← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 126

Sashe 114

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yadda suka saba gudanar da harkokin su haka suka gudanar babu wani canji a tare da su, sai dai yau Asmah ta dage a part ɗin zee za'a shirya dinner tunda a nan Aslam din yake,in yaso idan ya gama zai kwanta sai ya dawo nata dakin har zuwa wani daren tun da ya ce kwana 1-1 zasu yi, koda ya dawa ɗakin Asmah ya fara biya wa ko zama bata bari yayi ba ta kora shi wajen zee, da da daddare kuma da zai yi dinner ya saka zee ta kira ta suka yi tare, ya kuma ce kullum tare zasu dinga yi duk wacce keda miji a je part din ta ayi. Da daddare Bayan ya sallami zee guraren karfe 9 ya dawo part din ta yadda ya din ga rawan jiki a kanta sai da abin ya daure mata kai, zaka rantse irin kamar wanda yayi wata da watanni bai kusance ta bane, sai sambatu yake yi, yana saka mata albarka tare da yabo yana cewa ita ta dabam ce a cikin matan duniya dan Allah duk rintsi kar ta rabu dashi, kaza kaza haka yaita yi kamar zautattce wani abin ma bai San yana fada ba, ita dai mamaki ya ne ya cika fal, bayan sun nutsu yadda ya ringa tattalin ta kamar wani daren farko abin har dariya ya din ga bata, hakan ya faran ta mata ko ba komai ta ji dadi duk da ya dandani wata macen bai wofintar da ita ba, shikam ai sai lokacin ya ƙara tabbatar da darajar ta da kimar ta lallai ya tabbatar yayi sake a baya, daya bari ta subuce mishi, badan Allah yaso shi ba da duk wannan romon lagwalan daɗin bazai San akwai su a duniya ba.

Bayan wasu satittika gidan Aslam ya gama daidai ta, idan kaga yadda Asmah da zee suke gudanar da rayuwar su sai kayi rantsuwa ba kishiyoyi bane, sun maida juna kamar wasu yan uwa, suna girmama juna anty sama anty ƙasa basu taba bari wani sabani ya shiga tsananin su ba, sun haɗe Kansu ban da tattalin abin da zasuyi su faran ta ran Aslam babu abin da suke yi. Sai dai fa Asmah tana shan fama sosai da Aslam,kullum cikin taro shi take a kan hanya madaidai ciya idan ya bauɗe, tana namijin kokari wajen ganin cewa yayi adalci a tsananin su, sau da yawa har faɗa suke yi idan yayi wani abin daba daidai ba ta nuna mishi bai kyauta, amma faɗan baya nisa dan a take suke shirya wa, tana tausayin zee sosai dan takan ce, lallai Allah ya sota da rahama daya sa ita ce ta kasance abokiyar zaman ta idan da ta samu muguwa da wlh zaman gidan Aslam sai ya gagare ta, a dai yadda yake nuna yafi son ta karara a bayyane, kuma ko a gaban waye, sai dai itama zainab yana iya bakin kokarin shi wajen sauke duk wani hakki nata dake kanshi kuma yana bata kulawa kamar yadda yake ba Asmah, yana kuka matukar respecting dinta ganin yadda ta tsare girman ta ko a fuska bata taba nuna tana da muwa da wasu abubuwan da yake yi ba wata ran ma har yakan ji babu dadi shi karan kanshi, a gefe guda kuma ga kambun daya bata na uwar gida kuma wacce ta fara bashi farin cikin daya kasa samu a tare da Asmah wato haihuwa. Duk abin da Aslam yake yi zee bata taɓa nuna damuwa ba koda kuwa akan fuskar ta ne, takan kauda idanun ta idan yayi wani abin, ta riga ta sani takuma sadaƙar cewa Asmah ta yi mata fintinkau a zuciyar Aslam, tana tsananin kishi da Asmah sosai, amma kishi irin na matan annabin rahma, don duk abin da taga tayi na kwarai har Aslam ya yaba koda kuwa kwalliya ce ko girki kokari take ita ma ta takwatan irin shi kokuma wanda ya fishi koma wanda bai kai shi ba, a bangaren iyayen ta kuwa tana da labarin duk halin da suke ciki a wajen wan mahaifin ta Alhaji Abdur-rahman wanda dama shine ya shirya mata komai na tahowar ta Nigeria yana a Malaysia jirgin ta ya daga zuwa Nigeria hasalima shine yayi mata komai na barin kasar ita da ɗanta ba tare da sanin ƙanin nashi ba, jirgin ta ya daga da daddare da safe ya nufi gidan ƙanin nashi da nufin ya sanar dashi abin da ke faruwa kuna ya nusar da shi gaskiya shine fa ya tarrar ana tsaka dawan nan tataburzar.

