← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 126

Sashe 101

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan karon dai dama ta biyu fans an samu halarta, aiko dai da yawan su sukaje, dan wannan karan harda wadan da basu samu zuwa biki ba.sai ga su inna habee a bidda, su zainaba wannan karon dai babu kuka bakin nan har kunne, su sweetie an sako na kasan akwati, ranar gani ga daughter na sai shagwaba take zubamin, maryama uwar gida ce ta amshe mu da fara'ar ta, ta kaimu falon ta, su O'O sai zunlen ta akeyi ana dariya, nace ba rabi baza kiji tsoron Allah ba ko ina sai kin nuna hali, nan take ta shiga jigilar gabatar mana da abinci, kala kala harda su tuwon shinkafa miyar wake abincin nufawa, aiko dai duk shi suka rufar wa,ana shan miyan wake ana santi, nidai nace musu asha miyar wake a sannu,kakus ko dake cikin ta bai da kwari tun a gidan ta fara zawo, zainaba tsabar santi memo ta dauko wai dan Allah a gwada mata yadda ake miyar nan in ta koma garin su ta ringa yi, oum Aneesarh dake duk itama irin zahra ne banufe take aure ta gware a iya miyar wake, ita ta dinga koya mata yadda akeyi, sai ga inna habee ma ta dauko nata memon tana rubutawa teema kam data fara lashe plate saida ya koma kamar an wanke, anty mahmaa kuwa anga yan uwa sai yare take ta zuba wa ba kama hannun yaro.

Haka aka shiga gabatar da suna cikin farin ciki da annashuwa, yaro yaci sunan mahaifinta Barr, za'a kira shi da sultan.ana tsaka da shan suna mummy ta kira su batool ta haihu mace, nan fa aka shiga wani sabon farin ciki. Mami tace "ita kuma batula ana yayin samari sai ta tashi ta haifo kishiya ,to tunda dama bana gari ta haihu na bar ma mummy." Dariya suka saka mata ya Rabi'ah tace "Mami ya da saurin karaya haka tun baki ga kishiyar ba." Haka suka shiga wasa da dariya cike da farin ciki.

Lokacin da su O'o akayi arba da zahra duk rudewa sukayi, ta kara wani kyau tayi fresh duk yadda suke hasashen ta ta wuce nan, nan fa su zee da su rabi aka shiga kashe selfie nima dan kar a barni a Baya shiga nayi muka dinga dauka na samu na daurawa a status.

Washe garin suna su Asmah dasu mami suka dauko hanyar minna yayin da aka bar ummi akan sai ran suna zata zo ta koma ranar saboda ita ke kula da zahra a nan.

Batool anji maza wurin naƙuda abinka da mai baki, sai surutai kala kala take yi, ita karan kanta Dr dake amsar haihuwar duk tausayin ta saida batool ta saka ta dariya, Dr bash dama cewa yayi bazai iya karbar taba, dan koda ta fara a gida kasa tabuka mata komai yayi kamar ba likita ba, sai da ya kira maah kenan ta dauko wata likita makwabciyar su suka zo kenan, aiko yasha faɗa gurin maah kamar zata mare shi.

Bayan an mata wanka da babynta an kimtsa su, zuwa dare maah tace oya maza ya haɗa mata kayan batool zasu tafi, zaro ido yayi yace "maah me kika ce." Tace "gidan ku bashir abinda kunnayen ka suka jiyo maka shi kace." Gyada kai yayi a zuciyar shi yace akwai ƙura kuwa, ba yadda ya iya haka ya haɗa musu kayan ya kai mota ya zuba musu, sannan ya gaya musu ya gama suka fito suka tafi, ɗakin bash nada maah ta sauki batool kusan da nata ɗakin.

Bayan ya kaisu komawa yayi shima ya jido kayan shi sai gashi da katon a kwati mai taya yana ja, lokacin da ya shigo duk suna falo banda batool dake can kwance tana baccin huce gajiya. Su afifah sun zagaye maah suna kallon ta na gasawa yarinya cibi, an kashe fanka an kashe Ac falon ya dauki dumi sosai, duk idanu suka kwalalo mai, maah tace"ka manta ne da sauran kayan su batulan?" Yace "maah ba kayan su bane nawa ne?" Tace "naka kamar yaya, ko ka amso guga ne" yace cikin babbata rai dan ma kar tace A'a "maah nima na dawo nan Gidan da zama ne har san da zasu komo mu koma tare." Sallallami maah ta shiga, tare da cewa ",yau ni zuwaira naga karshen rashin kunyar yayan zamani, wato biyo matar ka kayi bashiru." Da sauri yace "A'a fa maah." Tace "to idan A'a ne ɓace min da gani kafin na sassaɓa maka." ta faɗa tana nuna mishi hanyar fita magiya ya shigo mata, har da cewa wai tsoron Gidan yake ji bazai iya zama shi kadai ba, harara maah ta watsa mai tare da cewa "to wlh sai dai in a baskwata zaka zauna don nan dai babu ɗakin zaman ka." Ba irin nacin da baiyi ba maah ta kafe kai da fata, dole haka ya amince zai zauna a BQ din ko ba komai kullum zai samu ya dinga ganin batool kafin ya fita da idan ya dawo.

