Sashe 117
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Dad ya nakasa iya nasaka dan gaba daya kafafun shi sun samu karaya bibbiyu ga kuma hannun shi na dama, banda uban ciwukan daya jijji ga kanshi daya fashe , fuskar shi ta canja kamanni lokaci guda haƙora ukun sama dana kasa duk sun zube sai wawakeken giɓi, su karan Kansu litocin sun tausaya mai kuma sun jinjina ma taurin ranshi da bai mutu ba duk da tarin ciwukan daya ji. Abinka da harkar nera suna gaya wa Alhaji Abdur-rahman akwai karaya za'ayi gyara yace a bashi Dad ya zai canza mai asibitin ba bata lokaci kuwa akayi cike ciken komai aka saka shi a. Ambulance sai asibitin da zee ke kwance.A cikin daren aka yi ma Dad ɗauri dan tsananin azaba harda su kashi a wando suma kuwa yayi yafi so uku yana farfaɗowa, gashi baisan ya kira Allah ba, sai tsala ihu yake yi kamar wani Arne, ranar gaba ɗaya asibitin sai da akasan da zaman Dad masu tausayi nayi masu dariya nayi, su Asmah da Mami ma sun sami labari duk da basu san ko wanene bane kwarai sun tausaya mai, Alhaji Abdur-rahman ne kaiɗai yake ta kai kawo akan shi har zuwa safe, sai da yaga komai ya daidai ta har barcin azaba ya kwashe Dad sannan ya yi sallama da likitoci da niyar zai je gida ya huta, zuwa anjima zai dawo, da safe wuraren karfe 7 Aslam ya iso asibiti,kusa da motar Alhaji Abdur-rahman yayi fakin ba tare da sani cewa motar shi bace, fito wa yayi ya zagayo ya buɗe ɗaya gefen ya dauki little juyowan da zai yi daidai lokacin Alhaji Abdur-rahman ya iso wajen fakin din domin shiga ɗaukar motarshi, kallon mamaki suka shiga bin juna da shi, Aslam na tunanin to waya gaya mishi zee na asibiti don shi a tunanin shi zee yazo dubawa, shi kuma yana tunanin ya akayi Aslam yasan Dad na asibitin nan to ko shima Dr ya kira shi, Aslam ya ƙarasa ya bashi hannu sukayi musabaha, Dad yace "Ya mukaji da wannan iftila'il kuma." Ba tare da ya fahimci komai ba yace "Sai godiyan Allah, amma jikin da sauƙi sosai Alhaji don Dr ma yace yau zai bamu sallama." Alhaji Abdur-rahman cikin mamaki "sallama Kuma! wa za'a ba sallama?" Aslam yace "Ita mana." "Ita wa?" Ya tambaya, Aslam shima abin ya fara ɗaure mishi kai dan haka yace " Ita Zainab ɗin." Zaro ido Alhaji Abdur-rahman yayi cikin kaɗuwa yace "kana nufin kace min Zainab na kwance a wannan asibitin ita ma?" Aslam yace "eh Alhaji ai na dauka ma ita kazo duba wa." Maimakon ya bashi amsa sai "innalillahi wainnailaihi rajiun ya shiga maimaita wa." Can kuma yace "Muje ka kaini wajen ta na duba ta meye ya same ta." Suna tafe Aslam ke gaya mishi ai ta samu miscarriage ne, Alhaji yace "subhanallahi garin yaya." Shiru ya danyi kamar bazai gaya mishi ba sai kuma wata zuciyar ta umarce shi daya faɗa domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa, tuno kawai abin da ya faru don faɗawa Alhaji sai da yaji zuciyar shi ta dauki zafi dan sanyin data ɗan yi tuni ya gushe. Bai yi ƙasa a gwuiwa ya kwashe komai ya shiga gaya mishi, tunkan Aslam ya kai karshe Alhaji wata uwar burki ya taka tare da juyowa hankali tashe yace "Kana nufin Abdus-salam yaje gidan ka ajiya har yayi sanadin zubewar cikin jikin Zainab." Kasa bashi amsa Aslam yayi dan wani irin tukukin bakin ciki yake ji a ranshi. "Innalillahi wainnailaihi rajiun, Allah wadaran naka ya lalace, gaskiya Abdus-salam baiyi wa kanshi adalci ba dama na gaya mishi wani rabon karfi gareshi kisa yake, to shi Allah ma yaso shi bai mutu ba amma kuma da wannan halin daya shiga ai gara mutuwa." Kallon rashin fahimta Aslam ya shiga binshi dashi, ganin haka yasa ya kwashe duk abin da ke faruwa tun da ga daren jiya da aka kira shi a waya daga general hospital zuwa wayewar garin yau, ko ɗar Aslam baiji a ranshi sai ma cewa da yayi "Allah kyauta Allah ya kiyaye na gaba." Sun tarad da su jugum jugum kamar wa'inda aka aikowa da saƙon mutuwa, Asmah da Mami na zaune a bakin daya extra bed ɗin dake ɗakin, zee kuma na zaune a bakin nata bed din rike da cup din tea a hannun ta idanunta sunyi jajur alamar