Sashe 27
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bashir yace" mummy a mana afuwa munyi kuskure kar kiyi fishi damu fushinki babban matsalace a garemu, wlh ni karan kaina mummy wata ran nakan rasa gane kàn Aslam , adai cigaba da mana addu'a" mummy tace"ai kudinne bashir kuna kai mutane iyaka, ace kune manya a gida amma qanana ma sun fiku hankali"
Nan dai bashir ya shiga ba mummy hakuri, kafin ya miqe da niyar wucewa ya kuma CE zaije can gidan Aslam d'in ya gani,
Dai dai lokacin motar kamal daya d'akkosu daga school ya paker a harabar gidan , a guje batool ta balle murfin motar ta kwasa da gudu zuwa part din mummy, saboda tsokanan zahra da ta dingayi a hanya , akan wani lecturer daya ce yana sonta ,ita kuma zahra ta tsani mutumin kwata kwata ko zance bataso,shine fa batool ta samu taketa guma mata,ita kuma ta cika tam kamar ta fashe jira kawai takeyi ya kamal yayi parking su yada hali, ita kuma sanin bata da gsky yasa ta kwasa da gudu cikin gida,
Daidai bashir ya sawo kai zai fito itama ta sawo zata shigo, yauma wani karon suka sake maimaitawa kamar dai rannan,
Kowannen su ja da baya yayi , yana Sosa goshi, idanun su ne ya sarqe dana juna , cikin matuqar mamaki har suna hada baki gurin furta , "you again".............
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fi sabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO ~
FREE BOOK
{ na sadaukar da wannan lillafin ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen
Page 59 & 60
Da kallon mamaki suke bin junan su, lokacin da wancen karon ya faru ya ɗaɗe bai manta fuskar yarinyar ba , tsiwar ta da rashin kunyar ta ya dade yana bashi mamaki,
Itama tayi matuƙar mamakin ganin shi a gidan su , kuma a part din mummy, amma hakan bai hanata ɓalla mai harara ba, cikin tsiwa , tace" wai kai Mallam me kake nema danine, ko wani lokaci muka haɗu sai ka bangaje ni, to wallahi kayi na farko kayi na karshe, duk sanda ka sake bangazata saina sa Allah ya isa" ta qareshe cikin murguɗa baki,
Shi abin ma dariya ya bashi, amma ya dake baiyi ba don kar ta rainashi, don ya lura yarinyar kwata kwata bata da kunya, kara hade rai yayi, cikin dakewa yace"waike me yasa baki da nutsuwa ne, kullun in zanganki kina cikin gudu sai kace wata qaramar yarinya , koda yake yarinyar ce, don da ganin ki ba kifi twelve years ba"
Cikin zaro tace "kan uba, nice Mara nutsuwa"
Kafin ya bata amsa su Asmah da kamal sun karaso wajen
Hannu kamal ya bashi suka gaisa, su Zahra ma suka gaisar da shi , a fakaice yake satan kallon Asmah, a zuciyarshi kuma yana raya "lallai kamal yayi dace, yanzu dama Aslam wannan zuqeqiyar yarinyar aka aura mai ya saki, lallai ya tafka babban kuskura, yayi wasa da damar shi ta farko, gashi kuma bai samu dama ta biyu ba,
Ganin sunzo gurin yasa batool ta hadiye sauran rashin kunyar da tayi niyyar sauke mai , amma fa sai banka mai uban harara takeyi, duk yana lura da ita,
Shigewa ciki yan matan sukayi yayinda Dr bash da kamal suka tsaya suna magana,
Suna shiga batool ko gaida mummy batayi ba tace" mummy dan Allah mutumin daya futa yanzu daga part ɗinnan meye alakar mu dashi ne, ni wlh haushin shi nake ji, ya fiye shegen iyayi wlh"
Mummy zuba mata ido kawai tayi tana kallonta ta inda take shiga bata nan take fita ba sai masifa takeyi , kamar zata ari baki
Suma su zahra duk tsayawa sukayi suna kallonta, saida tayi mai isarta , sannan ta lura da kallon da suke binta dashi,
Kwashewa tayi da dariya mummy tace"sannu mandiya ci gaba mana, ko har kin gama kenen,"
Cikin dariya tace "wlh mummy mutumin bashi da mutunci rannan fa wai marina zaiyi, ranar dinner ya Aslam, har ya daga hannu kome ya tuna naga ya sauke hannun yana kwafa kamar ya Aslam na tafe yana binshi a baya,"
Mummy tace " ai wlh bashir bai biya ni da kakkafta miki mari ba tunda ke kince baki da kunya"
Cikin tura baki ta tashi tana haurawa sama tana dan gungunin, a hankali "tab wlh yana wanka min mari zan rama"
Mummy tace" me kike cewa , ki tsaya kiyi a gabana mana, rasa kunya,"
Su Asmah gaisar da mummy sukayi , sannan suka haura sama dan su kimtsa kafin su fito suyi lunch.
