← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 126

Sashe 104

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kam Aslam da wani irin kallon mai cike da tsantar mamaki yake bin ta, har ga Allah ya manta da ita gaba ɗaya a shafin rayuwar shi, bai taba kawowa a ranshi a kwai wata rana da zata juyo ya sake haɗa idanu da ita ba,tun daga ranar da ya mallaki Asmah,bai ƙara kallo duk wata diya mace da sunan mace ba, yakan tunata a wasu lokatan musamman idan yana cikin alhini rashin samun haihuwa, a duk sanda ya tunata ranshi ne ke mugun baci, bai taba tuna alkharin ta ba ko kaɗan, a duk sanda zai tuna ta baƙin ta kawai yake tunawa,nadama da dana sanin auren ta kawai yake yi a duk sanda ya tuno ta, sau da yawa yakan furta ta cuce shi kuma yana ji har duniya ta nade bazai taba iya yafe mata abin da ta mashi ba, shin me ya kawo ta gare shi a halin yanzu?

"Mommahhhhhh." Zazzakar muryar yaron ne ya katse musu tunani gaba ɗayan su, har cikin zuciyar shi sautin muryar yaron ya daka , kusan a tare dukkan su ukun suka juyo dan kallon mamallakin wannan muryar, ruɗu, al'ajabi, mamaki, ne suka ziyarci shi a lokaci guda, wani irin waro ido yayi waje yana kallon yaron da ke zaune a jikin hajiya mama yana yana miƙa ma zee hannu alamar ta dauke shi, Asmah kam suman tsaye tayi, take kuma a lokaci guda taji kibiyar so da kaunar yaron ya caki zuciyar ta, har sai da ta dafe daidai saitin kahon zuciyar ta, duka idanunta ta baza tana kallon tana yaro mai kama da Aslam ɗin ta sak kamar yayi kaki, shin ɗan waye wannan a cikin ahlinsu bata taba ganin shi ba, kuma dai kallo ɗaya tamai tasan lallai shi ɗin jinin ahlin gidan ne.

Gyaran muryar da Alhaji baba yayi ne ya dawo da hankalin kowa kanshi, kallon su yayi yace "Muhammad, Asma'u, zainab ku nemi waje ku zauna." Jiki a sanyaye suka nemi guri suka zauna, Asmah kusa da mummy ta zauna a tare da kwantar da kanta akan cinyar mummy Aslam kuma kusa da Abba, yayin da zee ta koma mazaunin ta nada kusa da mami ta zauna.

Bayan kowa ya nutsu ya bada dukkan hankalulin sa, kallon Abba Alhaji baba yayi yace "bismillah Yusuf a buɗe mana taro da addu'a." Amsawa Abba yayi da "to Alhaji." Kafin ya shiga kwararo addu'a suna amsawa da amin, bayan sun shafa addu'a, shiru falon ya dauka na yan wasu mintuna, sauke numfashi Alhaji baba yayi kafin ya bude bakin shi cikin dattako da kamala da Allah ya hore mishi yayi sallama cikakkiya, kusan gaba ɗaya hada baki sukayi gurin amsa sallamar shi, yace "alhmdllh alhmdllh alhmdllh har kullum ina godewa Allah daya bani ku a matsayin yaya da kuma jikoki na, Allah ubangiji ya muku albarka baki ɗaya." Da amin suka amsa gaba dayan su kamar ɗazu, yaci gaba"dalilin da ya saka na muku wannan kiran na gaggawa shine, maryam (mami) tazo ta same da wani lamari mai girman gaske, ba komai bane kuwa face, zainab matar muhammad wacce kowannen ku a nan yasan irin rabuwar da sukayi da Muhammad badan ya sake ta ba, da kuma dalilin rabuwar tasu, to sai gashi zainab ta zo gare mu tare da ɗa bayan tsowon shekara ɗaya da rabi wanda ta gabatar min da shi a matsayin ɗan Muhammad ne." Kusan kowa a falon saida ya dago ya kalli Alhaji baba cike da kaɗuwa jin Abinda ya faɗa,bama kamar Aslam da Asmah da suka fi kowa shiga shock, duk da cewa dukkansu tun kallon farko da suka ma yaron suka tabbatar da cewa lallai jinin su ne amma basu taba kawo cewa zai zama dan Aslam ba, duk da kuwa ganin zee da sukayi zaune a gurin saboda suna da labari duk abinda ya faru tsakanin ta da Aslam wanda har hakan yayi sanadiyar faruwa a bubuwa da dama a baya ciki harda rabasun da mahaifinta yayi na tsayin shekara ɗaya harda ɗoriya. Ci gaba Alhaji baba yayi da cewa "duk da ba'a gaban mu zainab ta haifi wannan yaron ba jikina da zuciyata sun gama aminta da cewa lallai wannan yaron jinina ne, amma dai kafin mu yanke kowannen hukunci akan wannan lamarin zamuso ji daga bakin zainab shin ta yaya a kayi cikin da kowa ya tabbatar da zubewar shi ya rayu." Ya karashe maganar tare da kallon zee dake zaune kusa da mami kanta a kasa tana sauraren shi, dukkan su kuwa ita suka zubawa idanu alamar suna son jin Karin bayani daga bakin ta kamar yadda Alhaji baba ya umurta.

Ɗago da kanta tayi ta kalli little da ke ta wasan shi a hannun hajiya mama, take kuma wasu siraran hawaye suka ziraro mata, a hankali cikin sanyin murya da sanyin jiki ta shiga basu labarin abinda ya faru tun daga auren ta da Aslam da haɗuwar ta da beebaloo barin ta Nigeria halin da ta shiga bayan komawar ta Malaysian, bayyanar cikin little har zuwa haihuwar shi haduwar ta da Dr bala labarin beebaloo,da kuma dawowar ta Nigeria a karo na biyu domin ta zauna tare da mijin ta su raini ɗansu a gaban su.

