← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 126

Sashe 73

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya samu gamsuwa da jin dadin da bai taba tuananin ana samu a duniya ba, duk wani sha'awan daya tara na kwana da kwanaki saida ya sauke su tsab a wannan daren, bayan gaba dayan su sun samu gamsuwa rungumeta yayi, yana hawayen farin ciki a hankali ya shiga furta"ina son ki my teema, ina mahaukacin kaunar ki, ina son ki my batool, nagode Allah ya saka miki da alkhairi, ina kaunar ki fiye da yadda nake kaunar rayuwata, kece farin cikina kece zabin raina, ina sonki da dukkan ruhi da zuciya," kamar a mafarkin haka taringa jin saukar kalaman sa cikin kunnenta, ya rufe ido sai sambatu yake yi, duk da halin da take ciki na matsanancin kunyar shi hakan bai hanata ɗago da kai ta kalleshi ba, cikin sa'a shima ya bude idanunshi, cikin rawar lebe tace "da gaske kakeyi dama kana sona ba liƙa mata ni akayi kamar yadda ka faɗa ba" tausayi yaji ta bashi sai yake ga kamar bai kyauta ba da yace mata haka, cike da kwarin gwuiwa ya shiga girgiza mata kai yana cewa" kwarai kuwa batool babu Wanda ya liƴa mini ke ni da kaina naje na nemi auren ki, saboda so da kaunar da nake miki,kece my teema kece Fatima ta kece kaɗai macen da zan iya so acikin zuciya ta" wani irin ƙanƙameshi tayi, cikin tsananin farin ciki da jin dad'i ta shiga furta"I luv u 2 mijina nima wlh ina tsananin sonka ina mahaukacin kaunar ka, tare da matsanancin kishinka" kalamanta wani irin daɗi da suka mishi sun samu matsuguni a can cikin zuciyar shi, wani shaukin so da kaunarta ne suka ɗebe shi, take ya sake lalubarta bakinta ya haɗe da mashi, suka koma ruwa, dama itama tana da bukatar hakan.

Saida suka sake jiyar da juna daɗi, duk sun gaji hakan yasa ya rungumeta suka shiga bacci sai gabanin asuba suka farka, suna farkawa ya yunkura da niyyar tashi yaje ya haɗa musu ruwan wanka, sai ji yayi ta ruko hannun shi ta baya, kwayar idanunta kawai ya kalla ya fahimci komai, baiyi kasa a gwuiwa ba kuwa ya biye mata, ko da suka yi wanka ya makara sallah a masallaci har an idar dole a gida sukayi jam'i tare, bayan sun idar ya janyota suka koma bed suka shiga ramakon baccin jiya da basu samu yi sosai ba............

hmmmmmm batool da Dr bash rayuwa sabuwa, amma fa da alama fa Dr bash ya manta da warning ɗin maah😊 tun da wuri ku tuna mai, ɗan tayin cikin baiyi kwari ba, kar aje garin cin amarci a jawo ma maah arasa😜

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARI NE MALLAKINA NE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌

(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira 👌 a kiyaye pls)

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiy,Allah kajiqan iyayen mu}

💖Tallah!💖 Tallah!!💖

💖Tallah!!!💖

💖

Albishirinku manyan mata! ma'abota kwalliya da
_Rantsattsun lesussuka💃,
_Atamfofi manya da k'anana💃
_Galla gallan shaddodi manya da k'anana muna da su kowani iri💃
_Akwai kuma yadiddikan maza kamarsu koranza,plan yard dadai sauransu💃
_Munada mayafai, takalman maza da mata,sarqoqi, awarwaraye,da duk sauran nau'ikan kayan ado na maza da mata muna dasu 💃
Akanfaninmu na""R & U""Global Enterprise Dake Nan Garin Minna Niger State, saikunzu..........

Ga numbern mu kamar haka👇
08062160424
08066891424.....

Sayan day'a ko sari acikin farashi mai sauqi👌
Kubamu odern ku,danshine aikimmu akoda yaushe da yardar Allah........👌
Sai an gwada akansan na kwaraiiii💃💃💃.....

Page 105

~ASLAM~

Bayan fitar ta daga dakin dafe goshi yayi ya kama fareti a dakin, yakai gwauro yakai mari ya kasa zama, can dai ya naushi iska tare da cewa"oh my god, yanzu miye mafita" dan tsayawa yayi daga faret din da yakeyi da alama wani tunani yayi, can kuma ya furta "yesss" kafin ya fice daga dakin da sauri kitchen ya fara nufa bata nan, dan haka ya duba falo nan ma wayam, nan take ya tabbatar tana dakinta tunda bata wuraren nan biyu daya duba, dakin nata ya nufa cikin sauri sauri har ya mika hannu ya kama handle din kofar zai tura, take wani shakkar ta ya lullubeshi , zuciyar shi ta shiga ce mishi yanzu in ka shiga mai zaka ce mata, take yaba zuciyar shi amsa da babu, da baya da baya ya dinga yi har ya bar kofar dakin.

