← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 126

Sashe 63

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin kamshin na daɗa karuwa a hancinta, yasa ta bude idanunta daga lumshe sun da tayi, idanunta bai sauka a ko ina ba kuwa sai cikin nashi, yana tsaye a gabanta yana sakar mata wani irin tsadadden murmushi, zuciyarta ne ya shiga bugawa da wani irin sauri, ba karamin kyau ya mata ba , ji take zuciyarta na bata umarnin ta tashi ta rungume shi kawai, ko zata samu saukin yanayin da takeji game dashi a zuciyarta, amma dake jinin alhaji baba ce badai tauri kai ba.

Tabe baki tayi tare da dauke kanta daga gareshi kamar bata ga komai ba, alhali kuwa taurin kanta ne kawai ya hanata rungumarsa.

Zaro ido Dr bash yayi ganin irin kallon da tamai ta dauke kai, mamakin karfin hali da taurin zuciya irin na batool yakeyi, sarai ya daɗe da sanin itama ta kamu, a zuciyar shi yace, lallai yarinya man kaza nikuma yau nayi alkawarin sai naga karshen taurin kanki.

Batool jin har yanzu yana tsaye a kanta bai matsa ba yasa ta dago kai ta harare shi tare da cewa "lafiya mallam nifa bana son tsayuwa a kai, mutane na basa son ana tsayamin a kai toh na gaya maka, inba so kake yanzu kaji shaka ba kuma to" kin tashi yayi a kannata ya tsaya yaga karshen rashin kunyar ta, tashi tayi zaune tace"dan allah wai bakaji mai nace bane, nace maka bana son ana tsayamin akai " Dr bash yace "naji abinda kikace sarai shakar da kikace zaki min nake jira tukunna" karamin tsaki taja tare da komawa ta kwanta tana dan cuno dan karamin bakinta tana gungumi kasa kasa, cikin son ya tsoratata ya miko hannu kamar zai kamo ta ai ba shiri ta dunkule wuri daya, dan bata manta da muguntar da ya mata da safe ba ya matse mata lips har yanzu zafi wurin ke mata.

Komawa yayi kujeran dake facing Wanda take kai, zaro wayar shi yayi ya dan lallatsa kamar yayi dialing wani number, can kuma ya kara akunne, cikin kashe murya yace da dan karfi yadda ya tabbatar batool zataji "Amincin Allah ya tabbata a gareki yake saurauniyar birnin zuciyar Muhammad bashir"

Kamar saukar guduma haka kalman ya daki zuciyarta, bata San sanda ta tashi ta zauna ba, idanun shi baya kanta amma sarai yana kallonta ta kasar ido, ci gaba yayi da cewa "lafiya kalau sweetheart ya karatu yasu mom, ya kuma fama da soyyaya ta," shiru yayi alamar ana mai magana ta daya bangaren, kwashewa yayi da wani irin dariya cike da farin ciki yace"wow naji daɗi sosai my teema, a she har haka kikayi kewata, gsky na yarda ba karamin sona kikeyi ba, nima kuma ina mutuwar kaunarki bana iya hada soyayarki data kowacce mace a zuciyata," dan dakatawa yayi kamar yana sauraren daya bangaren can kuma ya tabe baki tare da cewa"tana nan gama tanan tana jina, karki damu kanki da ita, ba wai sona takeyi ba, nima kuma ba wani sonta nakeyi ba kawai dai ba yadda na iya da itane" shiru ya danyi kafin yace "wlh baby yadda kikayi kewata haka nima nayi kewarki sosai, yanzu dai albirinki, ki bani nan da 20 minute gani nan zuwa gida yanzu nan" shiru yayi can kuma ya kwashe da dariya yana cewa"baby duk murnan zuwanane haka, gsky naji dadi nasan kuma kina ji dani, yanzu ki tashi kije ki shirya min kwalliya ta musamman, nima gani nan zuwa na caba miki ado irin Wanda nasan yana matukar burgeki" daka tawa ya danyi, sannan yace "OK baby bye sai na iso I luv 2 " ya fada tare da ba wayar wata irin kiss mai sauti muuuaaahh💋, kashe kiran yayi tare da rungume wayar a kirjinshi ya lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya.

Wani irin huci yaji a kanshi ba kakautawa, dagowan da zaiyi yaga batool a gaban shi rike da kwankwaso, fuskarta murtuk kamar an aiko mata da saƙon mutuwa, idanunta sunyi ja tsabar wutar masifar kishin daya kunnu a zuciyarta lokaci guda, hankalinta ba karamin tashi yayi ba dama duk wannan uban kwalliyar da yaci ma wannan yar iskan fatiman yayi, aiko dai akwai bala'i yau a gidan nan, ko sama da kasa zasu hade yau bazai fita agidan nan ba saidai duk bura'uban da za'ayi ayi ta yau.

