← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 126

Sashe 126

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duke take a bakin kofar falon kuka taje kamar ranta zai fita,ji takeyi zuciyar ta na mata wani irin ƙuna kamar zai kama da wuta,ta gama shirin ta tsab dan tarban miji kwalliya ta yi mishi mai rai da lafiya cikin kananan kaya sai kamshi take zubawa amma yana shigowa ko kallon kirki bai mata ba sai ma rokon ta da ya shiga yi akan ta bashi Aron kwanakin ta zaije dakin Asmah, sai wani zumudi yake yi yana rawar kafa kamar wanda ya shekara babu mace a tare da shi, ta riga ta sani son da yake ma Asmah ya dama wanda yake mata ya shanye yana nuna mata banbancin a bayyane gaskiya ta fara gajiya da wannan abubuwan ko kaɗan bata da matsala da Asmah da shine take da matsala Kuma idan har irin Wadannan abubuwan sukaci gaba da faruwa tabbas zai ɗarsa mata wani abu game da Asmah ita kuma bata fatan hakan domin Asmah ta mata abin da bata cancanci wani mumman kallo daga gareta ba ko yanzu ta tabbata shine ya shirya wannan abin ba tare da sanin Asmah ba don ta tabbata inda Asmah tasan zaiyi wannan abin baza ta taba bashi goyan baya ba, domin ita shaida ce akan jajircewan ta akanta lallai Asmah tana sonta fisabilillah, don haka ta gama yanke shawaran da take gani shine kaɗai mafita a gareta tunda wuri kafin Aslam ya haddasa mummunan gaba atsakanin su dan zuciyar ta ta fara kaiwa matakin da baza ta iya cin gaba da jure irin walannan abubuwan ba. A hankalin ta lallaba ta mike jiki ba kwari ta wuce bedroom dinta ta fada kan gado ta kwanta rigingine tana ci gaba da kukan ta bata san sanda barci barowa ya sace ta ba.

Sati biyu cur ya kwashe a part din Asmah,kamar yadda zee tace ta bashi, a cikin kwanakin nan babu abin da suke yi sai shan amarci inji ta bakin shi, kwata kwata baya gajiya da husnar shi kullum daɗi take karamai ko wani lokaci cikin sha'awar ta yake, Asmah ba famar da bata yi ba ya koma wurin zee da yayi sati ɗaya amma ya shafa wa idanun shi toka karshe har fushi tayi da shi sukayi fada wai ko zaiti fushi ya tafi amma a banza dan haka kawai ta kyale shi tunda ai yayi rabi, Ita wlh kunyar zee ma take ji ga Kuma tausayin ta da take ji kamar kamar me tasha auna kanta a ma'aunin zee kawai sai taga baza ta taɓa iya jurewa idan ita ce, ita ko baiwar Allah koda wasa bata taba yarda ta nuna damuwar ta akan wannan lamarin ba, Aslam take so dan haka dole ta taya shi son abin da yake so idan har son da take mai na gaskiya ne , amma Kuma dole zata dauki mataki don ita zuciya bata da ƙashi. Ranar da ya cika sati biyu, sai gurin karfe goma dare ya tafi kamar bazai taɓi ba sai kwan gaba kwan baya yake yi, da murna ta tarbe shi taci gayunta kamar yadda ta saba ta rungume shi tana gaya mai irin yadda tayi kewar shi, dan da gasken fa taji kewar shi kamar kamar me, shi karan kanshi sai da ya tausaya mata lokacin da suka kasan ce tare, saida ta bari sun samu nutsuwa suna kwance kanta akan kirjin shi tace,"my luv." Yace "na'am my luv." Tace "so nake ne Naimi wata alfarma a wajen ka idan babu damuwa Kuma hakan bazai zama takurawa ba." Yace "ba komai my luv ki faɗi duk bukatar ki idan bai sabawa Shari'a ba, Kuma baifi karfina ba na miki alkawarin ko menene zan miki, domin na faran ta miki kamar yadda kika faran ta min."sauke jiyar zuciya tayi tace "baifi karfin ka ba insha Allah." Dan shiru suka yi gaba ɗaya shi yana sauraren ta ita Kuma tana tunanin yadda zata faɗi bukatar ta,ta yadda bazai mata wani gurguwar fahimta ba, can dai ta daure tace "Dan Allah da manzon sa, Aslam so nake ka raba nama gida da Asmah." Shiru yayi ya bai bata amsa ba da alama ma ya fada tunanin, dagowa tayi suka tsirawa juna idanu gyada mai kai tayi tace "dan Allah da manzon sa karkace A'a Kuma karka tambaye ni dalili." Ta karashe maganar hawaye na cika mata idanu, tausayin ta taji ya mamaye mishi zuciya take tsohuwar Zuma ta motsa yana son zee sosai itama don ita din zaɓin shi ce, amma fa ko rabin na Asmah baikai ba, yana adalci a tsakani su a komai amma banda gurin nuna soyayya, shi Kuma wannan kadai ne jarabtar shi, ganin hawaye ya fara wanke fuskar ta yasa yace "ya isa haka Zainab ki share hawayen ki zan miki abin da kike so shi kenan zaki koma gida na dake odoye yayi miki." Rungume shi tayi tana gyada kai, take ta shiga jero mai godiya ta kare da cewa dan Allah karya gayawa Asmah sai ranar da zata tare ɗin ya ko yi mata wannan alkawarin, tare da cewa tabar komai nata na nan a kwai komai acan gidan taje ta duba abin da bai mata ba sai a canza mata, wanda babu Kuma a siya a saka mata.