Dr bash yana tuki yana tunanin batool , shi kadai sai murmushi yake yi, can kuma a fili ya furta " kan uba nice mara nutsuwa " cikin kwaikwayan muryanta,murmushi ya kuma saki, kafin a hankali ya furta "ta cika tsiwa" haka kawai ya tsinci kanshi cikin wani irin nishadi na musamman,
Da haka ya iso gidan Aslam , gaisawa sukayi da mai gadi, nan yake shaida mishi matar gidan bata nan amma me gidan yau kwana uku bai saka shi a ido ba, kuma ya tabbata yana cikin gidan bai fita ba , don inda ya fita zai sani ,tunda shi zai bude mishi get,
Cikin mamaki yace ka "tabbatar yana ciki " megadi "yace kwarai yallabai , don ko jiya da hajiya ta dawo ta tabbatar min yana ciki kuma yana lfy"
Dr bash yace " anya kuwa yana lfy, yanzu dai zanje na dauko dan uwan shi Amir zamu shiga mu duba , idan kuma madam ta rigani dawowa ka gaya mata Dr bashir ya zo,"
Megadi ya amsa da to "to yallaɓai a dawo lfy"
Motar shi ya shiga yabar gidan , don zuwa ya dauko Amir,
Karfe biyar daidai na yamma motar brr Adam ta parker a harabar gidan alhaji baba, fitowa yayi daga cikin motar sai zuba kamshi yakeyi, yaci kwalliya cikin dañyar shadda ash colour, sai maiqo takeyi, gsky brr Adam ma ya hadu over,Baki ne dogo kyakkyawan gaske mai siffar dakakkun maza, kallon daya zaka san ma'abocin ibadah ne , saboda yadda fuskar shi ke cike da kamala da haiba, na hasken musulunci,
Megadi ne yamai iso gurin daddy, daddy dama ya riga yasan da zuwanshi don , kuma yasan ba wurin shi yazo ba gurin Zahra ne, don haka ya bada umarnin a kaishi sitting room , a kuma je a gaya wa mummy baƙon zahra yazo
Haka ko akayi mummy dama ta riga tasan za zancen, don jiya daddy ya fada mata komai, itama tayi na'am dashi ganin yadda mijin nata yayi na'am dari bisa dari, tasan bazai yi na'am da abinda zai cutar da ɗiyar wani bama balle ɗiyar shi,
Wayarta ta laluba ta kira zahra, tace ta sameta a falon ta yanzu yanzu,
Zaune suke dama suna karatun alkur'ani da sukeyi duk bayan sallan la'asar, ranar da Mallam ɗinsu bazai zoba dama haka sukeyi su biyama junan su, dogon hijabine har ƙasa a jikinta irin mai dan kwalin nan,
Miƙewa tayi tace ma su Amira tana zuwa ,mummy na kiranta, a falo ta samu mummy, zama tayi a gabanta tace"mummy ganin,"
Kallonta mummy tayi kafin tace"kinyi baƙo, yana sitting room din daddy, dauki ruwa da lemo ki kai mishi , daga nan kuma ki saurari meya kawo shi gareki "
Cikin dan mamaki tace"tace mummy baƙo muka, nifa banba kowa izinin zuwa gidan mu ba, ita a tunanin ta wannan lecturer ne daya dameta a school,"
Mummy tace "to tunda ya riga yazo sai kije ki gani ko" amsawa tayi da to mummy sannan ta fice , kitchen ta fara biyawa ta ɗauki abinda mummy ta umarceta sannan ta nufi hanyar sitting room d'in,
Da sallama ta shiga falon, yana zaune ya ƙurawa ƙofar shigowa ido jira kawai yakeyi yaga ta inda zata bullo, yarinyar da tun gani na farko har yau ya kasa cireta a zuciyarshi daidai da minti daya,
Amsa mata sallaman yayi shigowa tayi cikin natsuwar ta, gabanshi ta nufa ta ajiye tiren hannunta , sannan ta koma baya ta nemi kujera ta zauna,
Sai sannan ta dago kai ta kalleshi, ji tayi gabanta ya yanke ya fadi, da sauri ta dake kai daga kallonshi, don yayi mata kwarjini sosai, gani takeyi kamar tasan fuskar shi amma kuma ta manta inda tasan shi,
Cikin siririyar muryarta tace "ina yini" taja bakin ta tayi shiru,
Tunda ta shigo yake binta da kallo sai yanzu ya tabbatar Ashe rannan ma kallon tsoro ya mata, yanzu ne yake qare mata kallo mai sunan kallo,
Cikin kulawa da maida dukkan hankalin shi gareta ya ̃amsa mata da" ina gajiya faɗeema, ya gida ya makaranta " ta amsa da lfy qlau,
Shiru sukayi dukkansu sai can ya katse shirun da cewa " nasan kin manta ni ko" dagowa tayi ta kara kallonsa a karo na biyu, still bata tunashi ba,
Murmushi yayi yace "dama nasan ni kadai nake kiɗa na da rawa na,"
A karo na biyu tace" kayi hakuri dan Allah ban gane kaba, amma kuma kamar na taba ganin fuskar ka a wani wajen"
Cikin jin ɗaɗi yace"well hakan ma na gode tunda kin tuna kamar kin sanni,naji ɗaɗi kuma nagode, amma kinga ni tun gani na dake na farko ko daidai da second daya ban qara manta ki a cikin zuciyata ba, nine abokin Abban hanifa, nan da muka hadu a gidan kwanaki kika kawo min ruwa "
Cikin mamaki ta dago tace "Ooh sai yanzu na gane ka, dan kayi hakuri ban gàne ka bane da farko, ya hanya ,ya iyalai".
Yace "lafiya qalau sunce ma na gaida ki"
Tace "aiko nagode ina amsawa,"
Dan shiru sukayi kowa da saƙesaƙen da yakeyi cikin ransa,