A washe garin ranar da su Asmah suka dawo kowacce ta hallara agidan maah, don yima batool barka, nan fa suka ga baby kyakkyawa da ita kamar afnan sak, Asmah kamar ta hadiye babyn ko yan barka da'ker take basu sai anyi magana ma take mikawa, da kayi minti biyar kuwa zata amsa.

A haka sati ya zagayo akasha suna mai ƙaya tarwa yarinya taci sunan maah juwairiyya, z'ake kiran ta da Ummeetarh, saboda sunan uwar miji taci.

Duk wani gata da kulawa da mai jego ta zata biɗa batool ta samu fiyye da haka a gurin maah, ta tsaya kai da fata tana kula da ita fiyye da yadda zata ma su amrat. Tsakanin ta da Allah take mata komai, gafe guda Kuma.ga wani irin so da take nunawa baby Ummeetarh, daga ita harsu afnan,a hannun su babyn take wuni sai tayi kuka ake kawo mata ita ta bata nono su kara daukar ta.

A bangaren Dr bash kuwa dirama suke kwasa da maah sosai, kwata kwata ta hana shi sakewa ya kasa samun yadda yake so, daya lallaba ya shige ɗakin batool sun dan keɓe,minti biyu zata kwala mai kira, haka dole zafi fito yana gungumi, idan har ya samu ya zauna tare da ita ya Daɗe to a falo ne cikin mutane .

~MALAYSIYA~

Yau kimanin watanni biyar kenan bayan haɗuwar zee da Dr bala, tun ranar da ta ambata wa Dad zata koma Gidan mijin ta ya nuna bacin ranshi bata sake furta kalma makamanciyar wanana ba, ta kyale shi ta zuba wa sarautar Allah ido har zuwa iya wa'adin data dibar mishi, a bangaren mom kam tayi iya bakin kokarin ta sosai wajen ganin ta shawo kan Dad amma abin yaci tura, karshe ma yace idan ta sake tada mai maganar a bakin auren ta, tun daga lokacin ta saka ma bakinta ta sakata ta kulle bata sake koda bashi labari mai kama dana Aslam ba.

Yau ne ta kama little Aslam ya cika shekara ɗaya, kuma yau ne Dad shirya mai gagarumin taron birthday irin na ƴaƴan gata Wanda zee bata San da zancen ba don ita ma tana can tana nata shirin da ba Wanda yasan na meye daga Allah sai ita.

Karfe Tara na safe Dad ya fito daga dakin shi cikin shirin fita mom na biye a bayar shi, har ya sa kai zafi fita zuciyar shi ta kasa jurewa yau tun safe baiji motsin su ba, baiji ko da kukan little ba, alhali ba haka ta saba yi ba duk safiyar Allah takan fito ta iske shi a dakin shi ta gaishe shi ta bashi little su gaisa, yau gashi har zai fita bata zo ba kuma baiji koda motsin ta ba. Kallon mom yayi yace "dubo min daughter kiga ko lafiya yau kwata kwata banji motsin ta ba." tace "wlh nima haka, ka riga ni furtawa a baki ne kawai dama yanzu nake shirin in ka tafi na shiga na dubota"ta karashe maganar tana nufar hanyar dakin zee.sallama tayi shiru ba amsa haka yasa tayi knocking nanma shiru , kawai sai ta murda kofar ta shiga, tana shiga ba zee a dakin ba little hakan yasa tadan kasara bakin toilet tana magana don duk tunanin ta tana toilet saidai jin ba alamar motsin kowa a toilet yasa cikin tashin hankali ta tura kofar toilet din nanma wayam ba kowa, ai da sauri ta dawo tana gaya wa daddy bata ɗakin cikin mamaki yace "bata dakin! to ina taje" mom tace "wlh nima ban sani ba." Bai yarda ba hakan yasa ya nufi dakin zee din da kanshi mom ta rufa mai baya, yana zuwa ko sallama bai samu daman yi ba ya tura kofar ya faɗa ɗakin, karaf idanunshi ya sauka akan farar linkakkiyar paper akan makeken bed din ta ta daura Biro ta danne shi, baki na rawa ya nuna wa mom papern tare da cewa "meye wancen".........

Dan Allah ku dinga comment mu samu mu gama littafin nan wlh na gaji nasan Kuma kun gaji ko?

Oum Ummeetarh
07041130088

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}

*ASSALAMUALAIKUM SISTERS*

Abun da mamaki ta yanda watan axumi yaketa qaratowa cikin Dan taqin lokaci.
Me kika tanadarwa kanki dama yaran mu yar uwa?
Munada kyawawan kayan Yara na dinki masu kyau sosay d bama zakice dinkawa akayiba yaro/yarinya sufito gwanin burgewa kowa yanasan barka,07046881166

Kayanmu sauqinsu yyi har kamar kyautane,zaki iya samunsu dga 2k harzuwa abunda yyi Sama,kizo kiyi sarin kayanmu kisamu alkhairi me tarin yawa,07046881166

Akway takalma Suma kyawawa daga kan 1k zuwa sama,07046881166

Sannan munada tsala tsalan frames d madubai n gyaran gida masukyau d arha sosay,07046881166

Akway leshina d atamfofi,abayas sewanda kikazaba duk a farashi mesauki,07046881166

Karna cikaku d surutu ku kira:07046881166 domin qarin bayani,karku manta alkhairin Tari maganin mantuwa zaku iyashiga Instagram handle namu don ganin kayayyakinmu: everythng_handmade,

Semunjiku 07046881166

Page 123
Chapter 101 · 0% Book details