Iyayen shi sunyi matuƙar farin ciki da wanan lamarin kuma hankalin su ya matukar kwanta wa ganin yadda suka haɗe Kansu abinda basu taɓa zaton zai zo da sauki ba, dama bata Asmah suke to ji ba don ita sun riga sunsan wacece ita su suka raine ta sunsan abin da zata iya da wanda baza ta iya ba, zee suke ji duk da kuwa ta ce masu ta shiryu, basu gaskata hakan ba sai da suka gani zahiran muraran, dan duk ran da zata je family hause tare suke zuwa, kowa a gidan ya shaida lallai Kansu a haɗe yake kuma suna gudanar da tsabtataccen kishi wanda da wuya a samu irin shi a zamanin nan na matan yanzu.

Duk wanda yaga Aslam yasan ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali dan har wani dan kiɓa yayi mai ban sha'awa, haka suma matan Asmah kam ta murje ta ƙara haske itama da dan kiɓa ta kara cika cif cif kamar yadda yake so, sai dai abin da ke bata haushi tumbi da taga yana son fito mata, haka kurum taga cikin ta na tasa wa alamar tumbi zata yi, tuni ta dena cin duk wani abu da tasan yana saka kiɓa da tumbi amma a banza abu sai ƙara gaba yake yi tun ba wanda ya kula har ta kai Aslam ma ya kula, aikuwa ya din ga mata dariya yana tsokanar ta ganin da gaske ba so take yi din ba. Cikin haka zee ta fara zazzabi koda akaje asibiti wai ciki ne dan sati biyu, zo kuga murna gurin Aslam da Asmah tuni suka fara buge bugen waya duk wanda suka kira yaji abin da ke faruwa sai yama Asmah kwallah dan tausayi tare da fatan itama Allah ya bata nata, yadda take farin ciki har taso tafi Aslam din zee kanta abin na matukar bata mamaki lallai Asmah daya ce tamkar dubu a cikin alumma samun kanta tayi da saka ta a addu'a itama Allah ya bata nata na kanta.

A can Malaysia kuwa a daidai wananan lokaci, ankai ruwa rana sosai da Dad lokacin daya farko ya ganshi a asibiti ciwon shi ne ya motsa sosai wanda rabon daya tashi yafi shekara ashirin tun zee na yar ƙarama, tun da ya farka bashi da wani abin fada sai daughter shifa a nemo mishi ɗiyar shi, ya ki kwantar da hankalin shi bare a samu ciwon ya kwanta,sai alluran barci ake ta ɗirka mashi, likitoci ma da suka ga abin yaki ci yaki cinyewa suka tambayi su mom wacece daughter ɗinnan ne dan Allah idan tana nan su kowa mishi ita, sai lokacin Alhaji Abdur-rahman yake sanar wa mom cewa shine ya fitar da zee da ɗanta zuwa Nigeria kuma yanzu haka tana ɗakin mijin ta, mom bata yi wani mamaki ba sanin halin Alhaji Abdur-rahman na ƴanci da son ƴaƴa, shifa duk abin ɗa yake so ko daidai ne ko akasin hakan baya taba hana wa, shi kuma kalar nashi jarabtar kenan, ta tuna lokacin auren zee da Aslam shine dai yayi uwa yayi makarɓiya, hankalin ta yadan kwanta tun da yanzu tasan inda zee take, duk da dama tayi zargin hakan.

Dabara ne ya fado mom nan ta samu Alhaji Abdur-rahman sanar dashi take suka haɗa baki yama Dad daɗin baki cewa anga zee ta dawo gida amma tace baza ta iya zuwa asibitin ta duba shi ba sabo da baza ta iya jure ganin shi a kwance babu lafiya ba yanzu dai ya daure a karfaffa jikin shi ya samu yaji sauki a samu a sallame shi yaje gida yaga zee, kamar wani ƙaramin yaro haka ya yarda da zancen su, dan da gaske zee ta kasance ita ce raunin nashi na farko a duniya kamar yadda yake faɗa.

Cikin kankanin lokaci ya wartsake aka sallame, dama Alhaji Abdur-rahman ya riga ya gama tsara yadda zai sanar dashi komai ya gayyato manyan malamai har su biyu da zasu mai wa'azi, tun kan akai karshen maganar da dai ya fahimci in da suka dosa ya birkice musu abin ka da jahilci zagi ta uwa ta uba, ya kuma lashi takobin zaije ya dauko yar shi koda da jan ciki ne kuma sai ya wulaƙan ta Aslam wulaƙanci mai tsanani,lamarin da yasa sukayi kaca kaca da ɗan uwan nashi ya gaggaya mai magana ya kuma ce yayi hankali dai da shiga lamarin aure da ma'aurata domin wani rabon tabbas yana kisa, ranar ya tattara ya dawo Nigeria rai a bace, yana dawo wa kuwa ya samu daddaɗan labari wai zee nada ciki, yayi murna sosai dan shima akwai son yara.
Chapter 114 · 0% Book details