← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 126

Sashe 94

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gida ne fankacece mai dauke da dakuna hudu ƙananan, daya uwar gidan daya na mai bi mata daya na miji sai daya na yara wanda nan aka gyara wa beebaloo,abinda yaba yan rakiyar beebaloo matukar mamaki, yadda suka ga da murna da farin ciki sauran matan mallam kamsusi suka amshe su, tuni suka gabatar musu da tuwan dawa da miyar gari harda ruwan randa mai sanyi, gaba dayan su ba wacce ta iya hadiye lomar farko na tuwon, saboda rashin dadin sa mayar salam sai uban yaji, karshe da yunwa ta ciwo su dole dama tuwan sukayi suka sha shi kamar koko, Allah Allah suke gari ya waye su baro kauyen.

Da safe uwar gidan mallam kamsusi ta kawo musu kunun garin dawa da dumame, cikin fara'a ta gaishe su babu alamar kishi ko kaɗan a fuskarta, kasa hakuri kanwar beebaloo tayi tace"baiwar Allah naji ance mana kece uwar gidan shi, kuma banga alama ba nace koba ke bace." Cikin washe baki tace "wlh nice uwar gidan shi." Da mamaki ta kara ce mata"shine babu ko alamar kishi a fuskar ki." Kallonta matar tayi da mamaki tace"kishi fa kikace baiwar Allah,kishin wa?kishin mallam wai, aini idan yau mallam zai karo wata matar ya cike ta hudu sai nafi kowa farin ciki, ko ba komai raba kwana zamuyi, aini nafi kowa farin cikin da auren nan na mallam badan kar nayi karya ba da sai nace har shi nafishi farin ciki da auren, kardai na cika ku da surutu bari na barku ku kimtsa." Ta faɗa tana mikewa ta fice, kallon juna yan rakiyar beebaloo sukeyi, cike da mamakin wanga lamari, to duk yadda akayi a kwai lauje cikin nadi.........

Oum Ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

109

~MALAYSIA~
Bayan wata uku

Dad ɗin zee na hango zaune a cikin wani ƙaton falo mai dauke da kujeru sama da guda hamsin, a cikin falon akwai wani ɗaki mai wawakeken kofar glass, zaune yake ya zuba tagumi da hannu bibbiyu yayinda gabanshi kaɗan mum ne sai safa da marwa takeyi ta kasa zaune ta kasa tsaye, basu kaɗai bane a falon a kwai wasu mutanen amma kowa da abinda ya dameshi babu mai shiga harkar kowa,

Daga kaina nayi na kallin sunan da ke rubuce a saman dakin ~labour room~ abunda idanuna suka hango min kenan.

Suna a wannan yanayin bini bini dad kan amsa call a waya yayinda mum kam gaba daya bata cikin hayyacinta, sai yi take tana aza hannu a kai tana saukewa, can bayan kamar 30 minutes sukaga an budo kofar glass din an fito, wani mutumi ne fari sol kamar zabiya sanye da kayan likitoci ya fito daga dakin, da sauri Dad ya zabura ya mike,shida mum har suna rige rigen isa gareshi, a ruɗe. Dad ya fara cewa "Dr ina daughter ta haihun,ko har yanzu?" Mum ma cewa take "pls Dr ina daughter na, wani hali take ciki, Dr idan abin bazai yuwu ba kawai ayi mata theater" Dr kam rasa ma wani amsa zai basu yayi, ganin yadda suka tare shi, gashi shi kuma sauri yakeyi yasa yace musu"excuse me pls" tare da dojewa ya wuce su da sauri, hannu mum ta daura akai tana hawaye tare da ambaton "innalillahi wainnailaihi rajiun" Dad kam bin bayan Dr yayi da sauri saidai kafin ya cin masa ya shige wani office, Wanda babu mai ikon shiga sai likitocin asibitin, dawowa yayi jiki a sanyaye ya nemi gurin shi Nada ya kuma zama.

Tsakanin shida mum an rasa mai jarumtar rarrashin wani, kimanin awa goma kenan da suka kawota asibitin, tun cikin dare naƙuda ya tasar mata gadan gadan, ba shiri kuwa aka shige da ita labour room, saidai har zuwa yanzu karfe goman safe bata haihu ba kuma ba Wanda yace musu wani Abu game da ita, saidai kawai gani sukeyi likitoci da nurses nata zirga zirga a ɗakin.

Hankulansu gaba ɗaya yakai matukar ƙololuwar tashi, tsoron su gaba ɗaya kar su rasa
ta, itace farin ciki su, ita kaɗai suka mallaka suna matukar tsoran rasata.

A wannan yanayin maimakon su tayata da addu'a, amma ina abinka da jahilai, Dad sai zufa yake hadawa idanunshi sun rine jajur,in yayi ya lailayo ashar ya ɗura wa Aslam, yayinda mum ta kasa tsaye ta kasa zaune sai fareti takeyi tana risgan kuka.

Bayan mintunan da basu gaza goma ba wata nurses ta fito daga ɗakin, nan itama suka mata caa aka, kallon mutanen falon tayi fuskarta dauke da murmushi tace,"su wanene iyayen zainab Abdussalam" bakin na rawa Dad yace "yes mune mune" mum ma tace "eh nice mahaifiyar ta, wani hali take ciki" nurse tace "alhmdllh ta sauka lafiya yanzu an samu baby boy," tsabar farin ciki mum batasan sanda ta rungume nurse ba, Dad kuma kallonta yayi yace "nurse wani hali take ciki" cikin murmushi tace," tana lafiya yanzu haka ana gyarasu ita da babyn nan da yan mintoci za'a fito da ita zuwa ɗakin Hutu, sai ku samu ku ganta" dad" ajiyar zuciya Dad ya sauke tare da shiga jero ma nurse ɗin godiya, nan kuma ya ɗauki waya ya shiga kiraye kiraye.

