Sashe 80
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai gurin sha ɗaya ta farka, lokacin Aslam tuni ya Dade da tashi,lalubashi tayi taji baya kusa da ita, kallonta takai kan agogon bangon dake dakin, sha biyu saura ta gani, salati ta rafka, tare da dirowa daga kan bed din, ta nufo falo, bata gashi ba kawai sai ta nufi kitchen da nufin ta haɗa musu breakfast mai sauki tunda lokaci ya kure har haka, yanzu fa kamata yayi ace tana shirye shirye daura abincin rana, tana shan kwanan hanyar da zai kaita kitchen ɗin tunkan ta karasa taji wani azababen kamshin na mata sallama da sauri ta karasa, ya juya baya hakan yasa baisan da isowarta ba, saiji yayi an rungume shi ta baya, murmushi yayi tare da cewa "kin tashi kenan" amsa ta bashi da "shine baka tasheni ba ko" ta faɗa kamar zatayi kuka yace "sorry bana son na katse miki barcin ki ne" tace "nidai ba wani wayo kawai kamin ɗan ka shirya breakfast ɗin kai kaɗai, kuma dai Allah ya tashe ni, sai ka barmin na karkare,mai gurin yazo mai tabarma ya nade" dariya ya kwashe dashi tare da cewa "kin makaro yarinyar saidai na gobe dan na riga na gama komai sai ci kawai ya rage" taya shi tayi suka kai abicin dining, nan suka zauna zaman ci yace shi zai bata a baki haka sukai ta cin abincin suna wasa kafin su Ankara karfe ɗaya, Aslam da gangan ya dinga mata wayau yana mata mata lokaci dan da gaske baya son fitar nan nata, amma ba yadda ya iya ne kawai.
Haka suka tayin komai a shiririce, basu suka shirya ba sai karfe uku, shima da'ker ta samu yayi wanka, dan da cewa barci zaiyi, gashi kuma su batool da Amira sai kiranta sukeyi anjita shiru, saida ta saka mai kuka, sannan ya mike kenan.
Koda yayi parking a kofar gidan ya Rabi'ah, da'ker ya bari ta shiga ciki, da cewa yayi ma zai jirata harta gama ta fito su tafi, saida tayi ta roƙonsa ya yarda zaije ya dawo, amma saita mai kiss, zaro ido tayi tana bin inda suke da kallo, ga mutane na gilmawa jefi jefi wasu a ƙafa wasu a mota, ga glass ɗin motar su farine ana iya ganin mutum kuma a sauke yake ma, ganin tayi shiru yace "uhummm ke nake saurare" wani dabara ne ya fado mata tace "na yarda amma nima da sharadi, zaka rufe idanunka tukum" bai kawo komai a ranshi ba ya rufe ido tare da cewa "oya bismillah" hannun ta takai saitin idanun shi tayi weaving taga bai motsa ba alamar dai ya rufe idon da gaske, miƙa hannu tayi ta buɗe kofar da sauri ta fice daga motar tana mai dariya, jin haka yasa ya bude ido, shima dai dariyar ya shigayi kafin cikin ɗan daga murya yadda zataji shi yace, "zakiyi bayani ne yarinya gobe ma ranace," gwalo tamai tare da shigewa get din gidan, saida yaga ta maida kofar ta rufe, sannan ya tada motar shi, yabar kofar gidan direct kuwa asibiti ya nufa gurin Dr bash dan sun kwana biyu basu hadu ba saidai a waya.
Gaba dayansu suna zaune a falon zagaye da umminsu da batayi awa daya da isowa ba, Asmah ce kawai babu a cikin su, fira akeyi cike da zakuwa da farin ciki da marmarin ganin juna.
Tun kafin ta karasa bakin kofar shiga main parlourn ya Rabi'ah takejin hayaniya da surutunsu na tashi, cike da zakuwa ta karasa baking kofar da sauri har tana dan haɗawa da gudu, gani tayi kofar a bude yake hakan yasa bata tsaya wahalar yin knocking ba ta faɗa falon bakinta dauke da sallama, daidai lokacin da ummi ke cewa Rabi'ah mikomin wayata na kira Aslam ɗin naji ko lafiya har yanzu bata iso ba, saijin sallamanta sukayi kamar daga sama.......
Oum Ummeetarh
07041130088
Share
Comment
Fisabilillah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 111
Cike da tsananin zaƙuwa dukkansu suka mike tare da rige rigen yi mata oyoyo, ƙamƙame juna sukayi gaba ɗayansu, suna tsalle kamar wasu ƙananan yara, ko nauyin jikin su basaji.
