Sashe 79
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Har zuwa wannan lokacin babu abinda ya shiga tsananin su, ta bangaren auratayya saidai zuwa yanzu an samu ci gaba sosai dan sukan sha romance dinsu na fitar hankali, saidai fa iyakar ta nan, ita kanta tana mamakin yadda akayi ya kasa nemanta har yanzu tun abin bai damunta har ya fara dan damunta, har take tunanin anya ma sonda yace yana mata da gaskene kuwa, dan indai akwai soyayyan dole zaiso su zama Abu guda ai, Allah sarki Asmah bata San Aslam yama fita bukatar hakan ba, saidai yana nan akan bakanshi, na cewa saita nemi hakan da kanta tukunna.
Gaba daya Aslam ya manta da wata zee a babin rayuwarsa, Asmah ce kawai a gabanshi a halin yanzu.
Yau gaba daya familin sun tashi da tsantsar farin cike, ba komai bane kuwa face haihuwan da akayi musu gagarumi, yayansu Rabi'a ce ta haihu maman hanifa, ta samu ɗa namiji wannan karon, da safiyar yau mami ta kira su dukkansu daya bayan daya tana gaya musu, duk wacce ta kira ,sai taji ta daka tsalle tana murna tare da tambayarta dama tana da ciki ne, tasan duk abinda sukema wannan tsallen murnan koba komai zasu zo gida zasu haɗu da juna, to ai dole, wata biyar fa ba kwana biyar ba, duk da suna waya da juna, da kuma iyayen nasu......
Oum Ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabilillah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan littafin ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 110
Ƴan matan mummy dukkansu sunje sunga babyn ya Rabi'ah sunyi barka, kowaccen mijinta ya kaita saidai cikin rashin sa'a a mabanbantan lokuta suke zuwa, ranar da batool taje ma tana isa Asmah na wucewa, dan Aslam bai barta ta zauna ba, tare suka shiga kuma ko minti talatin basuyi ba yace tazo su wuce, Rabi'ah kam bakin ta sake take kallon ikon god yadda suke wani nannan da juna dan ko da zai zauna saida ya bari ta zauna sannan ya zauna a kusa da ita ya riƙo hannayenta, bakinta cike fal da gulma amma ba daman yi, saboda Aslam daya kasa ya tsare, saidai insuyi su kalli juna ita da abban hanifa dayake shima yana gida lokacin hakan ne ma yasa aslam ɗin shiga gidan,aiko suna tafiya rabi'a ta shiga gulman aslam tana ba abban hanifa labaran diraman da a kasha waɗanda baisan dasu ba, dariya ya dinga yi tare da cewa "ina ruwan baban yaya"zahra ne kawai bata samu zuwa barka ba itama dan tana da nisa ne, kuma ga karamin ciki, Barr tsoro yakeji, hanyar bidda to minna bashi da kyau, yadai mata alkawarin zai kaita da kanshi idan ana gobe suna kuma zai barta har washe garin suna sañan yazo ya dauketa, takoyi murna take ta kira su batool ta gaya musu, nan suke yanke shawaran suma sai ranar da zata zo zasu ƙara komawa tunda zai kama ran aikin suna gashi kuma ranar ummin su zata iso itama.
~ASMAH~
Ranar da ta kama ranar aikin suna, wato ranar asabar, tunda ta tashi da asuba bata ƙara komawa ta kwanta ba saboda ganɗoki, bayan tayi sallah kitchen ta shiga ta fara haɗa breakfast, Aslam na masallaci, koda ya dawo maimaikon ya sameta tana karatun alkur'ani kamar yadda yasaba tarar wa kullum sai yaga ɗakin wayam, fitowa yayi ya shiga nemanta ɗaki ɗaki amma shiru, can ya zo gilmawa ta wurin kitchen yaji ɓuruntun kwanuka, mamaki ne ya kamashi bai taɓa tunanin ganin ta a kitchen a dai dai wannan lokacin ba, balle ma yau da take asabar ba aiki zaije ba, kara sawa yayi da sauri yana mata alamar lafiya me take yi a kitchen yanzu da hannu, don lazimi yakeyi bai da daman yin magana, da fara'ar ta tace" breakfast nake hadawa da wuri, kasan yaune aikin suna inason kafin takwas da rabi na isa cen" bata rai yayi shifa maganar zuwa aikin sunan nan ya fara bashi haushi, ko jiya bata da magana sai zancen zuwa aikin suna har dare, shi har zancen ya gundureshi ma, yaga sai wani rawar kai takeyi zata fita, wai wani takwas da rabi ya mata acen.
