← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 126

Sashe 19

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

whatttt! Ya fada cikin tsawan da babai shirya ba, kafin daga bisani yakai hannu ya dafe kanshi ya shiga maimaita innalillahi wa inna ilaihi rajiun, can kuma ya tsinkayi muryarta tana cewa" ohhh na tuna wai wani wanka da akace anayin in mutum ya gama period ko , na tuna shi amma wlh na manta yanda akeyi, don so daya mom ta taba koyamin lokacin dana fara jini, tun ranar da ta koyamin ban sakeyi ba, cos koda na sake yin wani jinin da naje yin wankan sai na manta yadda ta koyamin ni kuma ban tambayeta ba," wani zafi yaji zuciyarshi ta dauka amma haka ya daure yace su je toilet d'in ya gwada mata yadda akeyi, ba wani damuwa a tartare da ita tace to, shima dan taga ya bata rai ne inba hakaba cewa zatayi yayi haquri next time tayi,

Shiga sukayi ta kunna tap na ruwan dimi, koya mata yadda akeyi ya shiga yi, yana fada tanayi inda ba tayi da kyau ba ya gyara mata, da suka zo gurin wanke kai saida ya tabbatar ko ina ya samu ruwa da kyau , suka gama suka fito, ranshi duk a jagule duk farin cikin daya kamata ace ango na ciki a washe garin aurensa shi baya ji saima akasin hakan dayake ji,

Haka ya shirya ya bar gidan ko breakfast bai tsaya yi ba , direct family house ya nufa sai saqe saqe yake a ranshi, shi wa zai tunkara da wannan babban matsalan, don wannan ba abinda mutum zaiyi shiru bane, Wannan wani arin musiba ne Allah ya jarabceshi da shi, yanzu wannan itace uwar ya'ya shi, wacce zata musu tarbiya,nononta zasu tsotsa, tab lallai akwai babban kura a gabashi, furzar da wani iska mai dumi yayi daga bakin shi, a hankali ya furta "ta ina zan fara ne," hmmmm ya sauke numfashi, kafin yace"ya Allah kaji kaina, astagfurullah na tuba"

(😅 tukunna ma mallam aslam baka tuba ba tukunna ,ai wannan shafin farko kenan, tunda kace iyayen ka basu iyaba, Kaine dan iya ,kai ka iya , sai kaje ka qarata da iyawarka, gaka ga zee, bakaga komai ba ma tukunna😕)

Yanzu wa zai fara tunkara, Amir? ya tambaya kanshi , tunda bashi da kamar Amir din , girgiza kai kuma yayi a fili ya furta "no ba amir ba,don indai ya bari Amir yasan da wannna matsalan to dariya zaimai,yakuma cemai Allah ya qara, alhakin Asmah da iyayen shi ne" mami ce next data fado mai a rai, take yayi na'am da wannan shawaran , don ita yafi sabawa da ita zai iya gaya mata komai, ba kamar mummy ba da bata wani sakewa da shi, mastsyin shi na d'an fari,

Da haka dai ya daure ya qarasa gidan,horn yayi, mai gadi ya bud'e mai get , parking motar shi yayi a parking lot, ya fito,da rabon zaiga abinda zai qara tayar , mai da hankali kamar ance ya kalli gefen daman shi ya hango, kamal da Asmah,

kamal na jingine jikin motar shi ,sai murmushi yake saki ita kuma ta juya baya tana facing kamal d'in, duk da baisan mai suke fad'a ba zuciyarshi ya bashi kalamai soyayya kawai suke gayawa juna, don wannan murmushin da kamal keta saki ba banza ba,

Take ya manta da matsalar data kawo shi ji yayi zuciyarshi ta qara daukan zafi, fiyeda da, wato har yanzu Kamal na nan akan bakan shi na cin amanar shi kenan ko, lallai kuwa zaiyi maganinshi yanzu yanzu nufosu yayi a zafafe gadan gadan kamar wani kububuwa, fuskar nan a murtike ,

(Duk dauka na zai je ya shaqe kamal ne kokuma ya wanwanke shi da mari, dan har na kwashi yan qafafauna nayi bakin get , da shirin kota kwana, na gyara riqon takarda da birona, amma ga mamakina sai naga, )

Ya zo ya wuce su, kamal na shirin gaishe ko kallon banza bai mai ba balle na arziki, sai lokacin Asmah ta ganshi , kamal cikin dan damuwa yace "meya same shi haka kuma" cikin nuna i dont care, Asmah tace"ohoo masa, shiya sani "

direct part d'in mami ya nufa, cikin sa'a ba kowa a main falo haurwa yayi upstairs , a falon sama ya sameta a zaune ita kadai, tana amsa call,

Mamin ganin Aslam a wani irin yanayi yasa tayi sallama da wacce suke wayar ba shiri , ita har ta tsorata wlh , ita tunanin ta qila amaryarce bai samu virgin ba, don ita yadda aka bata labarin zee har ce mata akayi tanabin maza,

(kunsan dai halin mutane da qara gishiri a miya, in sata kake ace harda maita😤)

Cikin dan shiga rudu mami tace "subhanallahi Aslam lpy meya faru"
Zama yayi da baya akan kujeran dake facing mami, yana furzar da hucin bacin rai,ruwan sanyi mami ta miqe ta dauko mai a fridge ta miqa mishi ya amsa amma still be ce mata komai ba sai huci yakeyi, sake kwantar da murya mummy tayi tace"tace pls my son gayamin abinda ke damunka zaka samu relief a zuciyaraka,"

