Sashe 125
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ya tashe su, wankan ta tayi tayi shirin barcin ta , biyowa tayi ta falo domin ta kashe wuta da sauran su, kamar a mafarki taji ana dannan doorbell, bata yarda ba ta dauka kunnen ta ne, sai da ta sake jin na biyu sannan ta yarda,da dumbin mamaki ta isa wurin kofar ta leƙa ta wurin lekawa, Aslam ta hango sai fuskar shi wasai alamar yana cikin matsanancin farin ciki, sai da gabanta ya dan fadi "me Kuma ya dawo da shi ta tambayi kanta." Jiki ba kwari ta bude mishi kofar, shigowa yayi da sauri tare da caɓe ta ya daga sama ya shiga juyo da ita a tsakiyar falon, mamaki da tsoro ne suka kamata mustu mustun kwacewa ta shiga yi, ganin haka yasa ya sauke ta yana dariya , a mamakance tace "lafiya honey mai ka dawo yi," yace "na roko mana kwana ne gurin my luv yar albarka sati daya na tambaya amma tace ta bani biyu, wlh bakiji dadi ba kamar na goya ta dan farin ciki." Magana yake yi cike da tsantsar farin ciki, hannu ta daura akai tare da cewa "innalillahi wainnailaihi rajiun. Ya Aslam me yasa kayi haka." Bai damu da yanayin taba yace "saboda bamu gaji da juna ba, ko ba yanzu kika ce kema baki gaji dani ba to kamme zamu cuci kanmu ga hanya mafi sauki, roko mana ita nayi ta ara mana kwanakin ta Kuma ta bamu harda kari, naga ai ba haramun bane yin hakan ko?" Lokaci daya taji tausayin zee ya lullubeta har saida hawaye ya ziraro mata, ganin haka yasa ya cira ta sama ya nufi hanyar bed room yana cewa"nifa ba kuka na dawo kimin ba dawowa nayi muci gaba da shan amarcin mu, kin gane ko beb, bari ma na dumama miki sauran kazar ki ta jiya kici dan yau ma ba sauki." Jin hakan yasa ta fashe da kukan shagwaba tana cewa "ni bazan ci ko wani kaza ba wlh, Kuma daga yau na daina cin kaza a gidan nan." Dariya ya saka mata da haka suka shige bedroom din ya turo kofar da kafa, saura kadan ya buge min katon hancina ni mai dauko rahoto yau dai ban samu shiga bed room ba balle naga yadda wasan zai kaya, dan haka na lallaɓa na fito na nufi part din zee dan ganin yanayin da Mr Aslam ya barota.