Murmushi ya sakar mata yana mike wa tsaye, baya ya danja yana dudduba jikinshi yana kakkaɓe kakkaɓe, can kuma ya dago ya kalleta cike da zumudi yace"batool pls tayani duddubawa ina da inane basuyi ba" yana magana yana dan jujjuyawa a gabanta, wani kululun bakin ciki ne ya tokare ma batool makoshi, ji tayi kamar ta lailayo ashar ta kunduma mai, amma ba hali, jin shiru bata ce komai ba yasa ya dago ya kalleta, yi yayi kamar baisan halin da take ciki ba, yace mena miki kuma kike harara na, daga naiman taimako,ki duba min inda baiyi ba na gyara dan na birge baby teemah shine zaki kama harara na ,in bazakiyi ba kawai kice bashir bazan duba ba, ba sai kin harareni ba"cikin tsiwa tace "wai kai mallam me kake nufi naga kamar shirin fita kakeyi" amsa mata yayi da "eh wlh sauri ma nake yi zanje zance ne wajen baby teemah" tace "kana nufin a cikin tsohon Daren nan zaka fita ka barni a gida ni daya kamar wata tsohuwar mayya, to wlh baka isa ba babu inda zakaje ka barni ni daya" dariya ke cinshi,ganin gaba daya yadda hankalin ta ya tashi daga ji yace zaije zance, dakewa yayi yace "zan fita zanje gurin masoyiyata, mai son farin ciki na wacce zata iya haihuwa dani ta samar ma mahaifiya ta farin ciki, idan kin isa kin cika sunan ki batool ki hanani fita" yana gaman fadan haka ya juya ya kama tafiya, a guje batool ta biyo bayan shi, ganin haka yasa ya fice da gudu daga falon yayi waje binshi tayi saidai yana zuwa parking lot ya lalubi makullin motar yaji wayam, sai lokacin ya tuna yana aljihun kayan daya cire, dafe goshin shi yayi tare da cewa "kash, amma banji dad'i ba wlh" dai dai lokacin batool ta iso da gudu saida ya bari ta miko hannu zata rike mai riga, ya wala ta yabi ta gefenta ya kara kwasa da gudu, zuwa ciki zai dauko car key, bata yi kasa a gwuiwa ba ta rufa mai baya, koda ta iso falon ya haura sama,da sauri ta maida kofar ta rufe da key,tare da zare makullin, rasa inda zata boye tayi jin takun shi yana sakko yasa ta Saka key din a rigarta ta sama, ta boye shi a tsakanin boobs dinta, saurin tashi tayi a wajen ta koma kan kujera ta zauna.

Saukowa yayi hannunshi dauke da makullin mota, a ranshi yana mamakin mai ya hanata biyoshi har sama, mamkinshi ne ya dadu ganin ta zaune abinta tana kallon tv ko kallonshi batayi ba, har karkada key yayi irin wai ko bata San ya sakko bane, tanaji tayi kunnen uwar shegu, dage kafala yayi alamar ko ajikina d'in nan, ya nufi kofa abinshi zai fice, saidai yana tura kofar yaji shi a garkame, kuma ba key a jiki.

Juyowa yayi ya kalleta, still idanunta nakan tv bata kalli inda yake ba, cikin dan muryar fada fada yace "kee ina key din kofar nan yake" inda kukasan da dutse yayi magana, ya sake cewa "wai baki jina ne nace ina key, ki bani makulki zan fita" share shi tayi yanzuma bata tanka ba, yace "OK wato ga ɗan iska na magana kin kyale ni ko"

Dawowa yayi fa fara dube dube a falon , lungu da sako har su kasan kujera , har cikin flower vase, harda su kasan center carpet, ba key ba dalilin shi , batool na zaune duk abinda yakeyi tana kallon shi ta kasan idanu, duk inda yasan zata iya saka key dinnan ya duba a falon nan bai gani ba, take zuciyar shi ya bashi key dinnan na jikinta ta, dagowa yayi ya kalleta daidai tana gyara zaman rigarta da kyau, itama cikin sa'a lokacin ta kalleshi, yace "batool ina key" cikin tsiwa yace"ni ban dauka key ba, ka dameni da tambaya,ko ka bani ajiya ne wai" kara maimaita mata tambayar yayi "nace ina key yake" ya fada yana nufo ta , ganin haka yasa tayi wuff ta mike, hakan yaba key din dake jikinta daman yin kara kasancewar makullin ba daya bane a hade suke wajen guda hudu, tsab yaji karan kuma yaji daga ina karan ya fito, nufota yayi gadan gadan, aiko ganin haka yasa ta juya a sittin ta yanka da gudu, binta yayi taku biyu ya cimmata ya damko ta.

Mutsu mutsu ta shigayi tana neman kwatan kanta, cikin tsiwa da rashin kunya take cewa "wlh nidai ka sakeni babu wani makullin Dana dauka ka sakeni ka sakeni " bai saurari hargaginta ba ya hade hannayenta wuri daya ya rike, ya manna bayanta da kirjinshi ya matseta da karfi yanda ko motsi bata iyawa.

Daya hannunshi yasa ya shiga cajeta tun daga kasa, yana labubeta shine hannunshi har cikin pant dinta yana neman key, bai samu anan ba hakan yasa ya dawo da hannunshi sama, saka hannu shi yayi a cikin rigarta ta sama, wani shork ne ya ziyarcesu a tare daga shi har ita, lumshe idanu yayi jin yanda boobs dinta keda wani irin laushi da dadin tabawa, lalube ya shiga yi yana matse mata boobs da sunan yana neman keys sarai yaji key din a wajen amma haka kawai yaji ya kasa Ciro hannun shi daga wurin, luf batool tayi tana jin wani irin yanayin da bata tsintar kanta a ciki ba, na ziyartar ta.
Chapter 63 · 0% Book details