Goran ruwan ya bude ya kafa kai saida ya shanye shi Tass,ya cillar da goran ruwan , bude baki yayi da niyyar sanar da ita kalar cin amanar da ake shirin yimai, a cikin gidannan, saidai kuma tuna wanene kamal a wajen mami yasa ya qasa gaya mata, sai tsintar kanshi yayi da fada mata maganar zee na rashin sanin komai akan addinin islama,

Kallon shi mami keyi quri, ta riga tasan wanene Aslam tun ba yauba, wannan abinda ya fada bai isa ya saka shi cikin irin wannan bacin ran ba , saidai in ba iyakar maganar kenan ba, ganin dai iya abinda ya fada kenan yasa bata takurashi ba, tace"sai hakuri Aslam kariga kasan wacece zainab da inda ka aurota don haka dole kayi hakuri da duk abubuwan da zaka fuskanta a tattare da ita , sai a hankali zata gyara wasu abubuwan, yanzu dai kaga ace mutum baligi baisan addininsa ba ai akwai matsala, kuma gashi yanzu Kaine mijinta duk wannan haqqin na kanka yanzu, don haka abinda zamuyi mafi sauki shine kai zaka dinga koya mata wasu abubuwan a gida idan ka samu lokaci, sannan kuma zan ma malamin da ke zuwa gida yana ma su zahra karatu, magana idan yana da wani sauran extra time sai ya dinga zuwa itama yana biya mata a gida. Tunda kaga yaro ne qaramin amma Allah ya bashi baiwar ilimin addini , idan kuma hakan bai yuwu ba da kaina zanje har islamiyar su ta nan bayan mu inda suke zura a weekend dinnan nayi magana da mai makarantan ya bamu malama mace da zata dinga zuwa gida tana koya mata mu gani, in Allah ya taimaka sai kaga an dace, ai ba a barta haka ba kodan tarbiyan y'ay'a nan gaba,"

Duk abin da mami ke fada Aslam jinta kawai yakeyi amma hankalin kacokam baya kanta, yana nan yana tunanin qila ma har yanzu suna cen tare suna cin amanar shi,

Itama mami ta lura hankalin shi baya kanta, ta sake cewa"to Aslam kaji yadda ya kamata muyi kenan ".

Aslam yace"to mami sai ayi qoqari a samu malamin, da wuri nima zan fara koya mata kafin nan," mami tace"yawwa to shikenan , kuma karka gaya ma kowa wannan maganar mu barta tsakanin mu. Kasan mutane yanzu gulma bata musu kad'an, ko cikin gidan ba Wanda zaiji indai daga bakina ne kar azo gaba a goranta mata, kasan mu mata sai a hankali, gaka da kanne mata karsu rainata"

Miqewa yayi yace" mami bari naje " to kawai mami tace mai tana qara jaddada mai yayi haquri da matarsa,

Ya fito part din mami gaba daya hankalin shi na parking lot, gani yayi basa gurin , bama motar kamal din kwata kwata a gurin sake birkicewa yayi , nan ya shiga tunanin ko tare suka fita, take yaji kamar jiri jiri na dibansa,

Sashen su na samarin gidan ya nufa yana shiga main falo ya nemi kujera ya zauna ya dafe kanshi da hannayenshi biyu ya runtse idanun shi, cikin yanayin dacin zuciya ya shiga furta" ni muhammad Aslam, ni za'a wulaqanta da raina da lafiyata, to wlh bazai yuwu ba sai dai ran kowa ya baci , a cikin gidan nan, don bazan taba bari hakan ta faru ba indai ina nunfashi a doron qasa, koda tsiya koda arziki sai na raba wannan cin amanar," shiru yayi yana girgiza kai can kuma yayi kwafa yaci gaba da cewa" kamal! kamal!! Kamal!!! Hmmmm wato har wuyanka ya isa yanka da zakayi takara dani ko, to wlh saina nuna maka kwaruru ba tsaran wake bane , ko banza na baka shekara uku a haihuwa , shekara uku kuwa ba kwana uku bane, inba ma rashin kunya da tsaurin idoba matata zaka aura, kana qanina "a bayyane yake duk wadannan sambatum, cikin fitar hayyaci,

Amir da tashin shi bacci kenan yayi wanka ya sakko dan zuwa part din mummy ya samawa kanshi abin tabawa, tun daga kan tsep yake ta jiyo maganganu kamar na Aslam, aiko dai Aslam dinne zaune a falo yana ta zaro zance kamar wani tababbe, zuwa yayi daf da shi , ganin Aslam d'in baima San da wanzuwar shi a gurin ba , yasa yadan duqa yana leqa fuskarshi tare da sauraren sambatun sa,

Amir bai fahimci komai ba yadaiji yace kamal zai auri matarshi, to wata matar zainab d'in kamal zai aura ko wa?

kasa haquri Amir yayi yace "zainab d'in kamal zai aura ? " ya fad'a da dan qarfi yanda Aslam zai ji shi, bude ido Aslam yayi akan fuskar Amir, yace ba zainab ba Asmah, Amir yace "Asmah! Asmah!! Wace Asmah dama kana da wata mata Asmah bayan zee da aka daura aurenku jiya " shi Amir kwata kwata bai kawo cewa Asman mummy yake nufi ba,
Chapter 19 · 0% Book details