Sashe 52
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ganin taki amsawa tana mishi wannan kallon nata dake sage mai gwuywa, yasa cikin faɗaɗa fara'arsa yace"kina bukatar, abincin breakfast ne, ai nama riga na girka miki, nasan zakiji dadin girkina sosai muje dining nayi serving dinki kinji baby na" ya karashe maganar yana kokarin riko hannunta, bige hannun shi tayi tare da banka mai harara, kafin taja tsaki ta juya ta bar shi nan tsaye.
Falo ta dawo ta zauna, ganin shi da tayi da safen nan gaba daya taji ranta ya baci, zuciyarta tayi kunci, kwata kwata bata bukatar ganin fuskar shi a halin yanzu, ada tana jin haushin shine saboda irin musguna mata da yayi a baya,ya nuna mata tsantsar tsana da tsantsar kiyayya,
Hakan yasa itama tamai mugun tsana mai tarin yawa, amma a yanzu tanajin haushin shi akan rabata da masoyin ta na gaskiya da yayi, tasani shine ya mata shamaki da auren zabin zuciyarta, wai yana sonta ta ya ya zata yarda da wannan tatsuniyar gizon, Ai ko duk jikin ta kunne ne baza ta taba yarda da hakan ba, karya ce kawai yaudarace, kuma Allah ya fishi ta Allah ba tashi ba.
Shikam tana wucewa ya bita da kallo yana sakin murmushi, ko kadan hakan bai bata mai rai ba saima wani mugun kyau da yaga hararan ya mata, shida zai samu ma ta dinga mai irin wannan hararan ai zama zaiyi ya dinga kallonta kamar TV, da sauri ya biyo bayan ta zama yayi a gefenta, yadan karkato ta yana fuskan tarta, cikin lallashi yace"baby na debo miki abincin na kawo miki nan ne," share shi tayi kamar batasan Allah yayi ruwan mutum a wajen ba, bai daddara ba ya kara cewa "to ko na hada miki tea ne, na dafa miki ruwan shayi mai peppermint, nasan kina sonshi sosai ko" nanma shiru tamai bai damu ba yaci baba da cewa " to in baki son su duka ki faɗa wani abinda kike so saina girka miki," shiru again, mararaice murya yayi yace "don Allah my husnah ki bude bakin ki kimin magana naji muryar ki hankalina ya kwanta,dan Allah, ko zagina ne kiyi, shirun ki a gareni tamkar poising ne".
Gaba daya ya gama takura rayuwarta itafa duk wani Abu daya shafi Aslam bata son shi, a yanzu, maganar nan da yake mata ji take kamar yana diga mata ruwan dalma a zuciya, fahimtar da tayi sonjin muryarta yake kamar hauka, yasa ta kudiri aniyar saidai ya mutu amma ko shekara zaiyi yana mata magana baza ta tanka ba, kai ko zaginta yayi zata iya daure wa dadai ta bari yaji muryan ta da yake maitar son ji.
Zuciyar shi ce ta bashi shawara kan yajeya debo abincin ya biyo ta dashi nan wata kila inta ganshi taci, tsam ya mike ya nufi dinning ya shaqo plate da doya da kwai ya kawo ya ajiye a gabanta ko kallon inda plate d'in doyan yake batayi ba, sake komawa yayi ya hado mata tea ya kowa, ganin tana nan yanda ya barta ko fallon abincin batayi ba yasa ya dauki plate d'in ya zauna daf da ita ya dago doya daya a hannun shi ya kai kusan bakinta yace"haaa my husnah na ciyar dake da hannayena har sai kin koshi," shiru ba amsa, kara matsawa da doyan yayi daf da bakinta har yana dan mannuwa da lips dinta, ranta ne taji ya kara baci,a zafafe ta mika hannunta ta bangaje hannun shi, da karfi , take plate d'in doyan ya kufce ya watse a falon, tashi tayi ta banka mai harara, taja dogon tsaki, ta tsallake shi ta wuce ciki abinta.
Binta yayi da kallo har ta bace ma ganin shi, murmushi ya saki yana girgiza kai, ko kadan baiji haushiba saima wani burge shi da ta kara yi.
A haka suka kwashe kwana uku,ba wani sauyi har zuwa lokacin kuwa Asmah bata taba cema Aslam ci kanka ba, yayi nacin jin muryar ta harya gaji, girki kuwa haka zai mata na safe ya mata na rana da daddre ma ya mata, amma bata taba ɗanɗanawa ba koda wasa, shi kuma bai fasa yi ba, kuma bai taba gani ta shiga kitchen da suna girka wani Abu dan taci, baisan me take ci ba, a ɗan kwana ukun nan idan kuka ga Aslam duk ya sukurkuce ya zama wani iri sai rama yake karawa, dama bai gama maida jikin shi ba, na ciwon da yayi.