Sauran yan tsurarrin mutane dake falon tuni suka bar abinda sukeyi suka shiga kallonsu, sake juna sukayi kafin kuma ta shiga binsu ɗaya Bayan ɗaya tana rungumewa, lokacin data rungume Amira kam tsayawa tayi jin tudun Abu ya tokareta, dagowa tayi ta matsar da ita baya kaɗan tana ƙare mata kallo, tun daga sama har ƙasa, gane abinda take kallo yasa Amira saurin kai duka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta,Asmah ta bata kunya, kuma ga ummi a wajen, dariya ta kwashe dashi, tare da cewa "kaiii masha Allah Abu yayi kyau aure yayi albarka"
Ummi dake kallonsu tana murmushin ganin abin nasu bana ƙarewa bane yasa tace "to ya isa haka ku kyalemin ƴa tazo ta gaisa da umminta," sai lokacin Asmah ta lura da ummi aikam dai kwasa da gudu tayi ta faɗa jikin ummi dake zaune kan kujera, ta ƙamƙame, tana tsallen murna, ummi kam cewa take "yi a hankali Asma' u karki kada umminki" ina ko sauraren ummi batayi ba, saida taji muryar ya Rabi'ah a bayanta tana mata magana sannan ta sake ummin ta dago fuskarta fal farin ciki, duk sunyi cirko cirko a tsaye suna kallonta kowacce cikin matuƙar farin ciki.
Ya Rabi'ah tace, "yayi kyau wato ta ƙawayenki da umminki kawai kikeyi ko" ƙarasawa tayi ta rungumeta itama tana cewa "sorry yayana kema ai zan dawo gareki" ummi kam sai binta takeyi da kallo kuri, i tafa ta hanga ta hango bataga wani alamar cikin a jikin Asmah ba, idan idanunta ba karya suke mata bama sai tace taga kamar har yarzu a virgin dinta take, dan daga yanayin tafiyarta kawai ta gane hakan, dan ummi Allah ya mata wani baiwa irinsu ne matan da da summa mace kallon ɗaya suke gane yanayin da take ciki, shiyasa kallon ɗaɗɗaya tama su zahra ta gane kowacce nada kunshi, gabanta ne ya faɗi, jin tunanin daya faɗo mata arai na cewa to kodai har yanzu basu sasanta bane, tabdijam aiko da sake, bari dai ta natsu koma meke ciki zantaji.
Zama sukayi nan gaban ummi aka shiga firan yaushe gamo kowa na fadin irin yadda yayi missing din sauran ana dariya, batool ce ta kalli zahra ganin, yadda taketa zare idanu, yunwa takeji dan tunda ta samu cikin nan da taci abinci ko awa bata iya kaiwa zataji cikinta kamar anyi yasa, gashi daga zuwanta aka bata abinci taci, bai wani daɗe ba, gashi bata son tace zataci abinci kar suyi zargin wani Abu,dan kuwa a irin tulin abincin data narka ɗazu, idan tace tana, jin yunwa yanzu dole su saka mata alamar tambaya, itako baza taso haka ba, son kunya takeji , tunda tazo taketa muku muku da abinta, tunda cikin bawai ya fito bane, na Amira ne kawai ya fito sosai saiko na Khadijah wanda shima idan mutum ya kura ido zai iya gani, saidai fa ta makaro don tuni ummi ta gane kaf ciki ne dasu saidai bata nuna ma ta gani ba, batool tace "kekuma lafiya, kiketa muzurai kamar me jin kashi" hararanta tayi tare da cewa"A'a maijin zawo dai" dariya su Amira suka kwashe dashi, ummi tace "oh Allah na gode maka ni Amina, anyi aure, yau watan ku biyar rabonku da ganin juna amma hakan baisa kun fasa wannan hali naku ba ko, kullum kamar masu ganin hanjin juna minti biyu shiri minti biyu faɗa"batool cikin dariya tace "ummi kalla fa yadda take yamutsa fuska tana muzurai kuma kawai dan na tambaya sai ya zama laifi" ummi tace "to aikena bakiyi tambayar a mutunceba, ya zakice mata kamar maijin kashi" batool tace "wlh ummi nayi missing ɗinta ne sosai so nake mudan tuna baya" dariya suka sa dukkansu ummi tace "to kin kyauta" Zahra kuma tace "kedai wlh baza ki canza ba"Khadijah ce ta faki idanunsu ta saka hannu cikin dan pos ɗinta da tunda tazo yake kamkame a hannunta ta ballo farin kasarta(kalba) ta afa a baki tana tsotsa a hankali,Asmah data lura tace "sisto abin kuma yar haka ne, wani daɗi kika samune, kike ci ke kadai, to kowa yaci shi ɗaya ya mutu shi ɗaya" zaro ido Khadijah tayi jin Asmah daga zuwa zata tona mata asiri tun dazu take Ballan abinta babu Wanda ya lura sai ita, Amira tace"haba shiyasa tun dazu nakejin kamshi na buso ni to a sammana, tunda sai mun roƙa " ta faɗa tana mika hannu zata dauki pos dinta dake ita ke kusa da ita, aiko saurin tayi wuf zata kamkame abinta, saidai cikin sa'a Amira ta rigata fisgewa, cakumota tayi zata amsa da sauri ta wurgawa ya Rabi'ah, aiko tana caɓewa ta balle botir ɗin pos ɗin ta saka hannu a ciki, saiga farin kasa cike da Santana.