Baice mata komai ba saida ya gama lazimin shi ya shafa, sannan yace "karfe nawa kikace zakije aikin sunan ma?" tace "wai da nace ko takwas da rabi ya min a cen, koya ka gani,ko kana ganin yayi latti da yawa" hararan ya wurga mata sannan yace "wato yayi latti ko, to ni nama soke batun zuwa aiki suna, na fasa, matata ba baiwar kowa bace ba wacce zakije kima aiki" jin haka bata San sanda ta iso gaban shi ba, shima sai kawai ganinta yayi, kafin ya ƙara faɗan wata kalma ta haɗe bakinta da nashi, jin haka sai ya kara tallaɓe fuskarta kawai shima, tayi hakane dan karma maganar tayi nisa ya kaishi ga rantsuwa dan yanzu maganar nan daya faɗa gabanta saida ya yanke yayi mummunan faɗuwa,tasan sarai zai aika dan baya kaunar abinda zai rabashi da ita kona minti ɗaya ne, itako baza ta iya jure ya hanata fita aikin sunan nan yau ba, dan tsabar sa abin da tayi a rai har mafarki tayi gata ga yan uwanta ƙawayenta, shiyasa ma yau ta tashi da ganɗokin abin fiyye da yadda takeji jiya.
Saida suka kwashe mintuna masu ɗan yawa suna kissing din juna kafin, ta kwace kanta dan taga alamar baida niyyar saketa, dan Aslam mayen kiss ne baiki suyi awa haka ba, bata kai kanta ba ma ya ta kare balle, dukkansu sauke ajiyar zuciya suka shigayi kamar waɗanda sukayi wasan tsere, yana kallonta da idanunshi da suka canja launi, ya buɗe baki zaiyi magana tayi wuff ta rigashi da dace "dan Allah da manzon sa ya Aslam kayi hakuri kar kace zaka hanani zuwa aikin nan, wlh in ka hanani zazzabi zai iya kamani" yana kallon cikin idanunta ya mika hannu ya dungure mata goshi cikin sigar wasa, tare da cewa "nace baza kije ba koh" aiko inda kuka san ya wanka mata mari, ta fashe da kuka amma daga jin kukan kasan na zallàr shagwane, tsayawa yayi yana kallonta, cikin muryar kukanta da takeyi na shagwaba tanayi tana bubbuga kafa a kasa kamar ƴar yaye, tace "nidai dan Allah dan Allah dan Allah fa nace yayana plsssssssssss" ta kare da jan pls din sosai cikin wani irin siga najan hankali Wanda ita kanta bata San tayi ba.
Wani irin yarr yarr yake ji a jikinshi, gaɓobin jikinshi gaba daya sun amsa gayyatar da take musu, ba shiri ya juya da nufin barin mata kitchen ɗin, don bai gama lazumum shi duka ba yanzu ma karatun alkur'ani yake son yaje yayi, aiko da sauri ta bishi ta cukuikuiyeshi ta baya tare da kwantar da kanta a bayanshi, hannayenta kuma ta zagayeshi dashi, ta daurasu daidai marar shi, kasancewar ya fita tsawo sosai, ba shiri har bakin shi na rawa wurin cewa "naji naji na amince zan kaiki amma tare zamu kafata kafarki kin yarda" jin haka yasa ta shiga tsallen murna tana cewa"yess! Nagode nagode ya Aslam ɗina" aiko tsallen da takeyi sai ta ƙarkare birkita shi, zagayo da ita yayi gabanshi ya daga ta sama cak ya karasa main parlour da ita, girkin da ba'a karasa ba kenan.
Dan suna zuwa falon kan 3 sitter ya direta ya bita ya danne, a zafafe ya shiga aika mata da zafafan romance, duk da ba mayar mai da martani takeyi ba dama, don bata iyawa sai takega kamar zaiga rashin kunyarta, hakan bai dameshi ba, sai da ya rage zafi sosai ya rabu da ita, duk da bawai ya samu yadda yake so bane, gaba daya jikinta ya matu, ita fa ba iya haka taso wasan ya tsaya ba, ji tayi kamar ta kamo shi ta dawo dashi ya sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi amma baza ta iya ba, sai binshi tayi da idanu har ya ƙule ma ganin ta, ji tayi kamar ta tsala ihu,i tafa wannan lamarin ya fara isar ta.
Ɗakin shi ya shiga ya faɗa toilet ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, idanunshi a runtse, hannun ya kai yana yamutsa suman kanshi, shi karan kanshi ya gaji a halin yanzu matar shi kawai yake bukata, yana bukatar ƴaƴa shima, yana matukar kauna ya ga kwanshi, kamar daga sama yaji zuciyar na, cewa "duk kai ka jawo wa, kanta wannan bata lokacin, ta yaya zakace kana jiran abinda kasan bazai taba yuwuwa ba, to inzaka yunkara ka yunkura, idan ba haka ba kuwa zaku shekara a haka" da haka ya karkare wankan da zaiyi ya shirya ya fito, koda ya fito falon bata nan, hakan yasa ya nufi ɗakinta a kudundune ya ganta cikin bargo, shima bargon ya ja ya shiga tare da jawota jikin shi, babu Wanda yace ma dan uwansa ƙala kowa da abinda yake saƙawa a ransgi, a haka barci ya dauketa yayinda shi kuma ko alamar gyangyadi baya ji haka ya cinye lokacin barcin safen da tunane tunane, Wanda a karshe ya Samar ma kanshi mafitar da yake ganin zata bulle mai.