← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 126

Sashe 33

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zee kam hannu ta shiga mika ma aslam numfashinta na wanj irin fusga idonta na lumshewa, lokaci daya ta fede , ta rame ta ƙara fari fat,

Zuciya Ce ta debe shi ya karasa gabanta a fusace ya dagota ya hada ta da bango ya shaqe cikin fitar haiyaci yake cewa" meyasa kika zubar min da gudan jinina , mai na miki zaki sakamin da wannan mummunan sakamako, me jinina ya miki zaki salwantar min da rayuwar shi kika sani ko shi kenan kwaina a duniya, kin cuceni zee tsakani na dake Allah ya isa, ki gayamin wani likitane ya miki wannan aikin ,wa kuma ya baki wannan gurguwar shawaran ,ki fad'a min domin daga ke har duk wani mai hannu a cikin salwantar min da gudan jinina bazan barshi ba na rantse da Wanda raina ke hannun sa "

Zee kam tun taba zazzare ido , har jikinta ya saki numfashinta ya dauke ta sume, yana ganin haka yayi wurgi da ita ya shiga toilet ya ciki ruwan sanyi a katon bokiti ya sheka mata, take ta shiga sauke ajiayar zuciya,

Ganin ta farka yasa ya kara cin kwalarta yace"tambayarki nakeyi keda su waye kuka salwantar min gudan jinina" cikin kuka ta bude baki tana magana amma tsabar azaba maganar ma bata fita sosai,

Ganin taƙi bashi amsa yasa ya ya shiga gwada kanta da bango yana marinta , saida ya mata dukan tsiya ta ƙara sumewa , ya yasar da ita a wajen ya tsallaketa ya wuce,

Dakin shi ya shiga ya hada kayanshi kaf a cikin trolley ya fita ya shiga motar shi ya bar gidan da mahaukacin gudu,

Me gadi kam tun ganin yanda ya shiga gidan d'azu da gudu yasan ba lafiya ,wani Abu Mara kyau na faruwa,ganin fitar Aslam a haukace jikin shi duk jini, yasa da gudu ya nufi falon yana shiga yaga zee a sume ga fuskarta duk a kumbure ga jikinta duk jini, sallallami ya shiga jerowa kafin kuma ya fita da gudu ya debo ruwa ya watsa mata,

Aslam kam direct family hause ya nufa saida yayi horn mai gadi ya bude mai get kuma ya masa qarsawa cikin gidan, tsayawa yayi yana tunanin ta yadda zai saka kafar shi a cikin gidan yau..............

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabilillah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Page 67 & 68

A galabaice ta shiga sauke numfashi, idanunta arufe , me gadi kam daura hannu yayi aka ya shiga fareti, shikam yau ya shiga uku ya zaiyi da rayuwar sa ,

Fita yayi da gudu makota, ya shiga buga musu get, me gadin Gidan ne ya taso ya bude mishi, kasancewar sunsan juna, nan ya shiga rattabamai abin da ke faruwa, shima cikin jimami ya nufi cikin gidan, hajiyan gidan ya samu ya gaya mata abin da, me gadin .gidan Aslam ya gaya mai,

Hajja fati Macece mai tausayi, dattijuwa ce bata da miji, saidai tanada yaya manya maza da mata, wasunsu ma sunyi aure, anan take zaune,yar gata ce, dan ba abinda yayantsa basa mata, kuma itama metro ce a general hospital,

Cikin tashin hankali ta zari hijabinta ta bi bayan shi, har cikin falon mai gadin gidan Aslam ya mata jagora,

Ganin halin da zee ke ciki yasa hankalinta ya qara tashi, kallo daya ta mata ta gane inda matsalar take kasancewar ta babban ma'aikaciyar jinya mai matsayin metro, dagata tayi ta shigar da ita toilet din dake falon ta hada mata ruwan dumi ta saka ta ciki,

Sosai ruwan ya ratsa zee, take numfashinta ya fara daidaita ta fara bude idonta da suka lumshe, don batasan inda kanta yake ba ,

Saida ta gasata da kyau, ta barta a toilet ɗin tace ta lallaba tayi wanka, suje asibiti taga Dr,

Fitowa hajja fati tayi ta shiga gyara falon ,duk inda ya baci, saida ta gogeshi tas ,koda ta gama zama tayi a falon tana jiran zee, shiru shiru zee bata fito ba don haka ta tashi ta leƙa toilet ganinta tayi a zaune a toilet din ta gama wankan ta daura tawul amma fitowa ya gagareta domin baza iya tafiya ita kaɗai ba jiri take ji sosai,

Kamata hajja fati tayi suka fito daga toilet ɗin zaunar da ita a falo tayi ta haura sama ta duba ɗakinta ta dauko mata kaya marasa nauyi , dubawa tayi bata samu pad ba don haka ta aika mai gadi ya siyo musu , bata tayi ta saka, ta saka kayan sannan ta ce ta jirata ta dauko mota suje asibiti,

Duk abinda ke faruwa zee hawaye takeyi, tana sauke ajiyar zuciya, ta kasa tsaida hawayen dake bin idanunta, ta ƙudiri aniyar ko Aslam ne autar maza ta rabu da aurensa , tunda ya saka hannu ya mata irin wannan bugun dan kawai ta zubar da ciki,

Tayaya akayi yasan ta zubar da ciki waya faɗa mishi bayan daga ita sai beebalo sai allah suka san da wannan zancen,