taci kuka ta ba uku lada, ganin wan mahaifin nata yasa ta sake fashewa da kukan da da'ker su Mami suka samu tayi shiru, shima direct gareta ya isa ya zauna a kusan da ita tare da kamo hannayenta ya rike cikin nashi, yana bin ta da wani irin kallon tausaya wa, cikin tsananin kuka tace "Abba dan Allah ka gaya min gaskiya da gaske Dad shine mahaifina shiya haifeni, Abba Dad kullum ikirarin shi yana sona yafi kowa sona a duniya amma wlh ni soyayyar shi ni batai mini rana ba, tun da har ya kasa bani farin ciki, ya kasa barina na zauna da mijina domin na sami Aljannahta aƙarƙashinsa, Abba Dad yayi sanadin da cikin jiki na ya fita, shin wannan wane irin sone?." Ta karashe da wani irin matsanancin kuka, jikinshi ya jawota ya rungume, Asmah da Mami tuni zuciyar su ta daɗa karyewa ji suka kamar su taya ta kuka, Aslam kam taɓe baki yayi ya dauke idanunshi daga garesu, daker Alhaji Abdur-rahman ya samu ya lallɓa zee ya samu ta tsagaita kukan ta, cikin kwantar da hankali yace "Kiyi hakuri Zainab ko wani bawa da kalar jarabtar da ubangiji yake mishi a rayuwar shi ta duniya, ke da mahaifin ki jarabtar ku iri ɗaya ne, shi kece jarabtarshi, kema shine jarabtar ki, kiyi hakuri ki daina jin kamar cewa ba shi ya haife ki ba, tabbas shi ya haifeki, amma Allah ya jarabce shi da wani irin makauniyar soyayya akan ki, wanda a karshe shine yayi sanadin nakasan shi." Nan kuma ya kwashe duk abin da ke faruwa da Dad ya sanar mata, kan kace kwabo ta kara birkicewa, sai kuka take tana kiran dadin ta, karshe ma ta tsige Karin ruwan dake hannunta tace ita gurin dadin ta zata tafi, wai a haka ma Alhaji Abdur-rahman bai gaya musu irin raunukar daya samu ba daga ita har Aslam ɗin kawai ce musu yayi, yayi hatsari, ba shiri Alhaji yasa aka kira Dr ya duba ta, a take ya rubuta mata sallama ma gaba ɗaya kawai, Alhaji Abdur-rahman yace Aslam ya kaita gida, aiko ta ƙeƙashe ƙasa babu inda zata je sai taga dadin ta, dan dole suka dunguma zuwa ɗakin da aka kwantar dashi,da taimakin wani dr abokin Aslma don ɗakin ba'a bari a shiga Aslam baiyi niyar zuwa ba kawai dan yana jin nauyin Alhaji Abdur-rahman ne amma ba dan Allah yaje ba dan ko kaɗan baiji tausayin Dad ba kwata kwata mutumin ya sire mai, gani yake ma alhakin su ne ya kama shi na zuwa da yayi bagatatan ya musu asarar ciki. Alhaji Abdur-rahman ne gaba yana rike da hannun zee sai Aslam dasu Mami biye dashi, dukkannin su saida zuciyar su ta girgiza da ganin yadda Dad ya koma cikin abin da baifi awa ashirin da huɗu ba, wani gigitaccen ƙara zee ta saki tare da durkushe wa a gaban bed ɗin da Dad ke kwance, Asmah ma tuni ta fashe da kuka hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba, wai mutumin daya zo jiya ya nemi wulakansu haka, lallai Allah ba abin wasa bane, Mami ma sai dauke kwalla takeyi, na tausayin zee da mahaifin ta, Aslam kam take idanunshi suka kala sukayi jajur, duk yadda yake jin haushin Dad a zuciyar shi sai da ya tausaya mai, lallai ɗan Adam ba'a bakin komai yake ba, ganin yadda zee ke kururwa tana kuka, yasa Dr saurin basu umarnin su fita su bar mara lafiya shi kaiɗai kar su bata musu aiki, daƙer Aslam ya janyeta daga ɗakin, koda suka fito yace tazo ya kaita gida tayi wanka ƙin yarda tayi ta tafi, Asmah ma sarkin tausayi cewa tayi zata zauna tare da zee, ya kada dambu taliya amma suka ƙi bin shi, karshe shi da Mami ne kawai suka bar asibitin mami ta wuce da little can family hause dan zaman asibiti bai kamace shi ba. A nan suka wuni tare a asibiti sallah kawai ke tada su, daga inda suke zaune, sai bayan la'asa Alhaji Abdur-rahman ya musu abinci daga gida sa, , daga ita har Asmah babu wanda ya kalli inda abincin yake, saidai nan kuma Dad ya farka daga alluran barcin da aka mishi, sun so shiga su ganshi amma Dr ya hana ganin sun matsa yasa da'ker ya bar Alhaji Abdur-rahman ya shiga, ya samu Dad idanunshi a bude harass sai dai hawaye kawai yake zirararwa, ya tausaya mai amma hakan bai hana shi rufeshi da fada ba ya kuma sanar dashi