Nurse kam da'ker ta samu ta kwace kanta a hannun mum ta koma ɗakin da ta fito.

Ba'afi 20 ba kuwa aka gunguro zee daga labour room zuwa ɗakin Hutu, sai lokacin su mum suka samu ganinta, tayi fiyaut da ita, ta kara haske, basu Daɗe a ɗakin ba akace su fita su barta ta samu barci sosai an mata alluran barcine, kasancewar ba karamin wuya tasha ba, tayi nakuda mai tsayi kamin ta samu ta haihu da taimakon kwararrun likitocin asibitin.

Babyn dake nannade cikin farin shawel an mishi wanka an shiryashi cikin tsadaddun kayan sanyi aka mikoma mum, hannu na rawa ta karɓa, tsurawa yaron idanu tayi tana kallo, Dad dake tsaye ganin haka yasa shima ya matso don yaga mai take kallo haka, abinda ya faru da mum ne shima ya faru dashi, kallon yaron sukeyi babu ko keftawa.

Bacci yake yi idanunshi a kulle fari sol ƙato da shi mai kama da Aslam sak, babu abinda ya banbantasu,kwata kwata bai dakko komai na zee ba, duk da mum da Dad basa kaunar Aslam hakan bai hana ɗanshi samun kyakkyawan matsuguni a zuciyoyin su ba, farat daya yaron ya shiga ransu, a kallo na farko.

Gaba ɗaya sun shagala da kallon yaron saida sukaji, muryar nurse tana musu magana sannan suka dawo hayyacinsu,saƙon Dr ta sanar musu na cewa da yayi su same shi a office, Dad ne yabi bayan nurse din zuwa office ɗuin Dr yayinda mum ta rungume yaron tsam a kirginta tanajin wani irin son shi da kaunar shi na huda kofofin zuciyarta.

Saida zee ta kwashe awa shidda kwarara tana barci kafin ta farka, wuraren la'asar, zuwa lokacin kam asibiti ya cika makil da yan'uwa da abokan arziki yan gayu masu abin hannu,yawancin su ma turawa ne wadan da su mum ke hulɗa dasu, kowa ya dauki yaron nan kallon daya zakaji ya shiga ranka, da alama dai baiwarsa ce hakan.

Zee ta farka da sauƙi sosai don bayan Dr ya duba ta, ya tabbatar musu nan da gobe ma za'a iya sallamarta taje gida abinta, bayan mum ta bata shayi mai zafi tasha ta kuma sha magunguna, sannan aka bada daman mutane su shiga su dubata, kowa barka yake mata, bata iya amsawa sai smiling kawai take musu, lokacin da aka bata babyn kuwa tsura mishi idanu tayi tana binshi da wani irin kallo, babu abinda take gani a fuska da jikin yaron sai Aslam dinta, take wani irin kewa da kaunar mijinta ya turniketa, rungume yaron tayi sosai a jikinta tana jin wani irin kaunar shi na huda zuciyar ta, bata San sanda ruwan hawaye ya wanke mata fuska ba, ta shiga risgan kuka harda sheshsheka, ganin haka yasa mum ta miƙa mata hannu alamar ta bata yaron girgiza mata kai tayi alamar A'a dole mum tayi hakuri ta bar mata abinta.

Zuwa dare babyn ya fara kuka, Dr yace ya kamata a bashi abinci yunwa yakeji, Dad yace Dr ya rubuta musu madaran da za'a dinga bashi yaje ya siyo, da mamakin su ji sukayi zee tace , A'a kar a siyo madaran ita zata shayar da ɗanta, Dr yace well dama haka ake bukata, nan wata nurse ta gyara mata shi sosai ta koya mata yadda zata rikeshi a yayinda da zata shayar da shi, nonon aka sa mai a baki ba shiri kuwa yaro ya kama yana tsotsa, duk da matsanancin zafin da takeji hakan baisa ta fasa shayar dashi ba, nurse din data fahimci tanajin zafi ta shiga kwantar mata da hankali da cewa karta damu zai daina, idan ya kwana biyu yana sha, shikenan baza ta kara jin zafi ba kuma.

A asibitin suka kwana zuwa washe gari ta ƙara samun sauki sosai don haka Dr ya rubuta musu sallama suka dawo gida, kulawa sosai zee ke samu daga gurin iyayenta ita da little Aslam dinta, wata babban nurse mai zaman kanta, wayayya mai wadataccen ilmi Dad ya daukar musu ita ke kula da komai nasu ita da babyn bangaren wanka tsaftar su da abincinsu, kai komai ma daya shafe su.

Zee taji dadin yadda iyayenta suka karbi yaron da yadda suke nuna mai kauna da kulawa, bata taɓa zaton haka ba, ganin yadda suka dauki karan tsana suka dorawa uban ɗan.

Kafin sati ya zagayo tayi bulbul ita da babynta gwanin sha'awa, jego takeyi na yayan gata, baza ayi taron suna ba, raɗin suna kawai za'ayi dad ne ya siya duk wani abinda ake bukata na radin suna kamar rago da sauransu,tambayarta sukayi sunan da take so a saka ma ɗanta babu kunya ko kara tace Muhammad Aslam, haka ko akayi, duk da Dad yaso ace sunanshi ta zabar wa yaron.

(kuji min Dad da ƙoƙari wai da sunanshi ta zaba😒 babu kunya ba tsoron allah cikin da yayi niayyar hallakawa)
Chapter 94 · 0% Book details