← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 126

Sashe 66

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dago da kai tayi tana zare ido, idnunsu ya sarke dana juna,kallon juna sukayi na kusan 30sec, kafin da sauri ta yunkura ta dire kasa.

Daurewa yayi ya daddafa katakon gadon ya mike da'ker yana layi jiki ba kwari, yana mikewa kuwa jiri kwashe shi zai fadi tayi azaman taroshi tasa dukkanin ɗan karfinta ta rirrike shi a haka ta taimaka mai har suka shiga toilet, zaunar dashi tayi akan abin da ake zama a toilet d'in juyawa tayi zata fita karaf taji an riko hannunta, da sauri ta juyo ta kalle shi, marairaice fuska yayi kafin a hankali ya bude bakin shi yace"pls mrs Asmah ki taimake ni kimin wankan" wani irin zaro😳idanu Asmah tayi cike da tashin hankali.....

Tabdijam lallai Asmah kya zaro ido koni dake cikin Celine ina dauko rahoto saida na zaro ido😳balle ke

Oum ummeetarh
07041130088

..

Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARI NE MALLAKINA NE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌

(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira 👌 a kiyaye pls)

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiy,Allah kajiqan iyayen}

💖Tallah!💖 Tallah!!💖

💖Tallah!!!💖

💖

Albishirinku manyan mata! ma'abota kwalliya da
_Rantsattsun lesussuka💃,
_Atamfofi manya da k'anana💃
_Galla gallan shaddodi manya da k'anana muna da su kowani iri💃
_Akwai kuma yadiddikan maza kamarsu koranza,plan yard dadai sauransu💃
_Munada mayafai, takalman maza da mata,sarqoqi, awarwaraye,da duk sauran nau'ikan kayan ado na maza da mata muna dasu 💃
Akanfaninmu na""R & U""Global Enterprise Dake Nan Garin Minna Niger State, saikunzu..........

Ga numbern mu kamar haka👇
08062160424
08066891424.....

Sayan day'a ko sari acikin farashi mai sauqi👌
Kubamu odern ku,danshine aikimmu akoda yaushe da yardar Allah........👌
Sai an gwada akansan na kwaraiiii💃💃💃.....

Page 101

Ganin ta tsaya kallonshi tana zare ido yasa ya marairaice fuska tare da cewa"pls mrs Asmah ki taimaka min" ganin zai karyar mata da zuciya yasa ta fizge hannunta da sauri ta fice daga toilet d'in, ko hauka takeyi ita ta ina zata iya mai wanka katoto dashi, yanzu shi ko kunya sai ya iya tubewa zirr a gabanta, lallai maza sai abarsu, yoo shi baisan riga ma da babu ajikin shi daure kawai tayi ba, tunda ta cire mai Riga har yanzu bata yarda ta sake kallon shi ba, kunya takeji balle kuma ace ya cire harda wondo.

Saida ya kwashe kusan 15 minutes a zaune yadda ta barshi kafin ya lallaba, ya mike da'ker ya fara wankan, bayan ya gama lallabawa yayi, yayi brush da alwala da daddafa bango ya samu ya fito daure da tawul, bata dakin dan haka ya samu ya lallaba ya zauna bakin bed,

Asmah kam tana dakin tunda ta barshi a toilet, jin motsin zai fito ne yasa tayi sauri ta fice a dakin dan tasan ba kunya ya ishe shi ba kar yazo ya fito mata haka zirr, dining ta nufa inda kayan tea suke, nan ta samu Kofi ta hada mishi tea mai kauri da zafi zafin shi, saida ta kwashe kusan 15 minutes tasan dai duk tsiya zuwa wannan lokacin ya gama shiri ya saka kaya,daukan dan karamin tiran data daura kofin tea d'in tayi ta nufi dakin da sallama a bakin ta ta tura kofan dakin, yana nan zaune a bakin bed d'in tunda ya fito toilet ya zauna bai motsa a wurin ba jira yake tazo ta taimakeshi ta dauko mai kaya ya saka yayi sallah,

Kallo daya tamai tayi saurin dauke kai daga kallonshi gabanta na faduwa, lallabawa tayi ta duka kusa da kafar shi ta ajiye mai kofin tea d'in, tace "ga tea nan na hada maka kasha, sai kasha magunguna" mikewa tayi tana niyar barin dakin, dan gaba daya jikinta rawa yake yi, ganin shi zaune daga shi sai tawul,har takai bakin kofa ta tsinci muryar shi yana cewa"pls mrs Asmah karki barni, kizo ki taimakeni ki saka min kaya nayi sallah" daskarewa tayi a gurin bayan ta zaro duka idanuwanta waje,kamar wacce aka dannawa pause, a zuciyarta tace innalillahi mutumin nan na neman ya kasheni da sauran kwanaki a duniya, ta kasa juyowa tayi abinda ya sakata ta kuma kasa yin gaba, har kusan 3minutes a haka ganin da yayi bata da alamar yin gaba ko baya yasa ya kara cewa "pls to ko ciromin kayan kizo kiyi daga sif" jin haka yasa ta daure ta juyo bata kalli inda yake ba ta wuce gaban wardrobe din tace "wani irin kaya zan ciro maka" yace "kowanne" jin haka yasa ta duba side din da jallabiyas suke ta ciro mai wani sabo mara nauyi, ta duba gurin kana nan kayan shi ta dauko mai singlet da boxer ta hado mai dasu.

