← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 126

Sashe 84

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isa kofar gidan motar Abban hanifa na shawo kwana ta dayan hanyar, dukkansu kusan a tare sukayi parking nan suka shiga gaisawa, Dr bash sai lokacin yamai barka baki da baki, nan kuma ya kira Rabi'ah ya gaya mata gashi dasu Aslam, sannan suka shiga, bama kowa a falon duk suna ciki, zama sukayi Abban hanifa kam dakin shi ya nufa, basu fi 5 minutes da zama ba Ummi tayi sallama a falon, fuskar washe take cewa "oyoyo yarana sannunku da zuwa ina azkar naji Rabi'ah na fadin isowarku" daidai nan ta karaso ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, Dr bash ne ya fara saurin sauka daga kan kujera ya shiga gaisheta tare da mata barka da isowa lafiya, Aslam kam matsawa yayi gabanta ya tsuguna tare sa kamo hannunta daya ya rike fuskar shi cike da farin cikin ganinta yace"sannu da zuwa ummi fatan kin iso lafiya," murmushi tayi tana daura daya hannunta akan tarin suman kanshi, tace "lafiya qalau my son fatan na sameku lafiya" yace "lafiya qlau , nayi kewarki sosai ummi " tace "nima haka my son, ya aiki ya iyali" yace "alhmdllh ummi" tace "masha Allah, Allah ubangiji ya muku albarka, baki daya,ya karamuku zaman lafiya da kwanciyar hankali ya Baku zuri'a dayya ba" kusan haɗa baki sukayi dukkansu bashir, Aslam, ya Rabi'ah da batool da fitowarsu kenan daga ciki da kuma Amir da shigowar shi kenan falon, gurin cewa "amen ummin" sai sannan ta sauke hannunta akan Aslam shima sakin hannunta yayi ya nemi guri kusa da kafarta ya zauna, Amir kuwa hannu yaba Aslam da Dr bash sukayi musabaha, sannan ya tsuguna ya gaida ummi, kafin ya koma kusa da dr bash ya zauna, ya Rabi'ah data zagayo ta zauna kusa da ummi ne tace "ya Aslam ya Amir da Dr ina wunin ku" Amir ya amsa da lafiya qalau sisto, Aslam ya amsa da ina gajiya yayinda Dr bash yace lafiya qalau anty Rabi'ah barka fa Allah ya raya, da amin suna amsa, batool ma karasowa tayi ta gaida Aslam da Amir ta nemi guri ta zauna, a fakaice Dr bash ke hararanta,ganin ta gaida kowa ban dashi, hararanta ummi tayi tace "shi bashir din uwa ya kashe miki hala" kallon ummi tayi tana dan zumɓuro baki sannan ta kalleshi tace "to ina wuni" duk dariya suka saka mata, banda Aslam daya kalleta ya dauke kai, shifa har yanzu baijin zai iya sake musu fuska , don rashin son raini a jninsa yake, Asman shi ne kawai zai laminci ta raina shi ita ma albarkacin soyayya.

Daidai nan Amira ta shigo falon samun tayi suna dariya, bata San ko na meye ba, ta dai ƙaraso, zama tayi a hannun kujera kusa da ya Rabi'ah ta kalli su Aslam da Dr bash ta gaishesu a tare, amsa mata sukayi, gaba daya, sannan ta maida kallonta kan Amir da tunda ta sawo kai falom yake ta binta da kallon luv yana murmushi tace "yayana barka da dare, ka dawo lafiya ya aiki" fuskar shi a washe cikin farin ciki da annashuwa ya amsa mata cike da kulawa, ya Rabi'ah tace "oh ni Rabi'ah duniya mutane kala kala wancen taki gaida nata mijin,wannan kuma saida ta ware shi dabam sannan ta gaishe shi bata hadashi cikin jam'in mutane ba,lallai yaran mummy kuma sha'anin ku, kai kuma ya Amir babu ko kunya kake mata irin wannan kallon a gaban mu " hararanta Amir yayi, sukan dan taba wasa da Rabi'ah kasancewar su abokan wasa, ummi ce ta kalle ta tare da cewa "ya isheki haka Rabi'ah saka idon ki ya fara yawa ina ruwanka wai" dariya ya Rabi'ah tayi.

Su Asmah da zahra da khadijah ma fitowa sukayi bayan gaisuwa suka zazzauna aka shiga dan fira jefi jefi, ya Rabi'ah ta mike ta kawowa su Aslam Abinda tabawa, Abban hanifa ne ya fito yayi wanka ya canja kaya, kallonsu yayi yana ba amir hannu Wanda shine basu gaisa ba yace " Ah'ah guys kuce duk kana nan kenan" matar shi ta amsa da "ba dole ba kowa ya biyo sahu" dariya yayi sannan ya shiga gaisar da ummi, daidai nan kuma aka fara kiran isha'e, kallon yayi yace "nidai nayi masallaci" Amir ne ya mike tare da cewa "muje nima" sauran ma suka mike, Aslam ya kalli ummi yace" umminmu bari muyi sallah" tace "to sai kun dawo" sannan suka fice.

Suma matan ciki suka koma sukayi sallah, dama sun riga sunci abinci, nan ummi ta bude jakar Asmah ta kwaso sauran magungunan data bata tace "karbi ki shanye ki bani hannu tunda kinci abincin anan shikenan yanzu inkinje gida ba lallai kisha ba" saida ummi ta mata kat a lokacin nan, sannan ta barta haka.