abin da zuwan shi gidan Aslam a jiya ya janyo, karshe kuma ya daura da nasiha,daga yadda Dad ke kuka yana Neman gafarar shi,shi kamshi ya tabbatar yayi nadama sosai harda cewa a kira zee da Aslam ya nemi gafarar su, Alhaji Abdur-rahman ya hana tare da cewa taya bari ya kara samun sauki tukun, daga karshe ya koma barci saboda karfin magungunan da aka bashi yanzu bayan farkawanshi. Bayan isha'e Aslam da Abba da Alhaji baba suka zo asibe ko za a basuyi ba Alhaji Abdur-rahman shima ya dawo da ta masallaci . Mami ne data koma gida ta labarta wa Abba abun da ke faruwa shine fa ya sanar wa su daddy da Alhaji baba sun tausaya matuka duk da sunji tsiyar daya tafka Allah ya kama shi. Bayan sun gaggaisa Alhaji Abdur-rahman yace bari yaje yaji daga bakin Dr ko zasu iya shiga su ganshi dan ɗazu jikin da sauƙi, kafin ma ya kai ga tafiya wata nurse ta nufosu da sauri tana haki, dukkan su ido suka zuba mata zuciyoyin su na tsistsin kewa, tace "wacece zee da Alhaji Abdur-rahman da Aslam da karima a cikin ku." Zabura zee dake rungume jikin Asmah tayi ta mike, Aslam ne ya bata amsa da "gamu nan duka." Tace "Dr yace kuzo maza patient ɗin ku yana son ganin ku da gaggawa." Da sauri kuwa suka rufa mata baya dukkansu zuwa ɗakin, Dr ɗaya suka samu da nurse ɗaya akan Dad suna faman bashi taimakon da zasu iya, kimanin mintuna ashirin kenan da farkawanshi, tunda ya farka jikin shi ya ƙara rikice gaba ɗaya sai dai bakin shi bai mutu ba sunan zee da Aslam, Alhaji Abdur-rahman da karima, kawai yake kira a wahalce, ganin yanayin da yake ciki ne kawai yasa Dr ya zare mai karin ruwan da jini da duk wani na'ura dake jikin sa dan jikin shi ha bashi wannan mutumin kam da'ker zai kai labari, hakan daya gani yasa ya aikin nurse dinnan ta kira mutanen da yake nema watakila wasiyya zai bayar, da gudu zee ta karasa gaban shi tana wani irin kuka, mai ban tausayi, da'ker yace "Zainab mutuwa zanyi, ki yafe min." Ciki kuka tace "dadi na baza ka mutu ba in sha Allah zaka warke zafin ciwo ne yasa kake ganin kamar ajalin ka yazo." Murmushi yayi wanda ba kowa bane zai fahimci hakan saboda yadda fuskar shi tayi dameji, yace "mutuwa zanyi Zainab ni nasan abin da na hango, ina mijin ki yake." Aslam dake tsaye daga can baya idanunshi jajur ya karaso gaban Dad, kallon shi Dad yayi ya mika hannunshi guda mai lafiya ya kama hannun Aslam ya manna dana zee dake tsaye kusa da shi cikin maganar shi irin ta marasa lafiya sosai wanda sai mutum ya kasa kunne yake iya gane mai yake fada yace "Aslam kayafe min, nasan na cutar da kai na yi sanadin da ka rasa gudan jikin ka, amma dan Allah karka kulla ceni komai nakeyi akan soyayyar Zainab ce, itace jarabtata duniya tunda na haifeta nake bata wa mutane da yawa rai akan ta indai ita zatai dariya, Allah ya rarabceni da makahon so akan Zainab, kuma har yanzu dana ke kan gabar barin duniya daidai da kwayar zarra banji ɗigo na sonta ya ragu a zuciya ta, ga amanar Zainab nan na bar maka Aslam, duk duniya babu wanda take so sama da kai dan Allah ka kula min da ita ko bayan rai na, dan Allah badan halina ba." kafin ya samu daman kara cewa wani abu tuni harshen shi ya karye sai magana yake yi amma babu mai fahimtar shi, tuni zee ta ƙara ruɗewa tare da fashe da wani irin kuka ta faɗa jikin shi ganin haka yasa Aslam janyeta da karfi tana fisgewa ya fice da ita daga ɗakin, Asmah ma dake kuka Abba ya rike hannun ta ya fice da ita waje,Alhaji Abdur-rahman ne ya masto gare shi yana sharar kwallah ya kama hannun shi ya rike gam yana cewa "dan uwana insha Allah baza ka mutu ba, zaka tashin akan kafafun ka zafin ciwo ne." Alhaji baba dake tsaye gefe yana kallon yanayin Dad ya tabbatar wannan kam yana kan gaba, matsowa yayi gare shi ya shiga laƙaba mishi Kalmar shahada, Allah sarki Dad kasa.kamawa yayi sai ya bude baki zai kama kuma maganar ya sarƙe, karshe idanun shi ya shiga kafewa kumfa na fitowa daga bakin shi, take kuma jikin shi ya fara sakewa a hankali kuma kanshi ya karye gefe.............