← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 126

Sashe 70

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da idanu suka rakata har ta kule ma ganin su, Dad ne ya sauke ajiyar zuciya yana kallon mom yace"lamarin daughter ya fara shamun kai, anya ba asiri wannan dan iskan yaron ya mata ba kike gani, ki duba kiga yadda ta canza gaba daya cikin dan wasu watanni ta zama wata silent da ita, ko magana bata mana idan ba da kwakwaran dalili ba, naji na hakura na janye na bar mata cikinta ta Haifa tunda dai ita taji ta gani zata iya , amma duk da haka ban tsira ba" mom tace "bana tunani asiri ya mata nafi tunanin soyyaya ce take mishi mai matukar girma, lokacin da ta fara zuwa makarantar koyan girki Dana tamabayeta dalili, direct ta gayamin saboda Aslam ne , saboda duk randa ta koma dakinta t,ya kasance ta iya girki Aslam zaiji dad'i zaiyi alfahari da ita" dad ya daura da cewa "haka nima dana tambayeta game da wannan karatun da takeyi, ce min tayi saboda Aslam ne, saboda yana son tasan addinta ni wannan lamari ya fara isana fa , yanzu cikinta yakai wata nawa" mom tace shekaran jiya da mukace asibiti dai akayi scanning Dr yace wata bawai kenan cif" sauke ajiyar Dad zuciya fuskar shi dauke da matsanan cin damuwa yace "Allah ya sauke ta lafiya" mom ta amsa da amen ya rab , itama zuciyarta babu dad'i...............

Comment nake so ta ko'ina kokuma mu koma tsallake tsallake baban gora😁 ehee kundai ji na fada ko naga comment kokuma update ya koma yau ayi gobe a huta.

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabillilah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARI NE MALLAKINA NE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌

(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira 👌 a kiyaye pls)

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiy,Allah kajiqan iyayen mu}

💖Tallah!💖 Tallah!!💖

💖Tallah!!!💖

💖

Albishirinku manyan mata! ma'abota kwalliya da
_Rantsattsun lesussuka💃,
_Atamfofi manya da k'anana💃
_Galla gallan shaddodi manya da k'anana muna da su kowani iri💃
_Akwai kuma yadiddikan maza kamarsu koranza,plan yard dadai sauransu💃
_Munada mayafai, takalman maza da mata,sarqoqi, awarwaraye,da duk sauran nau'ikan kayan ado na maza da mata muna dasu 💃
Akanfaninmu na""R & U""Global Enterprise Dake Nan Garin Minna Niger State, saikunzu..........

Ga numbern mu kamar haka👇
08062160424
08066891424.....

Sayan day'a ko sari acikin farashi mai sauqi👌
Kubamu odern ku,danshine aikimmu akoda yaushe da yardar Allah........👌
Sai an gwada akansan na kwaraiiii💃💃💃.....

Page 103

Washe gari bayan sun tashi da asuba, taimaka mai tayi yayi alwala ya tafi masallaci, ita kuma a nan dakin nashi tayi sallah bayan ta idar zama tayi tayi azkar da sauran addu'o'i da takeyi, a karshe ta roƙi Allah yaba Aslam lafiya, alkur'ani ta dauka ta shiga karatun a bayyane.

Bayan an idar da sallah a masallaci, shima dai zama yayi a can yayi dukkan addu'o'i shi a karshe ya roki Allah yasa Asmah ta soshi koda Rabin sonda yake mata ne, Allah ya kawo mishi karshen komai cikin sauki, daga nan kuma gida ya dawo direct.

Tun daga bakin kofa yake jin zazzakar muryarta tana karanta alkur'ani mai tsarki cikin suratur nisa'i, dakatawa yayi daga sallamar da yayi niyya, ya tsaya yana saurarenta yana lumshe idanu, godiya da kirari ya shiga jerowa ubangiji daya mallaka mishi Asmah a matsayin matar sa, take kuma zee ta fado mishi a rai, ya tuna fama da gwagwarmayar daya ke sha kullum idan yana koya mata karatu, sai ranshi yayi matukar baci, ya mata jan ido take maida hankali, kuma washe gari idan yace ta biya da'ker take iyawa.

Minti kusan 15 ya kwashe a tsaye a wurin yana saurarenta kafin kuma, a hankali ya tura kofar bakin shi dauke da sallama, bata amsa ba saida takai wayar da take karantawa sannan ta yi sadakallahul azim, ta amsa sallaman shi, kara sowa ciki yayi ya zauna a bakin bed, addu'o'i tayi ta shafa sannan ta juyo ta kalleshi tace mashi "in kwana Mr Aslam " murmushi yayi cikin jin dadi ya amsa mata da "lafiya lau, kin tashi lafiya ya hidima dani" martanin murmushin ta mayar masa sannan tace"lafiya qlau alhmdllh ya jikin ka" ya amsa mata da cewa "da sauki"tace "Allah uban giji ya kara afuwa, ni zanje nayi wanka a dakina, daga nan zan shiga kitchen me kake so na girka maka" shiru yayi kafin yace "yau dai na baki zaɓi ki dafa duk abinda kike son ci nima zanci" OK kawai tace sannan ta tashi ta nade pray mat ɗin ta ajiye a ma'ajiyar sa ta fice daga dakin,

Dakinta ta je ta fara gyara wa ta share duk da ba wani datti yayi ba, tana gamawa ta shiga toilet dan tayi wanka.