Tunda ta shige daki ta lalubi bakin bed ta zauna dabass, take duk abinda ya faru tun daga fara ciwon Aslam har zuwa yau ya shiga dawo mata tsab a brain dinta, ta tuna yadda yake tsananin jin jiki da yadda kullum Daren duniya yake fama da matsanancin zazzabi, Ashe duk karya yake mata dan dai kawai ya samu ya rabi jikin tane, bata son karya, balle ma irin wannan karyar da zaka ma Wanda ya aminta dakai, take Kamal dinta ya fado mata a rai, Kamal bai taba yi mata karya ba, hawaye taji yanaziraro mata tunawa da irin yadda Kamal ya nuna mata soyyaya da kulawa, a fili ta furta"Allah sarki ya Kamal, Ashe dai nida kai baza mu zamto abokan rayuwar juna ba" daga haka kuma ta zame ta kwanta girkin da bata karasa ba kenan, haka tayi ta tunane taunane daga nan kuma barci barawo ya sace ta mai cike da mafarkan kamal.

Aslam ganin bata fito ba har azahar gaba daya hankalin shi yayi matukar tashi, kusan so biyar yana zuwa kofar dakinta da zumar shiga, sai kuma ya kasa, haka yata zarya bashi falo bashi daki, ko abinci bai samu daman ci ba, kai yunwar ma gaba daya bai jita ba, sai gurin yamma da yaji ulcer na shirin tirnike shi, ya shiga kitchen ya Samar ma kanshi abin tabawa.

Sai gurin karfe biyu ta farka, a firgice, take ta shiga furta astagfurullah, mafarkin da tayi a yanzu ya tayar mata da hankali, ta sani ya kamal ya haramta a gareta, tunda ya kasance a yanzu mijin yar uwa kuma kanwarta,amma yadda ta kwanta tana tunanin shi barci ya kwashe ta yasa har take mafarkin shi, kallon agogon dake manne jikin wall din dakin tayi biyu harda minti 10, lokacin tuni har an idar da sallan azahar a masallatai, alwala ta dauro ta fara gabatar da sallah, bayan ta idar kuma ta koma ta kwanta, Aslam ne ya fado mata a rai, ji tayi gabanta ya yanke ya fadi, samun zuciyarta tayi da son sanin wani hali yake ciki yanzu, take taji zuciyarta na azalzalan ta akan ta tashi ta fita ko ganin shi ne kawai tayi, da'ker ta samu tayi yaki da zuciyarta ta tayi fatali da wannan umarnin da take bata, wayar ta ta dauka ta kunna data ta shiga WhatsApp d'inta Wanda rabonta da shi yafi sati, message na gama shigowa ta fara bi daya bayan daya tana dubawa Wanda zata amsa tayi Wanda zata share ta share, haka har takai kan message d'in Khadijah, budewa tayi, idanunta ne ya sauka akan wasu zafafan hotunan da Khadijah ta turo mata yau kimanin kwana uku kenan, hotunan ta ne ita da kamal masu shegen kyau, kala kala cikin wanin irin yanayin da ita kanta baza ta iya fassarashi ba take bin hotunan da kallo, gasu fess da su sunyi wani fresh shar dasu, kallo daya zakama hotunan kasan ma'abota hotan cike suke da tsantsar so da kaunar junan su, yanayin murmushin dake dauke a fuskokinsu kadai ya ishi mai kallo shaidar hakan balle kuma idan ka kalli yanayin styles d'in hotunan, a kasan hotunan ta rubuta, "komai ya daidaita a tsakanin mu yar uwata fatan kema haka daga naki bangaren"

Bata sanda ruwan hawaye ya fara wanke fuskar ta ba sai gani tayi yana diga akan screen d'in wayar, ta bata lokaci akan kallon hotunan fiye da awa daya, can kuma Kamar wata tabbabiya ta saki wani kayataccen murmushi, a fili ta shiga furta "na taya ki murna yake yar uwata Khadijah, hakika Allah ya baki miji daya tamkar da dubu, Allah ya zaunar daku lafiya,ya Allah wannan soyayyar junan su da na gani kwance akan fuskokin su Allah ka dauwamar musu dashi har abada" reply ta mata da "wow masha Allah, perfect mach, gsky hotuna sunyi matukar kyau yar kanwata, tunda nake ban taba ganin couples d'in da suka yi marching sosai da juna irin wadan nan ba, kyawawan masoyan asali, Allah yabar kauna romeo & Juliet " a karshe ta kawata rubutunta da emoji kala kala, na murna dana murmushi tayi sending, sauka tayi a WhatsApp din ta koma gallery folder daya ta ware na hotunan kamal zallah, take ta shiga folder ta fara deleting d'in duk wani photo da ta Sani na shi dake wayarta, yadda take deleting hotunan shi haka takeji yana fita a zuciyarta, saida tayi deleting duk wani abu daya shafi kamal a wayarta, daidai da app da tasan shi ya saka mata a wayar saida ta goge dan kar ta dinga tunawa da shi, bata bar komai ba hatta da phone number dinshi saida tayi deleting a wayarta, take taji zuciyarta ya samu wani irin space mai girma wanda a da babu shi a zuciyarta ta, lallai kamal ba karamin wawakeken gurbi ya samu a zuciyar ta ba,wasai take jin kanta a yanzu babu kowa a zuciyarta.
Chapter 73 · 0% Book details