Hakan ce kuwa ta kasance daga ita sai shi suke ta shirye shiryen su na komawan ta odoye ba tare da Asmah ko wani nashi ya sani ba har suka gama kwashe kayan sawan su a gidan Asmah bata sani ba, sai ranar da zata wuce da safe shida zee ɗin suka saka ta a gaba suna bata hakuri tare da gaya mata batun tashin, aiko kamar saukar aradu taji zancen, take ta
daka tsallen albarka tace bata yarda ba, rarrashinta suka shiga yi amma taƙi kula ko daya daga cikin su, wasa wasa fa fushi tayi sosai dasu har su mummy ta kira takai karan su amma ba wanda ya goyi bayan ta sai dai a bata hakuri , tanaji tana gani zee ta bar gidan aranar tare da little koda take sallaman ta kin amsa ta tayi saima ficewa da tayi ta bar mata ɗakin ta shige wani ta ɓamo kofa ta murza key tana hawaye, itama zee jikin ta yayi bala'il sanyi ji take kamar ta fasa amma Kuma inta tuna mafita take neman musu ta yadda zaman lafiyar su zai dore sai taji zuciyar ta ta ƙarfafa, komai idan ana nesa nesa da juna yafi armashi, Kuma duk abin da Aslam zaiyi ma ɗaya, ɗaya baza ta gani ba bare taji haushi ai kazantar da baka gaji ba tsabtace inji hausawa, wannan shine mafarain rabuwar gida tsakanin zee da Asmah Kuma hakan ya taimaka ma zaman su sosai da sosai Asmah tayi fushi Kuma daga karshe da kanta ta sauko har taje taga gidan zee din ta saka mata albarka suka ci gaba da zumuncinsu kamar yan uwa ba kishiyoyi ba, wannan kenan.

BAYAN SHEKARA GOMA

Abubuwa da dama sun faru a cikin waɗan nan shekarun masu daɗi da marasa dadi, kadan daga cikin marasa dadin akwai mutuwar Alhaji baba da hajiya mama, wanda tsakanin su wata biyu ne kacal, cikin masu daɗi akwai haife haife da akayi sosai a cikin ɗan waɗan nan shekarun batool da zahra yayan su hudu hudu, Khadijah uku, Amira shidda, dan yan biyu ta jera har sau biyu bayan haihuwar daddy, kwanciyar hankalin da nutsuwa ya watada a cikin zuciyar Alhaji baba, yan matan mummy zuwa wanan lokacin sun zan manyan mata zumunci da shakuwar su kuwa kullum gaba yakeyi, kowacce ta tara zuri'a tana zaune lafiya a gidanta sai hamdala. Asmah kam zuwa wannan lokaci ta zama Babbar mace ƴaƴa sun baibaiyeta ta ko'ina tun daga haihuwar su mummy kofar haihuwa ta bude mata dan ko wata biyar yaran basu rufa ba wani cikin ya bayyana a jikin ta, ta haifi yan biyu kaza bayan su ta sake yin ƴan daɗɗaya sau uku sai kuma abin ya tsaya tsab kamar anyi ruwa an dauke,a bangaren zee ma zuwa wannan lokacin komai alhmdllh dan itama ta waye ta shigo gari Asmah ce data fahimci kamar batasan komai a bangaren ba ta saura ta akan hanya tare da wayar mata dakai babu hassada ko munafirci a ciki dan ita wlh tausayi zee ke bata kula tsakanin ta da Allah take sonta har zuciya, aiko dai zee ta ga gurin zama kama jiki tayi itama gyara takeyi sosai tunda ta fahimci yana da mahimmanci sosai ga mace musamman mai kishiya dan ta fahimce tashin gyara na daya daga cikin abin da yasa Aslam yafi fifita Asmah akanta, ta ƙara haihuwa itama y'ay'a biyu bayan little duk maza daya Dad da alhaji Abdur-rahman, Aslam ya samu kwanciyar hankali yayi wani ƙiba ya zama babban mutum matan shi kuwa Kansu a haɗe yake kamar yaya da ƙanwa, haka ma ƴaƴan su dan tuni su mummy suka koma hannun zee da zama little kuwa yana wajen Asmah dan shi na wajen ta dama,yaran idan ba ka sani ba baza ka iya tantance wa'inne ne na Asmah ba haka baza ka iya gane su waye na zee ba, zee suna kiranta da mammah kamar yadda sukaji little na kira Asmah suna kiran ta da mummy abin gwanin birgewa sai wanda ya gani masha Allahu lakuwata illaha billah.....

Karshe

Alhmdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!!

Oum Ummeetarh
07041130088
Chapter 126 · 0% Book details