Bayan fitar ta zama yayi ya dauki alkur'ani data ajiye yana karantawa shima, daga gefen sa wayar sa dake ajiye ya fara ringing, daukan yayi ya duba mai kiran, Amir ya gani dan haka ya saki murmushi kafin yayi picking call ɗin yana dagawa daga cen bangaren Amir yace"sannu hakimi, wai har yanzu baka gama cin amarcin bane, yau wata nawa rabonka da da kaje office" dariya Aslam ya kwashe dashi sannan yace"yau kuma wutar masifa ke cinka, naga ko gaisawa bamuyi ba ka hauni da tambaya" Amir yace"abin naka ne ai ya fara wuce gona da iri idan ka ajiye aikin ne sai ka faɗa kawai ayi replacing din wani da kai, haka kawai kabar dan taliki da aiki,kai kana na can kana sharban amarci kama manta da mutane idan ba mutum ya kira ka ba kai baza ka kira ba" Aslam yace"sannu daddy ai sai kayi replacing dina da wanin mu gani, da kake ta wani maganar amarci amarci, ni na gaya maka amarci nake sha " dariya Amir ya kwashe dashi kafin yace"ai nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya" Aslam yace " kai dai bari kawai ka tayani da addu'a ina nan inata kokarin kafa gwamnatina" Amir yace "rannan muna waya naji ka sako min wasu soki burutsu" kwashewa da dariya Aslam yayi, take kuma ya shiga bama Amir labarin abinda ke faruwa.

Kyalliyarta tayi kamar kullum sai tashin kamshi takeyi, fitowa tayi ta nufo hanyar kitchen don hada musu breakfast,kunun tsamiya takeson yi yau da alale, la'akari da tayi da bai da lafiya bakin shi ba dadi ƙila zaizo Abu mai dan tsami tsami, har ta dauki sacet din garin kunun ta fara gwabawa sai kuma ta tsaya tana tunanin anya zai sha dan dai ko a gida bata taba ganin yasha wani kunu ba inba na gyada ba, zuciyarta ta bata shawara da cewa kije ki tambaye shi mana, ki cire kokwanto aranki, shawaran zuciyarta tabi ta ajiye kwabin da tajeyi ta nufi dakin shi.

Daidai lokacin Aslam ya fara ba Amir labari, har takai hannu zata tura kofar ta tsinkayi muryarsa da abinda yake fadi cike da nishadi yake bada labarin, yanayi yana kwasan dariya, kusan suman tsaye tayi a bakin kofar nan, kanta ya daure, yanzu dama duk wannan rashin lafiyar na Mr Aslam na karya ne dama pretending yake yi, yaji sauki tuntuni, take taji ranta ya baci, tunani ta shiga yi ta shiga ne kota koma, wani zuciya ya bata shawara ki shiga kawai ayita ta kare, dakewa tayi ta tura kofar ta shiga ranta a bace, ya juya baya baima San da shigowarta ɗakin ba daidai lokacin Amir yana cewa"lallai Aslam ka cika ɗan air, wato sanyi kakaji zai kashe ka ta rungume ka ko" kwashewa yayi da dariya yace "baiwar Allah har hawaye takeyi saboda tsabar tausayina, haka zataji tana sannu Mr Aslam jikin ne innalillahi na shiga uku,dan Allah Mr Aslam karka mutu" yana mganar ne cikin kwaikwayon muryarta, suna dariya shida Abokin cin mushen nashi,dai dai time d'in kuma Allah ya bashi ikon juyowa, idanunshi ya sauka a kanta ta rike ƙugu tana wani huci, take hantar cikinsa ta kaɗa gadaishi rike da waya a hannu, shi tsoran shi daya baisan tsawan lokacin data ɗauka tsaye tana sauraran shi ba, duk da haka bai karaya ba , maida murya yayi ya komar dashi na marasa lafiya yace"wlh dan uwa husnah yar Aljannah ce tana kokarin kula dani sosai, tana da zuciya mai kyau" yanayin yana dafe kirji yana sakin yan ƙananun tari, daga daya bangaren Amir najin haka ya gane abinda ke faruwa, shiru yayi yana suraren diramar nan, yana jin nishadi.

Harara ta wulla mai tare da cewa "yau dubun ka ya cika kabar wani pretending na gano ka, sannu da kokari ka kyauta" iya abinda ta iya fada kenan ta juya ta fice daga dakin, kasa koda kwakwaran mosti yayi, gadai waya a kunnenshi har zuwa wannan lokacin ya kasa saukewa,a baiyane ya furta"innalillahi wa inna alaihi rajiun shike nan ta kare min "daga can bangaren Amir ya kwashe da wani irin dariyar keta don duk abinda ke faruwa yana sauraren su, sai lokacin ya tuna wayar ma a kunne take Ashe budar bakin shi sai cewa yayi "Allah ya isa tsakanina da kai Amir, ina zaman zama na da safen nan ka jawomin tonuwar asiri" cikin dariya Amir yace"Allah ya kara sauƙi Mr Aslam sai munzo dubiya, ka gaida min kanwa da kokari " tsabar haushi yanke wayar yayi, tare da yin jifa da shi Allah ya taimaka ya fadi akan gado.

~BATOOL~
Chapter 70 · 0% Book details