Ta karashe labarin tare da fashe wa da matsanancin kuka zamowa tayi daga kan kujerar da take zaune ta sanya gwuwowin ta biyu a ƙasa ta haɗe hannayenta alamar roko da neman gafara, cikin kuka tace "ku dubi girman Allah da darajar da Allah yayi wa ma'aiki yaku wadannan ahli masu mutunci da karamci ku yafe min.a baya nasani na aikata muku abubuwa da yawa na rashin ɗa'a da rashin ganin girman ku da mutuncin ku a matsayin ku na iyayen mijina wanda nake tsananin so da son kasncewa da shi har karshen rayuwa ta, nasan ban kyauta ba kuma nasan ba Abu me kyau nake yi ba a lokacin to amma rashin ilmin addini da jahilci ke ruɗa na a waccen lokacin, amma yanzu wlh na sauya zainab din da kuka sani a da ba ita bace kuke gani yanzu a gaban ku, na muku alkawarin zaku same ni fiye da yadda kuka yi zato na, dan Allah ku karɓeni a cikin ku a karo na biyu." Ta kara she maganar cikin kuka sosai.
Gaba ɗayan su jikin su yayi matukar sanyi, irin su Asmah da mami kam tuni sun fara tsiyayar da hawaye, tsit falon yayi kowa da Abin da yake saƙawa a ranshi, mummy ce tayi karfin halin miƙewa ta ta isa wurin zee ta ɗago ta daga duƙen da take ta rungume ta a jikin tana bubbuga bayan ta alamar rarrashi, kafin kuma ta maida ta mazaunin ta nada ta zaunar da ita.

Gyada kai Alhaji baba yayi cike da tausayin zainab da kuma gamsuwa da tuban ta, domin kallo daya zaka mata ka tabbatar abin da take faɗa daga zuciyar ta yake fitowa, cike da isa da yarda da kai akan zantar da ko wane irin hukunci a tsakani ahlin sa yace "ya isa haka zainab mun fahimce ki, mun kuma yafe miki akan abin da kika mana kuma mun karɓeki a karo na biyu a matsayin suruka kuma jika a gare mu kije ku zauna tare da mijin ki da ɗanki da kuma abokiyar zaman ki." Da wani irin sauri Asmah ta sauke idanun ta akan Alhaji baba dake magana, kafin kuma ta juya da dasu kan zee da ake cewa suje su zauna tare, itama zee ɗin kan Asmah ta sauke idanun ta da suke nan gaje gaje da hawaye, kallo kallo suka shiga bin junan su da shi, kowacce da abinda take rayawa a zuciyar ta.

Muryar Aslam ne ya dawo dasu hayyacin su, cikin wani irin dakkakkiyar murya mai nuni da cewa abin da yake faɗi daga cikin zuciyar shi yake fitowa yace "Alhaji a gaskiya bazan iya zama da mace fiye da ɗaya ba ahalin yanzu ba, bazan iya haɗa husnah da kowacce mace ba a halin yanzu, bazan iya yin adalci a tsakanin su ba, idan kuma ka takura to lallai zaka jefe rayuwa ta cikin halaka."yana gama fadin haka ya miƙe tare da daukar little dake kan cinyar hajiya mama ya nufi har yar barin falon, har ya kai bakin kofar fita ya tsinci muryar daddy yana cewa "Muhammad kada ka kuskura ka fita daga falon nan, kuma umarni nake baka ba shawara ba."........

Oum Ummeetarh
07941130088
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya,Allah kajiqan iyayen mu}
Hg

*ASSALAMUALAIKUM SISTERS*

abun d mamaki u watan axumi yaketa qaratowa cikin Dan taqin lokaci,
Me kika tanadarwa kanki dama yaranmu yar uwa?
Munada kyawawan kayan Yara na dinki masu kyau sosay d bama zakice dinkawa akayiba yaro/yarinya sufito gwanin burgewa kowa yanasan barka,07046881166

Kayanmu sauqinsu yyi har kamar kyautane,zaki iya samunsu dga 2k harzuwa abunda yyi Sama,kizo kiyi sarin kayanmu kisamu alkhairi me tarin yawa,07046881166

Akway takalma Suma kyawawa dgakan 1k zuwa sama,07046881166

Sannan munada tsala tsalan frames d madubai n gyaran gida masukyau d arha sosay,07046881166

Akway leshina d atamfofi,abayas sewanda kikazaba duk a farashi mesauki,07046881166

Karna cikaku d surutu ku kira:07046881166 domin qarin bayani,karku manta alkhairin Tari maganin mantuwa zaku iyashiga Instagram handle namu don ganin kayayyakinmu: everythng_handmade,

Semunjiku 07046881166

Page 125

Cak ya tsaya a bakin ƙofar shi bai tafin ba kamar yadda yayi niya kuma bai dawo ciki ba kamar yadda daddy ya umarta, mummy ce cikin fushi tace "Wai ba dakai ake magana bane, kana jin mutanen." Daga yadda yaji amon muryar mummy yasan ranta a bace yake, take jikin shi gaba ɗaya yayi sanyi duk wani karsashi da yake da shi tuni ya neme su ya rasa, baya kaunar abin da zai sa mummy tayi fushi da shi komai ƙanƙantar abin yana gudun bacin ranta a duniya fiye da yadda yake gudun na kowa, ba ta da sauki idan tayi fushi, har gara Fushin daddy so goma akan nata.
Chapter 104 · 0% Book details