Koda su Aslam suka dawo basu shigo ba' Abban hanifa ne daya shigo ya shaida musu, mazajensu na jiransu waje, kowacce kuwa ta tattaro kayanta sukayi sallama da ummi suka fito har main falo suka rakosu, har Asmah zata fita daga falon ummi ta kira ta a kunne ta raɗa mata "daga yau ki dinga mayar mai da martanin kinji" cike da kunya ta gyada kai, Rabi'ah data gama kasa kunne bata jiyo komai ba tace"wai umminmu nifa ban gane ba" ummi tace "ai baza ki gane ba rabi, kuje oh abinku karku ɓata musu lokaci sai da safe, kuzo gobe da wuri kunji ko" da to ummi suka amsa sannan suka fice.

Kowacce motar mijinta ta shiga suka dauki hanyar gidansu,suna fita layin kamal na shigowa, shima bai wani dale ba ya dauki deejanshi suka wuce.

A hankali yake tukin cike da kwarewa, zuciyar shi kuwa cike take da annashuwa, yanayi yana kallon ta yana murmushi, itakam Asmah gaba daya hankalinta naga maganganun da sukayi dazu da ummi, babu abinda yafi tsaya mata arai irin cewa da ummi tayi, ta dinga mayar mai da martani, Aslam ganin tayi nisa yasa ya kunna wakar *saida ke* na hamisu bireka yana bi a hankali, sautin wakar ne ya dawo da hankalinta kanshi a kan dan bakinshi ta sauke idanunta inda yake motsashi a hankali yana bin wakar.

Karki barni, sahibaaata♪
Karki ƙini ki fahimmmta♪
Saidake zani huuuta♪
Zuciya ta dake ne ta lallabo♪
Ta amince ki madani dan dako♪

Shiru tayi tana sauraren wakar da yakeyi, har cikin zuciyarta ko wani baiti daya na wakar ke tabawa, ji take kamar ita aka rairawa wakar,har suka karaso gida babu Wanda yayi ma wani magana cikinsu, bayan ya kashe motar yayi parking, zagayowa yayi ya buɗe mata kofa, dagowa tayi ta kalle shi fuskarta dauke da murmushi tace "nagode Mr Aslam" kashe mata ido yayi tare da cewa "u ar wlcm" fitowa tayi ya kulle motar tare da daukar Jakarta suka shiga ciki, suna shiga falo ya zauna a kujera yana cewa "wash yau nagaji gaba daya jikina ciwo yake min" ita kam Jakarta ta dauka tare da karasawa ciki, wanka tayi ta shirya cikin kanana kaya marasa nauyi tayi wanka da daddaɗan turarenta sannan ta fito fallon, tana baza kamshi, a tsaye ta same shi, yana niyyar shiga ciki, kallonta yayi tayi mai kyau sosai, murmushi ya sakar mata tare da cewa "har kinyi wanka," murmushi tamai itama ba tare da ta tanka ba, yace "to nima bari nayo nazo ki bani labarin abinda ya faru yau a gidan aikin suna" tace "aiko je ka dawo kasha labarai bari na Samar maka abinda zakaci kafin ka fito" yace "OK tnx" ya wuce ya shiga ciki ita kuma ta wuce kitchen.

Jelop din spaghetti da yaji kifin gwangwani da kayan lambu ta mai, sharp sharp kuwa ta gama ta kwashe, ta kawo dinning , tana cikin jerawa ya fito shima cikin ƙananan kaya, kujera yaja ya zauna, tare da cewa "masha Allah yar aljannah sannu da kokari" murmushi tayi tare da daukar plate ta shiga serving dinshi, shake plate tayi taf sannan ta tura mai gaban shi, fork ya dauka ya d
ɗibi taliyar ya kai loma daya bakin shi, ajiye fork din yayi yana lumshe ido tare da muymuy da baki, hannu yakai ya rike kunnenshi daya yana murzawa yana gyada kai, tana ganin ya fara haka tasan karshen maganar, dariya ta kwashe dashi,tana cewa "zaka fara kenan ko" bude idanu yayi yana murmushi yace "to aike ne wlh kin iya girki mai dadi da saka mutum santi, test din girkin ki daya dana mummy, kai naki ma yafi nata dadi, dan yanzu ita tadan manyanta komai nata ya rage quality" zaro ido tayi tace "innalillahi Mummyn kake cema haka, to kuwa sai na gaya mata" dariya ya kwashe dashi yana cewa "ai nasan baza ki iya bane yarinya", haka yake ta cin abincin suna fira cikin nishadi harya kammala.

Falo suka dawo ya zauna akan 3 sitter tare da daukan remote yana chanza Chanel, zuwa tayi ta kwanta a kujeran daya zauna tare da yin pillow da laps dinshi tana kallon fuskar shi, shima kallonta yayi bayan ya gama canza Chanel din ya saka Wanda yake son ya kalla, kashe mata ido yayi tare da cewa yanzu kuma sai ki bani labarin abin da ya faru yau a gidan Rabi'ah, murmushi tayi tare da cewa "oya karkabe kunnenka kasha labari" karkabewan kuwa yayi, tiryan tiryan ta fara bashi labarin tun daga zuwanta gidan irin rungumar da suka ma juna ita dasu batool da irin farin cikin da sukayi na ganin juna, har aka gangaro batun ciki.

Kallon fuskarta yakeyi, babu ko keftawa zuciya cike da wani irin rauni, tunda ta fara bashi labarin batun cikin da yan uwanta keda shi zuciyar shi ta karye tausayin Kansu ya kamashi, daga yanayin yadda take bashi labarin cike da zakuwa da shauki ya tabbatar mai da abin ya shigeta sosai, take yaji a zuciyar shi ya zama wajibi yau shima ya ajiye duk wani Abu gefe ya kusanceta, ko suma zasu samu nasu cikin, gefe guda kuma ga bet dinshi da Dr bash dake dawo mai dalla dalla a zuciya kamar a yanzu suke kullawa.
Chapter 84 · 0% Book details