← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 126

Sashe 72

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nan kuma taji cikinta kamar wacce ta kwana uku bata ci komai ba tsabar yunwa har jikinta na rawa, dauko mata sauran banbaran ta sukayi, amma tana kallon shi wani yunkurin amai ya taso mata ba shiri suka ɗauke, ga dai yunwa tana ji kamar ta mutu, saidai ba komai zata iya ci ba, Afnan tace"anty batool to me zakici, ki fadi abinda kike so na girka miki yanzu yanzu" a wahalce tace "ki duba kitchen akwai cabbage ki dauko min dan Allah" a haɗa miki coslow ne kokuma a miki kwaɗan shi da kuli kuli, batool tace"ki kawo min shi haka kar ki haɗa da komai" cikin mamaki tace "haka gaya zakici" tace "eh, dan Allah kiyi sauri, ba sai kin tsaya yankawa ba a kawo min shi haka"cikin minti biyu ta kawo mata cabbage din ta saka wuka ta raba shi hudu ta wanke ta ɗauro mata guda ɗaya akan tray, wawura tayi ta kai bakinta ta fara gabza kamar wata mayunwaciyar akuya, kan kace kobo ta cinye tace a karo, ɗaya aka karo mata shima cikin kankanin lokaci ta gama dashi tasha ruwa tayi gyatsa, zuwa lokacin kam ta koma ba su Afrah tausayi, dan duk tagumi sukayi da hannu bibbiyu suna kallonta, nan kuma cikin yan mintuna bacci yayi awon gaba da ita, haka su Afnan suka tsaya suna kallon ta kamar tv, can kuma wayar Afrah yayi kara dubawa tayi taga, yayansu ke kira da sauri ta daga, kafin ma yakai ga tambayar ta , ta shiga labarta mai abin da ke faruwa, shi kanshi saida yaji wani irin tausayin ta, sallama sukayi yace indai ta tashi su kira shi su haɗasu ta waya,wani uzuri ya rike shi sai yamma zai dawo, baccin ta tayi sosai bata ko juyi, kamar wata matacciya, har akayi azahar bata farka ba ,su kuma basu tasheta ba , sai daf da la'asar ta farka, basa ɗakin duka suna falo, lallabawa tayi ta tashi ta ɗauro alwala tayi sallan azahar da na la'asar gaba ɗaya.

Bayan ta idar kuma ta fito falo,sai sannan suka San ta tashi, sannu suka shiga jero mata,murmushi kawai ta iya sakar musu, Afnan tace "anty batool yaya ya kira ɗazu kina barci yace idan kika tashi, a haɗa ku a waya" tace "OK ina zuwa tukun" ta faɗa tana nufar kitchen, sai gani sukayi ta fito hannunta dauke da plate shake da gayan kabeji, da idanu duk suka binta, bata kula dasu ba ta nemi guri ta zauna ta hau cin kayanta har wani lumshe idanu take tana mai mai da baki,saida ta take abinta Tass tasha ruwan ta ma'ishi, sannan ta kalle su tace "yadai naga an zubo min na mujiya ne" Afrah tace"Ai dole anty batool Allah dai ya raba lafiya" tabe baki tayi sannan tace "amin" ita fa har zuwa wannan lokacin bata San tana da ciki ba, maganar su Afrah bai sa ta gane komai ba duk a tunanin ta don sunji maah ta faɗa rannan ne yasa suma suke faɗi.

Nan suka shantake a falon sunata fira, har zuwa wajajan karfe shidda , saida sukaji karan horn din motar Dr sannan suka tuna yace a haɗa shi a waya da batool.

Bakinsa dauke da sallama ya shigo falon, da sauri Afnan ta amshi jakar hannunshi, har suna haɗa baki wurin yimai sannu da dawowa, cikin sakin fuska ya amsa musu.

Tunda ya sanyi kanshi cikin falon daddaɗan kamshin turaren da take maitar son ji ya ziyarceta, lumshe ido tayi tana shaƙa, wani irin natsuwa da kwanciyar hankali taji yana ziyarceta a lokaci guda, karasowa cikin falon yayi idanunshi akanta, har ya isa daf da ita bata da labari, saida taji kamshin ya ƙaru sosai a hancinta sannan ta buɗe idanu, abinda taji ɗazu da safe game da shine still yanzu ma ta ƙara ji, na yanzu ma har yaso yafi na safen, tsikar jikinta gaba ɗaya ya tashi, kamar ya fahimci halin da take ciki hakan yasa ya kalli su Afrah yana kallon agogo yace "oya kumuje na saukeku a gida kafin magrib," duk da ba haka suka so ba amma cikin su babu Wanda keda zarran yi mai musu, dole suka amsa masa da to, kallon batool yayi yace"bari na sauke su daga nan zan tsaya nayi sallan magriba,me zan siyo miki "budar bakin ta tace cabbage, "cabbage" ya maimaita abinda ta fada gyada mai kai tayi, har zai kara yin wani magana ko mai ya tuna kuma, ya fasa, su Afrah sallama suka mata tace su gaida maah, haka nan cike da kewar juna suka wuce.

