← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 126

Sashe 89

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hango ta ummi tayi kan gado da sauri ta karasa tare da dagota tace "subhanallahi Asmah meya sameki, a ina kikaji ciwo garin yaya kuma" rasa amsar da zata ba ummi yasa ta fada jikinta ta fashe da kuka, aikuwa take ummi ta idasa rikicewa, take ta shiga cewa"innalillahi wainnailaihi rajiun, kai Aslam dan ubanka nace ka gayamin gaskiya mekefaruwa ne" ganin yadda ummi ta zubo mai idanunta masu kaifi akan su, yasa baki na rawa yace yana nuna Asmah dake rungume jikin ummi"ummi ki tambayeta ta gaya miki." Juyawa ummi tayi da sauri ta kalli Asmah tace"Asma'u meke faruwa." Itama shi ta nuna tace cikin muryar kuka "ummi ya gaya miki shi." Ummi ranta ya fara baci jin yadda suke ta gara ta kamar ball, ta dago a fusace da nufin ta balbale Aslam da fada, sai gani tayi wayam baya dakin, juyawa tayi kan Asmah tace "to tunda shi ya gudu ke gaya min, kokuma na hada keda shi na muku dukan tsiya, ladan ɗaga min hankali da kukayi da rana tsaka." Shiru tayi tana shesheka ita dai bata iya karya ba, gashi maganar ya mata nauyi, aiko ummi ganin haka tace a tsawa ce"ke nake saurare fa Asmah." Cikin sheshsheka ka tace "ummi shine fa jiya" sai kuma tayi shiru tana ci gaba da sheshshekan ta, ummi tace "uhumm ina saurarenki shine jiya me" tace "shine jiya bayan mun dawo gida ya umm, ya ." Sai kuma ta fashe da kuka ta kasa karasawa, zuwa yanzu ummi ta fara harbo jirgin su, wani ajiyar zuciya mai karfi ta saki jin abinda hankalinta kwata kwata bai je gurin ba.

"Kai amma wlh yaran nan kun shammaceni da yawa kun dauki alhakina." Ta karashe tana daga Asmah da tayi luf a jikinta tace "kalleni nan Asmah." Da'ker ta da go da fuskarta amma bata kalli cikin idon ummi ba, ummi tace"a gurin ne a kwai ciwo ko ina" a kunyace ta gyada kai, sannan ta daura da cewa "amma ya duba dazu yace babu ciwo." Ummi tace "kin tabbata ya duba." Ta sake gyada kai ummi tace "to tunda yace babu babun ne." Kin shiga ruwan zafi, nan ma ta gyada kai ummi tace "tun yaushe." Asmah tace "tun jiya."Ummi ta sake tambayar ta kuma gurin har yanzu yana zafi ta sake gyada kai, ummi tace "to baki gasu bane,ina zuwa ki gani" ta karashe maganar tana mikewa ta nufi toilet din dake dakin.

Ruwan dumi ta haɗa mata ta debo dan gishiri ta zuba sannan, tace oya ta taso, ganin yadda take tafiya yasa ummi tace "ah lallai baki gasu ba kam, da sauranki" suna shiga toilet ummi tace ta shiga ruwan, tsayawa tayi tana matsar kwallah, ummi tace "shiga mana, nemar miki lafiya na ke yi, yanzu idan baki gasu ba zuwa anjima yace zai koma ai baza kiji da daɗi ba, kuma nasan sarai ba lallai ya daga miki kafa ba, dan ku yaran yanzu ba kuda hankali ba hakuri ne da ku ba akan komai ba balle wannan harka." Cikin shagwaba tace "to ni ummi dan Allah ki fita wlh zan shiga." Tafa hannu ummi ta shiga yi, tace"ikon Allah, yanzu Asmah ni kike kora kar naga jikin ki, inda Aslam ne ai baza ki kore shi ba shi, yara muci kashin ku da fitsarin ku, amma ku raina mu haka, to shikenan ai kin huta, zan fita amma wlh in baki shiga ba kika fito zan gane, sai kin koma na gasa ki da kaina kuma da tafasheshen ruwa, kinji na gaya miki kenan," ta karkare maganar tana barin toilet din.

Sauke ajiyar zuciya tayi sannan ta tube ta lallaba ta shiga ruwan duk da kuwa zafin shi don yafi na Aslam daya hada mata zafi, dan taga gara ta shiga wannan kar taƙi ummi tazo ta sakata da kanta a tafasasshen ruwa.

Ummi kam falo ta fito Neman Aslam baya nan dakin shi ta duba nan ma wayam, nan ta shiga Neman shi cikin gidan saidai babu ko mai kama dashi, fita waje tayi ta samu Abban hanifa, yana ganin ta yace "ummi meya faru ne , Allah yasa ciwon da sauki" ummi tace "hmmm nura bar tuna min abin haushi, yaran nan ai sunci tuwo a kaina babu wani ciwon dake damun su fa, sheɗantaka ce kawai irin ta Asmah da Aslam."