Yau kam da suka cika kwana hudu tun safe yake zarya kofar dakin ta yana knocking, tun safe bata fito ba balle ya samu ya ganta, har gashi karfe ukun rana ake nema, gaba daya hankalin shi ya tashi gashi yayi yayi tayi magana taki, ko waya zata yi dasu zahra ko mummy kasa kasa takeyi da murya don kar yaji.
Da gangan taki fitowa yau kwata kwata, abincin kam cincin da cake dasu dublan da soyayyen naman da take dasu a dakin su takeci tasha ruwa abinta, tanajin shi yana ta magiya amma ta share ko kadan bai fara bata tausayi ba, gajiya yayi ya silale anan kofar dakin nata ya zauna ya hade kai da gwuiwa.
Zuciyarta Ce ta bata shawaran cewa , me zai hana kiyi amfani da wannan daman da Allah ya baki akan Aslam ki rama duk cin zali da musgunawan da ya miki a baya, ki bautar dashi ki maida shi abin tausayi, yanda baiji tausayinki ba kema karkiji nashi, take kuwa tayi na'am da wannan shawara na zuciyarta, murmushin keta ta saki a fili ta furta"Aslam ka shiga uku dani, dame zan fara ne" ta tabayi kanta, murmushi ta saki tunawa da tayi da wankin ta data dan tara don tunda tazo gidan bata yi wanki ba, kwasa tayi ta cire kakkauran zanin gadon dake kan gado da bargon shi ta hada da kayanta kusan kala bakwai ta tattaro harda kyar take dauka ta bude kofar, abin tausayi yana zaune ya hada kai da gwuiwa yana gyangyadi, ji yayi kawai an watso mai tulin kaya a kai ba zato ba tsammani, firgigit ya bude ido tare da dago kanshi, saidai ganin ta yasa shi sauke wani ajiyar zuciya, kafin ya shiga sakar mata murmushi, kallon shi tayi a yatsine, kafin ta bude baki cikin yauki da yanga tace"ga kayana nan ka wanke min su kuma yau nake bukatar su ka gane ko" wani dadi ne ya lullubeshi maimakon yaji haushi jin muryar yau yafi komai yimai dadi, take jikin na rawa ya kwashi wankin ya ya shiga toilet din dake falon ya fara wanke wa a washing mashin yanayi yana jin wani nishadi na musamman, yau husnah ta bukaci ya mata wani abin wayyo dadi, shi wlh ko abinda yafi wanki zata saka shi zaiyi, haka ya gama wankin nan yaje ya shanhsanya su a waje ya dawo.
A falo ya sameta cike da dauki yana washe baki ya shiga sanar mata cewa ya gama wankin ya shanya, kallonshi tayi ba yabo ba fallasa tace" ka kyauta ma kanka" iya abinda tace kenan ba godi bare nagode, shiko ko a jikin shi a ganin shi Ai hakan wani ci gaba ya samu tunda gashi tana mai magama kuma ta sakashi aiki, shidai hakan yafi mai alheri akan shirunta a gare shi, zama yayi a gefen ta, ta juyo ta kalle shi tace, "pls ka koma ta cen" ta fada tana nuna mai kujeran nesa da ita sosai, ba musu kuwa ya tashi ya koma, shiru ne yadan ratsa tsakanin su, can ya dubeta yace "abincin ki na kan dining tun dazu na girka ko na kawo miki nan ne," dagowa tayi ta kalle shi cike da yanga da jan aji tace" zubo mi gani ko zan iya ci" tashi yayi jiki na rawa yau tace zataci girkin shi, yaje ya shakaro plate da jellop din shinkawa , yako hadu ko a ido, sai tashin kamshi yakeyi, mika mata yayi , ta nuna mai gabanta tace ajiye a nan , ba musu ya ajiye ya koma wurin zaman shi na dazu, daukar abincin tayi ta kai cokali daya bakin ta, ta fara taunawa abincin yayi dadi ba laifi a matsayin shi na namiji ya girka shi, yayi kokari sosai, amma dan wukakanci furzar dashi tayi tana ɓata fuska, shiko tsuru yayi yana kallonta , cikin bata rai tace"wannan wani irin girki ne haka ba dadi sai uban yaji , kamar girkin mayu, gaskiya ni bazan iya cin wannan abincin ba, ka tashi yanzu ka girka min sakwara da miyan taushe sannan ka min farfesun cow tail dan Allah kayi sauri dan in ka bata lokaci zai iya fita raina na fasa ci" tasowa yayi ya dauke plate din gaban ta yace"dan Allah kiyi hakuri my husnah wlh yajin ne yau ya kufce min amma yanzu zanyi miki abin da kike so ki bani 30 minutes kacal" tace "to yadai fi maka " ta maida kanta kan handset dinta taci gaba da charting dinta.
A daukance ya nufi kitchen din ya shiga fereye doyo.................
Ina team Aslam ku kawo mishi dauki hilis karku barshi ya daka doyan nan😁
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 91 & 92