Mikamai tayi ba tare da kalle shi ba, amsa yayi da gangan ya hada harda hannunta ya riko, a zuwan bai sani ba,da sauri ta fisge hannunta,kallon yayi yace "oh sorry" cewa tayi "kasa kayan kasha tea din bari na baka waje" yace "ki tsaya pls karki wuce" kamar zata ce wani sai kuma idanunshi dake kanta suka mata kaifi da yawa, bata ce komai ba ta samu guri a gefe ta zauna ta juya mai baya, daga zaunen da yake ya saka boxer, singlet d'in ya dauka zaisa amma yadda zai daga hannu ma wahala yake bashi, yayi yayi ha saka rigar ya kasa, ita kuwa Asmah tunda ta juya mai baya bata juyo ba balle tasan wainar da yake toyawa, ganin bata da niyar juyowa balle taga halin da yake ciki ta taimaka mai yasa ya saki wani kara mai sauti"ahhhccchh" a firgice ta juyo ta kalleshi gani tayi ya dafe kirjinshi yana yamutsa fuska kamar kirjin na mishi ciwo, bata san sanda ta isa gabanshi ta rirriko shi ba, sai faman sannu take jera mai ba kakautawa,ganin haka tuni ya kara narkewa ya sake mata nauyin shi duka a jiki, tuni tama manta da kunyar da takeji na ganin shi ba riga, cikin yanayin zafin ciwo yake cewa"rigana, rigana ki sakamun Rigana" jiki na rawa ta dauki singlet din ta saka mishi, duk rabin jikinshi na najikinta, da'ker take iya ture shi taja mai singlet din da kyau, a haka ta saka mishi har jallabiyan ma, tanayi tana "sannu na saka maka , sannu sannu" gyada kai yayi yana yamutsa fuska, ya daddafa gado ya mike yana layi, tashi tayi zata rikoshi yace "shimfida min pray mat, nayi sallah" da sauri ta dauka ta shimfida mai, nan ya kabbara sallan a tsaye ya fara amma karshe a zaune ya karkare, dan da gaske yana jin jiki, dan ma yana da dauriya sosai ne.

Tana gani ya idar ta dauki kofin shayin ta mika mai, kin amsa yayi ya girgiza mata kai alamar bazai sha ba, marairaicewa tayi tace"pls ka karba kasha ko kadan ne sai ka samu ka sha magani" da gangan yaki karba so yake ya sakata ta bashi a baki, Asmah ta kada ta raya amma yaki karba, saida yaga tana niyyar fashe mai da kuka ya bude baki da'ker yace"to kiyi hakaru karkiyi kuka zan karba, amma bazan iya sha da kaina ba, saidai in zaki taimakeni ki bani a baki" dake a matse take da yasha yasa ta amince zata bashi d'in.

Gyara zama tayi a gaban shi tana dibo tea d'in da cokali tana kaiwa bakin shi, yana sha yana yamutsa fuska kamar baiso, dan samun guri ma, idan ta debo wani bin ma bai karba saiya gauce fuska gefe, kamar wani dan karamin baby, haka zata ta bin shi da cokalin duk inda ya juya fuska, sai ya gama wala ta ya amsa, a haka ya shanye tea tass ba tare da ya Sani ba, sai gani yayi ta ajiye kofin, kallon cikin kofin yayi yaga wayam, saida yadan zaro ido yana mamakin yadda akayi ya shanye tulin shayin nan shida baida lafiya, ko lafiyar shi kalau ma baya wani shan tea da yawa.

Tana lura da yadda ya kalli kofin yadan zaro ido hakan yasa tace "ko a karo maka ne" da sauri ya girgiza kai alamar A'a, tashi tayi ta fita da cup din can kuma sai gata ta dawo da goran ruwa mara sanyi da wani cup, komawa tayi mazaunin ta nada ta bude ledar maganin ta ballo mai duka Wanda zaisha a lokacin ta mika mai ba musu ya karba ruwa ta tsiyaya mai a cup ta mika mai, karba yayi yasha maganin, yana yamutsa fuska.

Cup d'in ta dauka ta mayar kitchen ta dawo, kallonta yayi ya nuna mata breakfast dinta da ta ajiye tun dazu har ya sandare ya huce, sai lokacin ta tuna bata karya ba, dauka tayi takai kitchen ta ajiye dan bata jin zata iya cin wani abinci a halin da take ciki a yanzu.
Chapter 66 · 0% Book details