Dariya Abban hanifa yayi, ummi tace "wlh kuwa nura, kaje abinda kawai Aslam zai maidani idan na gama" yace "to ummi sai kin dawo shima ogan yanzu naga ya fita mun gaisa wai zaije masallaci duk da naga kamar lokaci da saura" ummi tace "ai yasan tsiyar daya shuka, to ko Makkah zaije yaje ya dawo zai same ni ai" Abban hanifa yana dariya yace "umminmu adai mishi hakuri." Bata tanka shi ba saima cewa da tayi "to sai anjima nura saina dawo nima".

Koda ta dawo zama tayi a bakin bed tana jiran Asmah, saida ta kwashe kusan 30 minute sannan ta fito, dan itama kanta taji dadin ruwan sosai, tun daga yana yin tafiyarta ummi ta tabbatar ta shiga ruwan sosai bata ma kanta algus ba.

Kaya ummi ta Ciro mata masu kyau riga da skirt na atamfa ta saka, zama tayi a darare ta kasa hada idanu da ummi, dariya ummi tayi tace "um um amarya kinsha kamshi" cusa kai tayi cinyoyinta tana dariya, nan ummi ta shiga tsokanar ta kamar yadda takan musu wani lokaci lokaci idan ta kama, saida ta gama tsokanar ta, Asmah duk kunya ya cikata kamar ta nutse a kasa, sannan ummi ta daura da nasiha, ta shiga koya mata yadda zata ɗauke bukatar mijinta da kyau yadda bazai ma kalli wata mace a waje ba balle yayi sha'awa, ta gaya mata mahimmanci da tasirin tsarewa miji bukatun shi na shimfida keda shi, har akayi sallah suka gabatar tare da Samar wa kansu abin tabawa sukaci, suka dawo falo suka daura, daga inda suka tsaya, Asmah ta tattara dukkan hankalinta tana sauraren ummi, tana naɗar duk abinda ta gaya mata m card din kanta.

Aslam bai dawo gidan ba saida yayi sallan la'asar, duk tsananin shi ummi ta tafi musamman da baiga motar Abba hanifa ba, hankali kwance ya shigo falon saidai ganin su zaune yasa yayi turuss, ummi tace "yayi kyau son dazu muna magana sai dai kawai na juyo ban ganka ba." A daburce yace "ummi kiran gaggawa na samu daga office shiyasa na tafi ban gaya muku ba." Ummi tace "ai nasani" Sosa keya ya shiga yi yan murmushi, tace nidai kafin ka zauna muje ka maida ni gidan suna.

Haka ko akayi Aslam ya maida ummi gidan suna a mota itama nasiha ta shiga yi mai akan ya kula da matar shi ya rike amana ya kula da hakkokinta, karshe ta shiga jero musu addu'an samun zaman lafiya mai dorewa da kuma zuria dayyiba.

Kwana biyu kunjini shiru ko? Kuyi hakuri wlh ban samu zama bane muna sha'ani, amma yanzu insha Allah zan maida hankali mu gama littafin nan, nasan kuma kun gaji ai, ku kara hakuri in-sha Allah saura kirisss.

Oum Ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabilillah🙏.

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗 Mai bukata should
Chat👇
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391

Team glow🧖‍♀️

Page 116

Koda ummi ta koma gidan suna da gudu su batool suka taso suna tambayar ta lafiya mai ya samu Asmah din, dan Abban hanifa ya kira ya Rabi'ah ya gaya mata, halin da ake ciki ita kuma ta gaya musu nan fa suma hankalin su ya ɗaga suka shiga tsumayen jiran dawowar ummi.

Ummi tace masu "babu komai ba wani ciwo bane mai tsananin, wai jiya da zazzabi ta kwana da ciwon kai, to yau ma ko kafin na isa ta wartsake abinta, tace ma zata zo sunan mijinta ne ya hana, tunda jikin ba kwari." Cike da tausayin ƴar uwar su suka shiga yi mata addu'a akan Allah ya ƙara sauki, ya Rabi'ah kuwa dariya tayi, tace "to kodai itama ta harbu ne, dan jiya dama bata cikin lissafi" ummi tace "lalai kam, to sai ki buga ma yayan naku waya ki tambaye shi dan ki tabbatar"zaro idanu ya Rabi'ah tayi tare da cewa "ni shegiya, inji dan daudu, dan Allah umminmu ki rufa min asiri na zauna a ɗakin mijina lafiya." Duk dariya suka saka mata kafin kuma kowa ya kama barkan gabansa, kowacce zuciyar ta cike da tausayin Asmah, duk sun dauki niyyar zuwa har gida su dubota, zahra ma cewa tayi gobe zataje saboda jibi zata koma bidda.

Da'ker Aslam ya samu ya iya danne zuciyar shi ya daga ma Asmah kafa a ranar, washe gari kuwa tunda sassafe ya nemi hakkinsa, dan Daren ranar da'ker ya samu ya rintsa, itama bata hana ba, amma gabanta sai faɗuwa yake yi, dan ta dauka zataji zafi ne kamar yadda taji ana farko, duk da ya ce mata babu zafi sosai, ba wani yarda tayi ba, sai dai ga mamakin ta wannan karon babu zafi sosai ɗin, sai ma daɗi da ta dinga ji yana rinjayar zafin, ranar kuwa ba round ɗaya yayi ba sai da yayi biyu lafiyayyu.
Chapter 89 · 0% Book details