Lallaɓawa tayi ta miƙe daƙer ta dauki wayar ta ta kunna , lambar dad ta kira, yana ɗagawa ta fashe da kuka tace "dad zai kasheni , dad kazo ka rabani dashi bana sonsa na fasa auren dad zan koma na zauna tare daku,kazo ka daukeni kar ya kashe maka ni"

Dad cikin tashin hankali yace"daughter meke faruwa, waye zai kasheki , " cikin kuka tace "Aslam ne" nan ta labarta mishi abin ya faru , aiko ran Dad in yakai dubu ya baci,take fuskar shi tayi jajur zabar bacin rai har wani tiriri yaje jin yana fita daga kunnuwanshi, nan ya shiga aunawa Aslam zagi da ɗiban Albarka kafin daga karshe yace ta bi hajja fati zuwa asibiti, kuma tasa idon ganin shi a nigeria nan da wasu ƴan awanni, zaizo saiya koyama aslam hankali, saiya gwammace da bai taba haɗuwa da ke a duniya ba ,

Karfafa zuciyar shi yayi ya rufe ido ya danna kan motar shi cikin gidan, yana parking ya fito, ina zai dosa yanzu , part din mami, haka zuciyar shi ta umarce shi, can ɗin ko ya tunkara,mami tana ganin shi tasan ba lafiya ba daga yanayin da taga fuskar shi a mugun hade idanun shi jajir, can kuma ta lura da jinin daya bata mai jiki,

Innalillahi wainnailaihi rajiun ta shiga maimatawa kafin da sauri mami ta iso gareshi ta mika hannu ta rike mai hannayenshi, cikin tashin hankali ta shiga furta "my son meya faru, meya sameke , daga ina kake haka, meke faruwa"

Zaunar da ita yayi akan cushion shima ya zauna suna fuskan tar juna, a hankali ya bude baki yace"mami me na mata da zata saka min da irin wannan mummunan sakayya, mami na cancanci haka daga gareta, mami zee ta zubar min da cikina dake jikinta," cikin kaduwa mami ta shiga sallallami, tana tafa hannaye,

Tace "garin yaya ta zubar da cikin kun samu wani sabani ne" yace " wlh mami ba abinda ya haɗani da ita, to mami imma wani Abu ya hadani da ita saita zubar min da ciki" mami tace"kai waya gaya maka, yanzuma ina zainab din take", kwashe komai yayi ya gayama mami tun daga message din da beebalo ta turomai har zuwa wutowar shi nan gidan, amma bai gaya mata a sume ya wuto ya bar zee,

Shiru mami tayi cike da tausayin shi hawaye ya cika mata idanuwanta,

"Yanzu kaje kayi wanka ka canza wadannan kayan da suka lalace, sai kazo musan abinyi, miƙewa yayi zuwa part dinsu, direct dakin shi ya shiga domin yayi abinda mami ta umarceshi,"

Yana wucewa mami tabi bayanshi da kallon tausayawa, gsky Aslam baiyi sa'ar mace ba, a dan shekarun shi wadanda da kaɗan suka haura talatin , yana fama da irin wanan kalubalen Rayuwa kala kala, ga rashin dacen mata, ga kuma soyyaya na dawainiya da zuciyar shi , da tana da iko da babu abinda zai hana ta aurawa Aslam Asmah a karo na biyu, kozai samu saukin Rayuwa,

idan ya auri Asmah ya rage wani matsalar daga cikin mastalolin rayuwar shi ,

sai yaji da batun zainabu , amma tasan bata da wannan ikon, Abu daya ta San zata iyayi, shine tausa kamal ya janye daga neman auren Asmah ya barma Aslam, a matsayin ta na mahaifiyar shi,

to tasan ko tayi haka tayi a banza, tunda dai ta Riga tasan wanene mahaifin mijinta wato alhaji baba , kaifi ɗaya ne baya magana biyu idan yace yes ta zauna haka zalika idan yace no, shima ta zauna,

mutum ɗaya ne take da tabbacin duk fadin duniyar nan zai iya canja maganar alhaji baba, amma duk da hakan baza ta zuba Ido kawai ba, zatayi wani Abu akan lamarin,

Koda yayi wanka kwanciya yayi a dakin yana nazarin abinda ya faru yau tundaga farko har karshe, koda yazo kan beebalo diga ma lamarinta question mark yayi,❓zai binciketa don bai yarda da ita sosai ba, idan ya gano da hannunta acikin wannan lamarin zai hukuntata hukunci mai tsanani ba ita kadai ba, da koma wanene , mai hannu akan salwantar mashi da gudan jinin shi ,

Haka ya zauna yayi ta saƙe saƙe , ko sallan magriba da isha, a ɗakin yayi bai fita ko ina ba, babu Wanda yasan ya kwana a gidan hatta mami tayi tsammanin ya fice daga gidan ne,

duk Wanda yaga motarshi baya kawo kamai a ranshi, daddy ne ma daya dawo da daddare yaga motar yadan zargi wani Abu, koda yama mummy maganar tace baizo ba saidai ko amir ne ya kawo motar gidan, bai wani gamsu ba , yadai barshi da niyar da safe zai tambayi mai gadi,

Washe gari da misalin karfe biyar na asuba jirgin da Dad ya biyo daga Malaysia zuwa Nigeria yayi landing a airport na garin minna, direct kuma general hospital direban da yazo daukar shi ya wuto dashi,
Chapter 33 · 0% Book details