Suna wucewa aka ana fara kiraye kirayen sallah, tashi tayi, ta daura alwala anan toilet din falon, a nan kuma falon tayi sallah.

Lallaba tayi ta koma dakinta ta kwanta, tana ta tunane tunanin make faruwa da itane haka, me yasa take jin haka game da Dr bash, Wanda da ko kaɗan bata jin haka daga gareshi, hasalima ita tsoran lamarin take, amma daga safiyar yau zuwa yamma duk inta daura idanunta a kanshi, sai taji wani mugun feeling dinshi ya taso mata, ɗazu ma matukar dauriya tayi bata rungume shi ba saboda ganin idanun su Afrah, ita dai fatan ta Allah yasa ba wani ciwo bane ya kamata.

Bayan ya sauke su Afnan a gida suna tafe suna bashi labarin yadda batool ta dinga cin gayan cabbage da kuma yadda tasa aka kwaso duka turaren sa, yana sauraren su wani nishadi na musamman na ziyartar shi, daga nan masallaci ya nufa yayi sallah, sannan ya nufi Neman cabbage duk inda yasan zai samu, cabbage yaje duk sun tattashi, saboda dare daker ya samu wani mutum yayi mashi kwatancen wani waje a kasuwan gwari, ai ko dai ya tula da yawa dan kusan manyan kwallo goma ya jidar mata, koda ya kamo hanyar gida isha,e ake kira dole ya samu guri yayi sallah sannan ya karaso gida.

Tana kwance kan pray mat din da tayi sallan isha,e, taji diran motar shi, wani daɗi ne ya lullubeta ko ba komai zata samu ta shaki kamshin da take so, bata gama wannan tunanin ba taji shi yana sallama a bakin kofar ɗakinta, da sauri ta yunkura ta tashi zaune, tana bubbuɗe kofofin hancinta jira take kawai taji saukar kamshin sa a hancinta.

Aikam dai ko minti bai kara ba ya ziyarceta, wani wahalallan ajiyar zuciya ta sauke, tana kara daddaga hanci, tun shigowar shi idanunshi ke kanta duk abinda takeyi yana karantar ta tsab.

Hankalin ta yayi nisa wajen shakar kamshin sa, bata ko kula ba har ya ƙaraso cikin ɗakin ya zauna bakin bed, ganin dai ta shagala da yawa yasa yayi gyaran murya, da sauri ta juyo ta kalleshi, yarr yarr haka ta dinga ji a jikinta, idanunta kawai ya kalla ya harbo girkinta kaf, ya gama fahimtar komai, wato dai kakar shi ce ta yanke saka.

Ya fahimci irin cikin nan Allah ya bata mai saka jaraba, hakan kuwa ba karamin dadi yamai ba shikam ai gaba ta kaishi, shi yana gani ma addu'an da ya tayi ne na Allah ya taro mai ita, Allah ya karba ya taro mai ita cikin sauki ta wannan hanyar.

Fuskewa yayi ya dauke idanshi a kanta yace "ya jikin naki," tace da "sauki" tana binshi da wani irin mayen kallo, yace "to alhmdllh tunda da sauki ni zan wuce ɗakina, cabbage dinki yana kitchen" ya faɗa yana mikewa ya nufi hanyar waje, kasa daurewa tayi, take taji a jikinta idan bata rabi jikinshi ko yaya bane nunfashin ta zai iya daukewa, bata San sanda ta mike ba saidai ji yayi an mai wata irin kyakkyawan runguma ta baya, ta daura kanta a bayanshi tana sauke ajiyar zuciya, hannayenta gaba ɗaya ta zagaye cikin shi dashi.

Daskarewa yayi a wajen dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, baiyi wata wata ba kuwa ya zagayo da ita gabanshi ya haɗe bakinsu guri ɗaya, ya shiga kissing dinta a zafafe, batool bata taba sanin ta iya kiss ba saida ta tsinci kanta da mayar mai da martani baiwar Allah jikinta har rawa yake yi, tafiya tayi tafiya lamarin ya wuce na tsayuwa, daga shi har ita basu San yadda akayi suka isa kan bed ba, cikin kankanin lokaci ya rabata da duk wani sitira na jikinta, bai tsaya bata lokaci ba ya dauki hanya, don a yadda ya lura idan yace zai kara wasu mintuna kafin ya shigeta zata iya zaucewa, shi har tausayi ta bashi yadda take abubuwan yasan ba yin kanta bane, abin fa har tsoro yaso ya bashi, amma tunawa da yayi akwai mata da yawa da ciki ke maida su jarababbu, sai ya ajiye tsoron shi a gefe yaci gaba da gashi.
Chapter 72 · 0% Book details