daya, daure face tayi tace "To bismillah faruwa da iyawa, to tun wuri bari na gaya maka bazan laminci wannan iya shegen ba, idan na dauki na Amir naka kam bazan dauka ba danshi na mishi uzirin ita kadai gareshi kai kuwa fa? Wai da yaushe ma ka tsallakemu a falo ka shigo nan." Ta karashe maganar cikin tsatstsare shi da idanun ta, Sosa keya ya shiga yi yana yan kame kame, tace "maza ka fice min da gani,ka karasa kama Dr iso yazo zai duba su ita da yaran." Dr nasidi ya duba ta sosai ya mata dinki danta samu tear sai da ya tabbatar babu wani sauran matsala sannan ya rubuta mata magunguna, ya duba yaran suma sannan aka fitar dasu aka ba kowa ya dauka cike da farin ciki sai hotona ake musu wasu na daurawa a media masu sakawa a status nayi masu tura a Facebook nayi kai harda su tiktok da Insta sai da kamal ya daura, (yan dama ta biyu fans masu yin tiktok a hya kallo lahiya😂 in kunyi kwa dauko mana mu gani muma.)